NewsHausa NewsHausa

Pages

LATEST POSTS

Saturday, 3 December 2016

SHIN ANNABI MUHD S.A.W. NE FARKON HALITTA ? | DR JAMILU YUSUF ZAREWA

SHIN ANNABI MUHD S.A.W. NE FARKON HALITTA ?

Tambaya :
Malam ina da wata tambaya wacce ta daure mun kai, idan ka san amsa don Allah ka bani tare da gamsassun hujjoji. Tambayata shi ne, shin Allah Annabi Muhammad ne ya fara halitta? Shin wai Allah ya ajiye shine sai lokacin da ya gadama sannan ya zo duniya?


AMSA :
Wa alaikum assalam
Akwai hadishin da ya zo wanda yake nuna cewa Annabi s.aw. shi ne farkon wanda aka fara halitta, saidai hadishin bai inganta ba, 
wasu malaman hadisin, kamar Ibnu-kathir a tarihinsa da Albani a silsilatussahiha hadisi mai lamba 458, sun ce hadisin karya ne.

Fadin cewa Annabi s.a.w. shi ne farkon wanda aka halitta ya sabawa alqur'ani, ta bangarori da dama ga wasu daga ciki :

1. Allah ya tabbatar da cewa Annabi Muhammad mutum ne kamar yadda hakan ya zo a ayoyi daban-daban, sannan kuma Allah ya tabbatar da cewa gaba daya mutane daga Annabi Adam aka same su, kin ga idan ka ce Annabi MUHD shi ne farkon halitta hakan ya sabawa ayoyin alqur'ani.

2. Tarihi ya zo da bayanin nasabar Annabi Muhammad s.a.w., tun daga mahafinsa har zuwa Annabi Ibrahim, kin ga wannan yana nuna an halicce shi ne daga maniyyin mahaifinsa, kamar yadda aka halicci ragowar mutane daga hakan.

Zance mafi inganci shi ne : farkon abin da Allah ya fara halitta shi ne Al'arshi, kamar yadda ya zo a cikin Sahihi Muslim a hadisi mai lamba 2653, cewa : "Allah ya kaddara abubuwa kafin ya halicci sama da kasa da shekaru dubu hamsin a lokacin Al'arshinsa yana kan ruwa"

Kin ga wannan yana nuna cewa Al'arshi ne farkon abin da aka fara halitta ba Annabi muhd s.a.w.
Allah ne mafi sani.

YADDA AKE WARWARE SIHIRI | DR JAMILU YUSUF ZAREWA

YADDA AKE WARWARE SIHIRI


Tambaya :
Assalamu alaikum Dan Allah malam a fitar dani cikin duhu game da abin da yake damuna Mahaifiya ta ce ta je gurin malami ai mata naganin ciwon mara dz yake damunta, tace tana da ciki yakai shekara, amma likitoci sun yi scanning sunce ba komai to sai malamin ya ce mata asiri aka yi mata, kuma zai yi mata magani nan take ta haife abinda yake cikinta amma za ta kawo tunkiya da dubu bakwai, sai take min magana in kawo kudi a sayi tunkiyar kuma akai masa dubu bakwan, to gaskiya malam zuciyata ba ta aminta da malaman ba ne shi yasa ! Na keso ka bani fatawa shin irin wannan hanyar ta magani ta halatta a addini? Idan bata halatta ba wacce hanya zan bi wajen qin biyan kudin da kuma sanar da ita, saboda ina da matsala , ta bangaren aqeeda mun banbanta? Wassalam na gode malam Allah ya qara basira.

Amsa :
To 'yar'uwa tabbas ba a warware sihiri ta hanyar sihiri, saidai ana iya warware sihiri ta hanyar ayoyin Alqur'ani, wasu malaman sun yi bayani cewa : ana iya warware sihiri ta hanyar karanta Ayatul-kursiyyu da Kuliya da Iklas da Falaki da Nasi, da kuma aya ta : 117 zuwa ta 122, na suratul A'araf, sai kuma aya ta : 79-81 a suratu Yunus, sannan sai a hada da aya ta : 65-70 a suratu Dhaha, za'a karanta su, sai a tofa a ruwan da aka zuba magarya guda bakwai, sannan ayi wanka da shi .

Amma bai halatta ki taimaka mata ba, wajan bada wadannan kayan da boka ya nema, saboda ba'a yiwa iyaye biyayya a wajen sabon Allah.

Ya wajaba ki yi mata nasiha cikin hikima, ki sanar da ita cewa : Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa :" 

"Duk wanda ya je wajan boka, ya tambaye shi wani abu, Allah ba zai amshi sallarsa ba, ta kawana arba'in" kamar yadda muslim ya rawaito a hadisi mai lamba ta : 2230. Kin ga in mutum ya mutu a wadannan kwanaki akwai matsala, musamman ma tun da akwai hanyar da shari'a ta yarda da ita, a wani hadisin kuma yana cewa :

 "Duk wanda ya je wajan boka ya gaskata abin da ya fada, to tabbas ya kafurce da abin da annabi Muhammad ya zo da shi" kamar yadda ya zo a Sunanu-abi-dawud hadisi mai lamba ta : 3904, kuma Albani ya inganta shi .

INA GANIN DA IRIN WADANNAN HADISAN ZA KI IYA GANAR DA ITA, TA DAWO KAN HANYA.
Allah ne mafi sani .

Friday, 2 December 2016

ALAMOMIN KARBAR TUBA|DR JAMILU YUSUF ZAREWA

ALAMOMIN KARBAR TUBA

Tambaya :
Assalamu alaikum dan Allah malam akwai hanyar da mutum yake gane Allah ya yafe masa zunubin da yayi, ya kuma nemi yafiya ?
Amsa :
To dan'uwa akwai alamomin da malamai suka fada, wadanda suke nuna Allah ya karbi tuban bawansa, ga wasu daga ciki :

1. Aikata ayyukan alkairi, da son yin abin da zai kusantar da shi zuwa ga Allah.

2. Mutum ya dinga kallon gazawarsa wajan biyayya ga Allah.

3. Ya zama yana yawan girmama zunubin da ya tuba daga shi, yana kuma jin tsoron komawa zuwa gare shi .

4. Ya dinga kallon dacewar da aka ba shi ta tuba, a matsayin ni'ima daga Allah.

5. Ya zama yana yawan nisantar zunubai, sama da kafin ya tuba.

6. Yawan istigfari.

7. Son kusantar salihan bayi.

Allah ne ma fi sani .

 Amsawa

Dr jamilu yusuf zarewa

HUKUNCIN FADIN ASSALAMU ALAIKA| DR JAMILU YUSUF ZAREWA

HUKUNCIN FADIN ASSALAMU ALAIKA


Tambaya :
Assalamu alaikum, malam jamilu Idan mutum zai yiwa dan uwansa sallama zai iya cewa Assalamu alaika idan shi kadai ne.


AMSA :
Malaman Malikiyya, sun hana cewa Assalamu alaika, saboda ba'a samu hakan daga daya daga cikin magabata ba, kamar yadda ya zo a FAWAKIHUDDAWAANY


Amma malaman Shafiiyya da hanabila sun halatta hakan, kamar yadda ya zo a Almajmu'u na Nawawy da Kashshaful Kanna'a

Don han haka abin da ya fi shi ne fadin Assalamu alaikum ko da ga mutum daya ne


Amsawa

Dr jamilu yusuf zarewa

Thursday, 1 December 2016

HUKUNCIN KALLON WASAN KWAIKWAYON ANNABAWA | DR JAMILU YUSUF ZAREWA

HUKUNCIN KALLON WASAN KWAIKWAYON ANNABAWA

Tambaya :
Malam Don Allah Tambaya Na ke da shi Da Fatan Za'a Fahimtar da ni. -wai Shin Kaset din da akeyi na Tarihin Annabawa Ya Halatta A Kalle shi ? Allah Ya Saka Da Alkhairi .

Amsa :
To dan'uwa malamai da yawa sun haramta yin wasan kwaikwayon annabawa saboda dalilai kamar haka :

1. Hakan zai iya bude kofar da wasu masu kallon za su yi isgilanci ko ba'a ga annabawan Allah, isgilanci ga annabawa kuma yana iya fitar da mutum daga musulunci, kamar yadda aya ta : 65 a suratu Atttauba ta yi nuni zuwa hakan.

2. Wasu daga cikin masu shirya film din suna wuce gona-da-iri, kamar masu nuna annabi Isa a matsayin Allah, addinin musulunci kuma ya haramta duk abin da zai kai a riki wani annabi ko managarci a matsayin Allah.

3. Irin wadannan wasannin na kwaikwayo, suna ragewa annabawa matsayi, saboda masu film din suna cakuduwa da matan da ba muharramansu ba, wanda hakan kuma ragewa annabawa kima ne.

4. Kasancewar hakan ya sabawa hikimar Allah ta sanya shaidanu ba sa iya kama da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi , kamar yadda ya zo a hadisi .

5. Kasancewar hakan zai jawo aki girmama annabawa, a kuma yi musu karya, domin wasu masu yin wadannan fina-finan mutanen banza ne, ka ga sai a dinga kallon annabawan da siffar wadannan.

Allah ne mafi sani

     Amsawa

Dr jamilu zarewa

HUKUNCIN AUREN YAHUDU KO NASARA | DR JAMILU YUSUF ZAREWA

HUKUNCIN AUREN YAHUDU KO NASARA


Tambaya :
Malam musulmi zai iya auren ahlul-kitab tana addininta yana musuluncinsa ?


Amsa :
To dan'uwa Allah madaukaki ya halatta auren ahlul-kitabi, wato Yahudu ko Nasara, kamar yadda ya yi bayanin hakan a cikin suratul Ma'ida aya mai lamba ta :
(5),


kuma an samu wasu daga cikin sahabai, sun aure su kamar Usman dan Affan - halifa na uku a musulunci- ya auri Banasariya, haka Dalhatu dan Ubaidillah ya auri Banasariya, sannan Shi ma Huzaifa ya auri Bayahudiya, Allah ya kara musu yarda. duba : Ahkamu-ahlizzimah 2\794


Saidai malaman wannan zamanin suna cewa, abin da ya fi shi ne rashin auren Ahlul-kitab saboda yadda zamani ya canza, domin da yawa idan mijinsu musulmi ya mutu yaran suna zama kirista, kai wani wani lokacin ko da sakinta ya yi zata iya guduwa da yaran, sannan zai yi wuya ka samu kamammu wadanda ba su taba zina ba a cikinsu .



Wasu kasashen kuma idan za ka auri kirista daga cikinsu dole zai ka yarda da dokokin kasarsu, a lokuta da yawa kuma za ka samu dokokin sun sabawa ka'idojin musulunci .

Allah ne mafi sani.

  Amsawa

Dr jamilu zarewa

Wednesday, 30 November 2016

HUKUNCIN SADUWA DA MAI CIKI |DR JAMILU YUSUF ZAREWA

HUKUNCI SADUWA DA MAI CIKI


Tambaya :
Malam na kanji wasu mutane na fadar cewa ba ya halatta idan
matar mutum tana da juna biyu yayi jima'i da ita har sai ta haihu meye gaskiyar maganar?

AMSA :
To dan'uwa ya halatta a sadu da mace lokacin da take da ciki, saboda fadin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi : "Duk wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira, to kada ya shayar da ruwansa ga shukar waninsa" Abu-dawud : 1847

Ibnul kayim yana cewa : "Wannan hadisi yana nuna cewa ciki yana kara karfi duk lokacin da ake saduwa, saboda Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kamanta shi da shuka, ita kuma shuka tana kara girma, idan aka ba ta ruwa" Tahzibussunan 1\193 .

Saidai masana likitanci suna cewa: Ba'a so miji ya dinga hawa kan matarsa lokacin da take da ciki, zai fi kyau ta dinga yin goho yayin da za su sadu, ko kuma ya sadu da ita ta gefe, saboda kwanciya akanta yana iya wahalar da yaron .

Sannan yawanci mata basu cika son yawan saduwa ba idan cikinsu ya girma, wasu likitocin suna bada shawara cewa a karanta saduwa a wadannan lokutan.

Allah ne ma fi sani .