June 2017 - NewsHausa NewsHausa: June 2017

Pages

LATEST POSTS

Sunday 25 June 2017

[FILM] Download Baahubali 3 Trailer 2019

Download baahubali 3 Trailer 2019 ,This indian how this fim will be...........?
But is watch this trailer is so...........

Download and Enjoy

Download video mp4 Now

Saturday 24 June 2017

Zan Bawa Masoyana Masoyana Mamaki Inji Rahama Sadau

Bayan hutu da aka sha na rashin fitar finafinan Hausa a kasuwa, masu shirya finafinan Kannywood sun kammala shiri tsaf domin sakin wasu daga cikin manyan finafinai da ake ta yi musu jiran tsammani tsawon lokaci.
A cikin finafinan da za ta saki sun hada da fim din da shaharariyar jarumar nan watau Rahama Sadau, wanda kusan za a iya cewa, shi ne fim na farko da zai fita kasuwa karkashin kamfaninta Sadau Pictures.
Wannan shahararren fim da aka dade ana jira ‘RARIYA’ ya samu karbuwa matuka tun kafin ya fita, wanda yanzu aka tabbatar da cewar za a fara haska a manyan sinimun kasar nan ranar 26 ga watan Yuni, 2017, watau ranar Sallah kenan.
Tun a baya, a ci gaba da kokarin da yake na tallata sabon fim dinsa mai suna Rariya, kamfanin SadauPictures ya sanya gasar rawa ga ma’abota kallon finafinan Hausa, inda za a lashe kyautuka masu gwabi ga dukkan wadanda suka sami nasarar lashe gasar.
Kamar yadda suka sanya a shafukansu na sada zumunta: Twitter, Facebook da Instagram, SadauPictures sun bayyana cewar gasar ta rawa ce kadai, wadda ake son a kunna wakar fim din mai take ‘Tankade na yo na sa Rariya’ sannan a taka rawa wadda ta fi ta jaruman ciki.
Tuni dai matasa suka fara gudanar da wannan gasa a shafukan Instagram, inda suke taka rawa sannan su dora, yayin da su kuma kamfanin SadauPictures za su sake sakawa a shafukansu.
Wannan dai shi ne karo na farko a tarihin masana’antar shirya finafinan Hausa da wani kamfani ya bugi kirji tare da sanya gasa makamanciyar irin wannan. Wadda za a ci kyautuka da suka da: Talabijin, Kayan Sauti da kuma Fanka.
Shugabar kamfanin, jaruma Rahma Sadau ta bayyana a shafinta na Instagran cewar gasar ta kowa da kowa ce, kuma za a gabatar da wadanda suka yi nasara a gidan talabijin na Arewa24 karshen watan nan da muke ciki.
Yau dai kimanin mako uku kenan ana fafatawa a wannan gasa, inda kowa yake kokarin ganin ya zamo zakaran gwajin dafin da zai lashe, sannan ya samu ganawa da Rahma Sadau.
Fim din Rariya, na daga cikin finafinan da masoya kallon finafinai ke matukar tsumayi a halin yanzu, domin ya hada jarumai irin su Ali Nuhu, Rahma Sadau, Sadik Sani Sadikm Fati Washa, Hafsat Idris da sauran su. Babban darakta Yaseen Auwal ne ya bada umarni.
Babban abin da masoya wannan jaruma ke son ji yanzu shi ne, lokacin da za a saki fim din, domin sun yi tanadin yin fitar dango domin su kashe kwarkwatar da ta dade tana yawo cikin idon su.
Ga dukkan alamu za a iya cewa wannan shi ne karo na farko wani fim din Hausa ya samu tagomashi a Nijeriya, domin za a haska shi a sinimu irin na zama a garuruwan Kano, Kaduna, Abuja da kuma Ibadan.
Jarumar ya bayyana ranakun da za a saki fim din yayin tattaunawar musamman da wakilinmu ta wayar tarho, inda ya ce duba da yanayin irin aikin da aka yi wa fim din, kamfanin Sadau Pictures sun yanke shawarar sakinsa a bukukuwan sallah.
“Rariya fim ne da aka kashe makudan kudade wajen yin sa, saboda haka hanyoyin tallata shi kadai sun bambanta da yadda ake yi wa sauran finafinai. Mun zabi lokacin bukukuwan karamar sallah ne domin domin bawa mutane damar kallon sa kasnacewar ana hutu.” A cewar Rahama Sadau

Adam A Zango Yayi Wani Sabon Fim Wanda Ba’a Tabayin Irin Shiba A kannywood



Adam A Zango Yayi Wani Sabon Fim Wanda Ba’a Tabayin Irin Shiba A kannywood

Jarumi Adam A Zango ya jima yana yo fina finai wanda suka saba zuwa da sabon salo a kannywood. A bana a kuma yo wani fim wanda yasha ban bam da sauran fina finan hausa na kannywood.

Fim ne wanda ya janyo cece-kuce ga sauran daraktoci akan irin salon da fim din yazo da shi. Wasu mutanen cewa su kayi, Adam A Zango ya yi amfani da tsafi acikin fim din, amma maganar gaskiya ba wani tsafi siddabaru ne kawai na na’ura mai kwakwalwa (cumputer).



Adam A Zango ya kashe naira milliyan goma sabida fim din, domin har kasar Cameroon yaje sabida daukar fim din. sunan fim din MADUGU wanda yasha bamban da sauran fina finan kannywood.

Tun kafuwar kannywood kawo yanzu ba’a taba yin fim mai abin al’ajabi ba kamar fim din MADUGU.
 inji fasihi wanda akeyiwa lakabi da Horon Darakta Hafizu Bello.
Wannan Fim MADUGU yana da jerin fina finai takwas da Adam A Zango yace zai bada umarni a bana 2017.

©hausaTop_com_ng

Gasar Lashe N5000 Da Haduwa Da Ali Nuhu,Umar m Shareef Da Maryam Yahya Da samun Tikitin Na ganin Fim din mansoor a Sinima- inji Ali Nuhu

Gasar Lashe N5000 Da Haduwa Da Ali Nuhu,Umar m Shareef Da Maryam Yahya Da samun Tikitin Na ganin Fim din mansoor a Sinima- inji Ali Nuhu

kun iya raira waka? kirkira naku waka irin na "Abin da ke raina",waka daga fim din mansoor domin samun lashe N5000,haduwa da Ali nuhu,umar m shareef da maryam yahya kuma lashe Tikiti na ganin fim din mansoor a sinima.

Domin shiga wanannan Gasar
*Bi shafin mu @pulsenigeriahausa.

*kirkira naku waka irin na "Abin da ke raina".

*Raba a shafib ku,Amabata @pulsenigeriahausa.

*Bukaci Abokan ku su so bidiyon akan shafin mu.

*Bidiyon da aka fi so zai lashe gasar.


Sanarwa daga babban jarumin Ali Nuhu A Shafinsa Na Instagram.

Domin kalla sanarwa bidiyon daga bakin jarumin sai ka danna nan

Download Video Mp4 Now


ku kasance da ®www.hausaloaded.com

Friday 23 June 2017

Yadda Maryam Yahaya (Mansoor) Ta Girgiza Kannywood


Ga duk mai bibiyar harkokin masana’antar shirya finafinan Hausa watau Kannywood, ya kwana da sanin bullar sabuwar jaruma Maryam Yahaya (Mansoor), wadda za a iya cewa ta shigo farfajiyar fim da kafar dama, kasancewar ta zamo cikin jerin taurarun da ake sa ran za su haska nan da shekaru masu zuwa.

Akwai mamaki matuka yadda cikin lokaci kankani jarumar ta yi wa takwarorinta fintikau wajen yawan fitowa a finafinai masu kyawun gaske, ko da yake ba abin mamaki ba ne idan aka yi la’akari da kamfanin FKD Production da ya tsaya tsayin daka wajen yi mata babban fim watau MANSOOR, wanda za a saki a satin karamar Sallah a sinimun da ke fadin kasar nan, ranar 30 ga watan Yuni 2017.

Maryam, ‘yar asalin Jihar Kano, ta shimfida kwarewarta a farfajiyar, gwana ce ta gwanaye, wadda take yin kyau da zarar an dora mata kyamara. Wani karin armashi game da ita shi ne, yadda ba ta wasa da aikinta a matsayin jaruma.

Bajintar da ta nuna a fim din, MANSOOR, duk da cewa ba shi fim na farko da ta fara fitowa ba, amma an ga yadda tauraruwarta ta haska (wanda aka gani tun kafin fim din ya fita) shi ne ya janyo mata farin jinin tun kafin ya fita. Tallansa kawai jama’a suka gani, amma suka tabbatar da cewar Maryam Yahaya za ta yi abun kirki a masana’antar fim.


Tun daga nan manyan furodusoshi suka fara nuna ra’ayinsu na sanya ta a finafinansu, kafin ka ce kwabo jarumar ta kai matsayin da take a yau, na zamowa cikin jerin manyan jaruman da Kannywood ke alfahari da su.

Cikin shekara daya kacal da fara yin fim, jarumar ta zamo tauraruwar da kowane lungu da sako ake labarinta. Gwana ce wajen iya aktin, musamman da ta kasance tana iya taka kowace irin rawa da aka dora ta matukar ba za a wuce gona da iri ba.

Masana’antar Kannywood ta dade ba ta samu jaruma da cikin lokacin kankani ta shige sahun takwarorinta ba, domin an saba ganin yadda wasu jaruman ke daukar shekaru kafin ‘yan kallo su gamsu cewar kwararru ne, balle har manyan furodusoshi su rika aiki da su a kai a kai.

Sai dai masana na ganin tagomashin da ta samu na horo daga wurin maigidanta jarumi Ali Nuhu, shi ne ummul’aba’isin kasancewarta kwararriya a masana’antar Kannywood.
Babban abin da yake kara mata farin jinni tsakanin abokan sana’arta shi ne girmama na gaba, karamci, mutunci da sanin girma mutane.

Har ila yau, jarumar ta dan yi tsokaci kadan game da abubuwan da ta fuskanta daga gida kafin a amince mata ta fara harkar fim.
“Dole ne duk wanda ya samu kansa a wannan hali zai iya samun matsala, musamman a gidansu za a ji irin ba dadi din nan. Amma daga karshe ina nuna masu harkar fim sana’a ce tamkar kowane irin aiki, lokacin da kake bakin aiki magana a waya ma jarumi ba shi da damar yi balle ya samu damar zuwa yawo.

“Kuma ina son mutane su sani, fim sana’a ce kuma ko wace masana’anta akwai nagari akwai kuma na banza. Idan ka tsare kanka Allah Zai taimake ka, saboda kai dai ka san me ka je yi, idan ka je iskanci ne kai ka sani, idan ma ka je a wulakance ne kai ka sani idan kuma ka je da mutuncinka Allah zai kare maka mutuncinka.” A cewar Maryam.




Jaruma Maryam Yahaya ta ciri tuta, ta kafa tarihi a masana’antar Kannywood, ta zamo gwana da ta ta yi bajintar a zo a gani cikin kankanin lokaci, alamu sun nuna matukar jarumar ta dage kan kadamin da ta taho a kai, babu shakka nan da wani lokaci za ta shiga sahun manyan jarumai mata da duniyar fim ke labari.

Cikar jaruma shi ne yin abin da darakta yake so, a lokacin da yake so. Haka zalika rawar da jaruma kan taka fim kan zamo wani siradi na sirrin nasararta. Batun kyau da cikar zati kuwa na karawa jaruma kwarjini a idanun ‘yan kallo, ta yadda idan ba jarumar da suke so suka gani a fim ba, bai cika birge su ba.

Finafinan da ta fito ciki sun hada da: Tabo, Mijin Yarinya, ‘Yar Main Ganye, Duhun So, da Arashi.
Ta samu magoya baya da yawa a shafukan sada zumunta, musamman Instagram, inda take amfani da @MaryamYahya.

©hausatop_com_ng

[MUSIC] ClassiQ Barka Da Sallah New Song

ClassiQ Barka da Sallah from arewa mafia .wanannan wata tsara ba ce da ClasssiQ yayi goron Sallah ga matasa.
kadan daga cikin baitocin wakar:

mallam sallah ya iso gayama mama da baba  special to the members a sai mana kayan sallah.

Zamu ci naman sallah
Sallah!
sallah!!
sallah!!!

Zamu ci naman sallah 
sallah!
sallah!!
sallah!!!

Download and enjoy......


Download Audio Now





Thursday 22 June 2017

A Daina Bata Mana Suna Kan Dabinon Saudiyya, Inji Sadiya Farouq

A Daina Bata Mana Suna Kan Dabinon Saudiyya, Inji Sadiya Farouq

Daga Ubaidullah Yahaya Kaura

Babbar kwamishiniyar Hukamar kula da 'yan gudun hijira ta kasa Hajia Sadiya Umar Farouq, ta yi matukar nuna takaicin ta, tare da alhini akan yadda ake ta kokarin batawa Hukamar da take jagoranta, jihar ta haihuwa (Zamfara), ita kanta dama kasar Nijeriya suna akan wai cewa ta karkatar da dabinon tallafi 'yan gudun hjijra da kasar Saudiya ta baiwa Nijeriya sadaka. 

Kwamishiniyar ta bayyyana matukar mamakinta, da takaicinta irin yadda wasu suka yi amfani da kafar sadarwa ta zamani, dama wasu jaridun kasar nan wajen yada labarin kanzon kurege akan cewa ta karkatar da dabinon tallafin zuwa jihar ta haihuwa wato Zamfara.

Kwamishiniyar tace ita dai abunda ta sani shine hukumar ta na iya kokarinta wajen ganin ta kyautatawa 'yan gudun hijira da ma kokarin sauke hakkin da duk ya rataya ga hukumarta. 

Kwamishiniyar ta tabbatar da cewa tabbas 'yan gudun hijira da suka fito daga jihar Zamfara su ma suna daga cikin wadanda suka amfana da tallafin dabinon, domin akwai tarin 'yan gudun hijira da rikicin barayin shanu ya rutsa da su kamar sauran sassa na kasar nan. 

Haka zalika Sadiya ta kara jaddada cewa hukumarta na iya kokarinta wajen daidaito da raba daidai a duk ayukkan da take yi.

Daga karshe kwamishiniyar ta roki al'umma da su kasance masu bincike da tabbatar da labari kafin yada shi.

©Rariya

Kada Mu Munta Da Sanya Shugaba Buhari Cikin Addu'o'in A Wanan Dare Mai Albarka



Daga Bashir Ahmad

‪A yayin da wannan dare mai albarka (Lailatu kadari) ke tunkaro mu, ina tunatar da ku cewa mu sanya shugaba Buhari cikin addu'o'inmu.

"Ya Allah, Mahaliccin dukkan halittu, makagin duniya, mai hukunci a ranar hisabi, Sarkin sarakuna, mahaliccin Annabi Muhammadu (S.A.W) ka dubi shugaba Muhammadu Buhari, shugabanmu, Uban kasa, ka ba shi kariya, ka ba shi ingantacciyar lafiya da karin hikima ka kuma kare shi daga sharrin masharranta.

Allah ya mun yi tawassuli da Annabi Muhammad (S.A.W) da Al Kur'ani, ya Allah Ka karawa Shugaba Muhammadu Buhari lafiya da nisan kwana. Allah ka kare shi daga dukkan sharri.

Allah Ya biya mana bukatun mu, Ya amsa ibadun mu baki daya.

Bashir Ahmad, shine mai baiwa shugaba Buhari shawara kan harkokin kafafun yada labarai

Wednesday 21 June 2017

Mutane Biyar Sun Rasa Rayukansu A Wajen Turmutsutsun Karbar Zakkar 500 A Katsina


...jami'an tsaro sun kama wanda ya raba zakkar

Akalla mutane biyar ne suka rasa rayukan su wajen karbar zakkar Naira dari biyar biyar a jihar Katsina.

Wadanda suka rasa rayukan na su sun kunshi kananan yara guda 4 da wata mata mai kimanin shekaru 40.

Lamarin ya faru ne a yayin da darururuwan mutane suka taru a gidan mutumin da ke raba zakkar mai suna Kamal Ma’a Gafai, a yankin Rafin Dadi da ke jihar.

Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar Katsina, DSP Gambo Isah ya shaidawa manema labarai cewa banda wadanda suka rasu, akalla mutane 15 sun jikkata.

Ya ce an kai mutane 15 din asibiti inda aka yi masu magani aka kuma sallame su.

Shi kuwa Gafai mai raba Zakka, DSP Isah ya ce yanzu haka ya na hannun su kuma sun shiga bincike akan shi.

©Faceboo/Rariya

Tuesday 20 June 2017

KANNYWOOD: Dawowar Rahama Sadau Harkar Fim Ya Fara Tayar Da Kura



Kamar Yadda kuka sani cewa an dawo da jaruma rahama sadau harkar fim a satin daya gabata wanda kamar yadda alamu yanuna jarumar tadawo da kafar dama domin kuwa sabon fim dinta mai suna rariya yana daya daga cikin jerin fina finan daza’a saki acikin bikin sallah.

Hakan ne yakawo tashin kura a wani bangaren daban musamman ma ga yan uwanta mata abokan harkar tata domin kuwa mafi yawancinsu ba’a son ransu aka dawo da Rahma Sadau ba. sabida suna zaton zata iya hana su rawar gaban hantsi awajen wasu daraktocin kamar Ali Nuhu da Aminu Saira dadai sauransu.

Jaruma Guda Dayace wacce tafito fili ta nuna murna da farin cikin dawowarta harkar wato Aisha Aliyu Tsamiya.
Shin Ko Mene Ra’ayinku Gameda Dawowar jarumar???

Darikar Tajjaniyya Da Shi'a Duk Daya Ne, Cewar Sheik Dahiru Bauchi


Shahararren malamin nan Sheik Dahiru Usman Bauchi ya bayyana cewa Darikar Taijjaniyya da Shi'a duk daya ne.

Shehin Malamin ya bayyana hakan ne a jiya Litinin a yayin da ya karbi bakoncin tawagar wasu mabiya Shi'a a gidansa dake Kano.

Ya ce da Shi'a da Darikar Tijjaniyya duk tafarkin Annabi (S.A.W) suke bi kuma masoyan iyalansa ne. Ya kara da cewa babu wani bambanci tsakanin akidun biyu.

"Da Shi'a da Darikar Tijjaniyya duk daya ne saboda dukkansu suna bin tafarkin Annabi (S.A.W) ne kuma masoyan iyalansa.

"Duk mulumin kwarai ya zama dole ya yi imani da Annabi (S.A.W) da kuma nunawa iyalansa kauna. Don haka dukkanmu mun iya imani da shi. Don haka daya muke" cewar Shehin Malamin.

Ya kuma yabawa tawagar Shi'an kan ziyarar da suka kawo masa, inda ya bayyana hakan a matsayin wata hanya ta hadin kan musulmai.

Tun a farko, jagoran tawagar mabiya Shi'an, Malam Yakubu Yahaya, ya bayyana cewa makasudin kawowa Shehin Malamin ziyara shine don taya shi murnar kammala tafsirin azumin Ramadan na wannan karo da ya yi.

Sources:Rariya

Abin Al'ajabi:Wata 'yar Nigeria ta yanki al'aurar wanda ya yi mata fyade

An gurfanar da wani mutum mai shekara 30 a gabata kotu, bayan yarinyar da ya yi wa fyade ta yanki al'aurarsa, a jihar Katsina da ke arewa-maso-yammacin Najeriya.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sanda ta jihar, DSP Gambo Isa, ya shai da wa BBC cewa, asirin mutumin ya tonu ne bayan da ya je neman shaida a wajen 'yan sanda domin likitoci su duba raunin da yarinyar ta yi masa a al'aura.

Jami'in 'yan sanda ya kara da cewa an fahimci abin da ya faru ne bayan 'yan sanda sun yi masa tambayoyi, inda daga nan ne aka gane cewar ya ji ciwon ne a lokacin da yake yi wa wata yarinya fyade da karfin tuwo.

A halin yanzu dai mutumin da ake zargin na gidan wakafi, bayan alkalin kotun majistire, sai Mai Shari'a Fadile Dikko ya dage sauraren karar zuwa 20 ga watan Yulin mai kamawa.
Alkalin ya ce zai mayar da shari'ar ga rundunar 'yan sandan jihar Katsina da kuma daraktan gabatar da kara na jihar domin gurfanar da mutumin a gaban babbar kotu, saboda kotunsa bata da hurumin sauraron batun fyade.

Bayanai daga jihar ta katsina na cewa lamarin ya faru ne a wani kango a karamar hukumar Kankara.
Lamarin dai ya faru ne a ranar 15 ga watan Mayun da ya wuce, amma ya fito fili ne a lokacin da shi mai fyaden ya je asibiti neman magani.
A karkashin doka a Najeriya dole ne mutum ya gabatar da bayanin amincewar 'yan sanda ga likitoci kafin su duba shi, idan rauninsa ya shafi wasu nau'uka ciki har da harbin bindiga.

©bbchausa_com

Monday 19 June 2017

BIKIN SALLAH: Gwamnatin Jihar Lagos Ta Karya Farashin Buhunan Shinkafa

BIKIN SALLAH: Gwamnatin Jihar Lagos Ta Karya Farashin Buhunan Shinkafa

Gwamnatin jihar Legas ta karya farashin shinkafa albarkacin bikin karamar salla mai zuwa.

Shinkafa babba buhu mai nauyin kg 50 za a saida ta ne a kan Naira 12,000, 25kg a kan Naira 6,000 sannan 10kg za a kan Naira 2,500.

Ko sauran jihohi za su yi koyi da wannan ngartar?

Daga Bashir Isa

Sources :Rariya

Man United Da Sauran kulob 2 suna Zawarcin Ronaldo

Kungiyoyi 3 da Dan wasa Ronaldo zai iya komawa a kakar bana


Babban Dan wasa Ronaldo na iya tashi daga Real Madrid

– Kungiyar Manchester United na zawarcin Cristiano Ronaldo

– Haka kuma Chelsea da PSG sun tasa Dan wasan a gaba

Dan wasan Duniya Cristiano Ronaldo na shirin barin Kungiyar Real Madrid. Mun kawo kadan daga cikin Kulobs din ‘Dan wasan zai iya komawa

1. Manchester United

Dama kuna da labarin akwai kishin-kishin din cewa Dan wasan yace so yake ya koma Kungiyar sa na da watau Manchester United inda zai kara haduwa da Jose Mourinho.

2. Chelsea


Roman Abromovich mai Kungiyar Chelsea zai dage wajen ganin shi ya dauke Dan wasan na Duniya daga Birnin Madrid zuwa Kungiyar Chelsea da ke Landan maimakon ya koma Manchester.


3. PSG

Ba mamaki idan Kungiyar PSG ta Faransa ta nemi sayen ‘Dan wasan don kuwa kamar dai Kungiyar Chelsea, Nasir Al-Khelafi yana son ‘Dan wasan kuma yana su na da kudi.

Cristiano Ronaldo na shirin barin Real Madrid bayan an fara zargin sa da kin biyan haraji. Tuni dai irin su Bayern Munchen su kace ba su a wajen zawarcin ‘Dan wasan.

©naija.com

Al-Mustapha Ya Bayyana Asalin Abinda Ya kashe Janar Sani Abacha

Bayan shekaru kusan 20: Al-Mustapha ya bayyana abin da ya kashe Abacha

– Dogarin tsohon Shugaban kasa Abacha ya bayyana abin da ya kashe sa

– Al-Mustapha yace ba guba tsohon shugaban kasar ya ci ba

– Manjo Al-Mustapha kuma yace ba ‘Yan mata ne ajalin na sa baDoa

Al-Mustapha yace tun da Abacha ya gaisa da tawagar Yasir Arafat ya fara jin ba daidai ba. Dogarin na Abacha yace sharri ne ace 'Yan mata su ka kashe tsohon Shugaban. Kusan 20 kenan da rasuwar Janar Sani Abacha.

Tsohon shugaban kasa sokan yaki Janar Abacha


Tsohon Shugaban kasa Sojan yaki Janar Abacha

Dogarin tsohon Shugaban kasa Janar Sani Abacha watau Manjo Hamzah Al-Mustapha ya bayyana abin da ya kashe mai gidan sa inda ya karyata cewa guba ya ci ko wai mata ne ajalin tsohon Shugaban kasan na Soji kusan shekaru 20 da suka wuce.

Dogarin Abacha Manjo Hamza Al-Mustapha

Dogarin Abacha Manjo Hamzah Al-Mustapha

Al-Mustapha yace tun bayan da tsohon Shugaban kasar Falastin watau Yaseer Arafat ya ziyarci Janar Sani Abacha ya ga an fara samun canji a jikin sa. Bayan ‘dan kankanin lokaci kafin ayi wani abu kenan dai sai Janar din ya kwanta wanda hakan ya kai ga ajalin sa.

A bayan can kun ji labari cewa Dogarin tsohon shugaban kasar ya kafa sabuwar Jam’iyya mai suna Green Party of Nigeria watau GPN. Tsohon Dogarin yace Jam’iyyar GPN ce mafita a Najeriya.

©naij.com

Sunday 18 June 2017

Dariya Zallah: Bafulatani Da Farfesa!!!

Farfesa ya ce idan nayi maka tambaya baka amsa ba zaka bani 5,000. Idan kuma kayi min tambaya bansaniba zan baka 20000.Profesa ya tambayi bafulatani “nawa ne nisan sama zuwa kasa?” Bafulatani ya ce bai sani ba.
Bafulatani ya ba da 5000.
Bafulatani ya ce saura ni.”Wace dabba ce idan tana kasa tana da kafa 4 idan ta soma tashi tana da kafa 3 idan tayi sama sai ta koma kafa 2 idan ta tashi saukowa sai ta sauko da kafa 1?” Farfesa ya zaro 25,000 dan bai sani ba. Bafulatani zai tafi sai profesa yace “menene ansar?”. sai bafulatani ya zaro 5,000 ya karawa profesa ya ce NIMA BAN SANI BA.
Hahahaha!!!! Duk da hakan sai ku ce Fullo bai da wayo.
Daure ka/ki yi sharhi

Dariya Zallah: Liman Mai Nasiha!!!

Wani Liman ne, bayan an idar da sallar Isha, sai ya tashi yana nasiha yana cewa ‘Allah ya kawo karshen ‘Yan Boko Haram, a taya sojojin Nijeriya da addu’a. Can wani saurayi a karshen masallaci ya tashi da jallabiya da bindiga a hanunsa. Liman ya ga alamun ya fusata, sai Liman yace: Bayin Allah kunji ina ta Surutu koh, giya na sha dazun
Daure ka/ki yi sharhi:

DARIYA ZALLA: Bakano Yaji dadi Fura!!!

Wata rana wani Bakano yaje zance wajen yariyar da zai aura a Zoo Road, bayan ta fito sun gaisa sai ga kannanta da sabon kwano cike da damamar FURA mai sanyi. Bakanon yaji dadin kawo furar nan domin yana son shan fura sosai.
Budurwar ta bude kwano ta zuba ma Bakanon FURA a kofi. Da Bakano ya fara shan furar nan garin jin dadin fura ya ratsa shi sosai can sai Bakanon ya kalli Budurwar
yace” kin san sunan Diyar mu ta fari kuwa sweety?
Budurwar tace a’a!

Da budar bakin Bakanon sai yace “FURERA”.

Daure ka/ki yi sharhi:

Ba Zan Lamunci Haddasa Rarrabuwar Kai A Cikin Gwamnatina Ba, Cewar Shugaba Buhari

Ba Zan Lamunci Haddasa Rarrabuwar Kai A Cikin Gwamnatina Ba, Cewar Shugaba Buhari

Majiyarmu ta The Nation ta rawaito cewa, shugaba Buhari ya bayyana hakan ne bayan ya ki baiwa mukarraban da suka tafi zuwa birnin London damar ganinsa, inda ya umarci da su mai dawa mukaddashin shugaban kasa farfesa Osinbajo muhimman takardu ya sa musu hannu a kai kamar yadda doka ta tanadar.

FARASHIN HAJJIN 2017 NA NIJERIYA: Sauki Ko Tsada?

FARASHIN HAJJIN 2017 NA NIJERIYA: Sauki Ko Tsada? 

Daga Jafaar Jafaar

A dauri can, zamanin da duniya ke kwance, kudin Naira kudi ne mai matukar daraja a kasashen Turai, Asiya, dama daular larabawa, wanda hakan ya sanya ma'abota tu'ammuli da Nairar suka ribace ta a huldar cinikayya dama kasuwancin kasa-da-kasa.

A irin wancan lokaci, darajar Nairar sama take da kudaden Amurka dana Saudiya, al'umai da dama na haba-haba da ita. Amma abin mamaki, waccan Nairar da ada din tayi wancan tashe, itace yau aka wayi gari kimar ta ta fadi dahar takai ko a kasuwar Agadas akema kallon hadarin-kaji. Kai hatta a cikin kasar Najeriyar, Naira bata da wani mutunci a idanun 'yan kasar. Kila hakan bai rasa nasaba da watsi da kananan kudaden Nairar kamar su Sulallan Naira Guda da takardun Naira Biyar da Goma da 'yan kasar sukai. 

Anyi ta korafe-korafe tun bayan da gwamnatin Najeriya ta sanar da farashin Hajjin bana, wanda bisa al'ada, kimanin jihohi Ashirin da daya na musulmai ne da birnin Tarayya Abuja kan lazimta a kasar Saudiya karkashin kulawar Hukumar kula da aikin Hajjin Musulmai ta kasar Najeriya din wato NAHCON. 

Mahukunta sunyi ta kokarin nusar da al'uma cewa ba wani abu bane musabbabin dadin farashin Hajjin banan illa tsadar da kudin Dala yayi akan Naira, kasancewar kusan kaso Casa'in da Takwas cikin Dari na dawainiyar Alhazai da hukumar NAHCON din kan aiwatar a kasar Saudiyan da kudin Dala ta keyi. Amma duk da haka, wadanda basu iya fahimtar cewa farashin chanjin kudi shine linzamin dakushasshen tattalin arziki irin namu ba, har yanzu suna ta neman karin haske. 

A bara, sa'ad da muke jimamin faduwar darajar Naira, wasu 'yan Najeriya nan-da-nan suka yi ta ganin baiken masu kokawa kan lalacewar Nairar, har suke gwabin wai "Da tashin Bam gwamma tashin Naira", wanda kuwa a zahiri, lalacewar tattalin arziki ka iya haifar da rikicin dama tsadar rayuwa. 

A yanzu haka dai, maniyatan aikin hajjin na bana, nata 'yan dabarun ganin sun gagganda sun nemi cikon kudin da zasu cikkata kudin kujera kan dadin da aka samu, to amma abin tambayar anan shine: Me yasa Alhazan Najeriya zasu biya kudi sama dana maniyatan sauran kasashe?

Haka dai za kayi ta ji; wannan yace kaza, wancan yace kaza, kowa kuma da abinda zaka ji ya fadi. Amma dai cikin wadanda suka yi tsokaci kan wannan lamari, akwai bayanan shugaban kamfanin jigilar jiragen sama na Med-view Alhaji Munnir Bankole, wanda a iya cewa jawabinsa ya bada haske sosai kan wasu batutuwa da suka shigewa maniyata duhu. Matsayinsa na guda cikin masu ruwa da tsaki a sha'anin jigilar Alhazai, kasancewar sa daya shafe sama da shekaru Talatin a harkar zurga-zurgar jiragen sama, Alhaji Munnir shima dai ya bayyana cewa tashin farashin chanjin dai shine ummul-aba'isin din tsadar da ake ganin kudin kujerar Hajjin bana tayi.

 A bayanin nasa, ya nuna cewa a tsarin jigilar Alhazai, a duk lokacin da jirgi ya kwashi maniyata yakai su kasar Saudiya, to idan ya tashi dawowa zai dawo ne tsura, ba tare da pasinja koda guda ba, wanda hakan kadai wani babban daliline da ko ba a gayawa kowa ba, kasan cewa sha'nin jigilar Alhazai ya bambanta dana jigilar passinjoji zuwa wata kasar. Sannan Munnir Bankole yace yayinda aka gama jigilar maniyata zuwa kasar Saudiya, to doka ce cewar jiragen jigilar Alhazai ba zasu zauna a kasar ba, saidai kowani jirgi ya koma kasarsa, harsai ranar da aka tsara za a fara kwaso Alhazai a maido su gida. Ka ga kenan haka jiragen saman zasu dawo Najeriya tsurarsu bada kowa ba, sannan idan lokacin fara dawo da Alhazan ma yayi su koma kasar Saudiyan tsura ba tare da pasinja ba. 

Har ilau dai, a kowani zuwa, duk kamfanin jirgi sai an caje shi dalar Amurka Dala Dubu Shida (sama da Naira Miliyan Biyu), matsayin harajin ketarawa ta sararin samaniyar kasahen Chadi da Sudan, da jiragen Najeriya kan ratsa kan suje kasar Saudiya. 

Duk da haka, wasu sunyi ta tambayar cewa to ta yaya kuma maniyata na kasar Pakistan kan biya kasa da farashin da maniyatan Najeriya ke biya, duk da kuwa suma sukan ratsa ta wasu kasashen kafin suje kasa mai tsarkin? Anan ma dai wani babban jami'i dake da masaniya kan hakar ya bayyana cewa ita kasar Pakistan takan ci moriyar afuwar biyan irin wancan haraji ne daga kasashen da take ratsawar, saboda wasu dalilai na huldar jakandancin kawancenta da kasashen da take ketarawar. 

To me yasa kuma Alhazan da suka biya a jirgin yawo wato intanashina, suka fi samun rangwamen farashi kasa dana Alhazan da suka biya ta wajen hukuma wadanda ake kira da Piligirims? Ba wani dalili bane illa adadin kwanakin da Alhazan Piligrims keyi a kasar Saudiya ya linka adadin kwanakin da Alhazan jirgin yawo keyi a kasar. Domin a yayin da Alhazan Piligirims keyin kwanaki Arba'in a Saudiyan, su Alhazan jirgin yawo baifi suyi kwanaki Goma sha Bakwai ba. Duka wannan kuma, baya da wasu 'yan hidindumu da hukuma kewa Alhazan Piligirims din wadanda babu ga 'yan intanashina.

A shekarar bara, duk da cewar farashin canjin ya kasance ne a Naira Dari da Casa'in da Bakwai kan kowace Dala, amma gwamnatin Najeriya sai data sanya tallafin kimanin Naira Milyan Dubu Sittin da Takwas matsayin daunin kudin Hajjin bara. 

Mun sani cewar kasafin Najeriya na bana an girke shi ne akan Naira Dari Uku da Biyar kan kowace Dala guda. Don haka idan ka lissafa Naira Dari Uku da Biyar din sau Dala Dubu Hudu da Dari Takwas da Biyar, matsayin kudin kujerar kowani maniyaci, zaka iske yayi dai-dai da Naira Miliyan guda da rabi. 

To amma wani abu da bamu gane ba shine, hatta a wannan farashi fa, gwamnatin tarayya sai data sanya tallafi a kudaden aikin hajjin na bana. Wani babban kusa a gwamnatin tarayyar ya shaida min cewar a banan, saida gwamnati ta biya Naira Dubu Dari Uku da Biyu akan kowani maniyaci don a saisaita tsefewar farashin chanjin dalar ga Alhazai. Wanda kaga idan ka lissafa wancan kudi sau Dubu Saba'in da Biyar adadin yawan maniyatan bana, zaka iske akalla ba akasara ba, gwamnatin Najeriyan sai tayi cikon sama da Naira milyan Dubu Asirin da Biyu daga aljihunta. 

A wannan yanayi Najeriyan ke fama da lalurar shagidadden tattalin arziki; yunwa da fatara a ko ina a kasar, ina ga babu hikima idan aka yi watsi da irin wadancan matsalolin rayuwa da 'yan Najeriyan ke kokawa kai, aka kwashi kudaden kasa aka antaya a aikin Hajji kawai saboda a samar da kudin kujerar kasa da yadda aka yanka. Na tabbata ladan ciyar da 'yan kasa dake da bukata ya dara ladan bada tallafin aikin Hajji, tunda batu ne na rai da ibada. 

Zanyi matukar takaici ace gwamnatin da bata iya samar da tallafin man fetur, ko gari, ko shinkafa ga talakawanta ba, amma ta bige da samar da tallafin aikin Hajji ga masu dashi. Mamaki na ma shine yadda talakan da sai kullum ya fita sannan yake samun na hatsi, amma shine zaka ji shi yana neman wai gwamnatin ta debi kudi ta antaya a rangwamen kujerar Hajji. 

A tafsirinsa kan Sura ta 3 Aya ta 97 a cikin Kur'ani mai girma, cewar Allah madaukaki: "Kuma mun sanya Ziyartar Dakin Kaba'a matsayin rukunan ibada ga mutane ga wanda ya samu iko." 

Malam Bilal Philips yace an ruwaito daga Manzon Allah Tsira da Amincin Allah su kara tabbata a gare Shi yana cewa: "Iko anan na nufin isasshen guzuri da karfin tafiya. Don haka, dole musulmi ya zamanto ya wadatu da abinda zai ci da wanda zai bari idan yayi niyyar zuwa Hajji. Idan har sai yayi rance sannan zai samu damar ziyartar dakin Allah, to aikin Hajji bai hau kanshi ba..."

©Rariya

Saturday 17 June 2017

KANNYWOOD: Ina Murna Da Rahma Sadau Ta Dawo Harkar Fim Din Hausa – Aisha Tsamiya

Tun bayan da kungiyar ladabtar da ‘yan wasan hausa ta sanar cewa ta dawo da jaruma Rahma Sadau kannywood, jarumai da masu kallon fina finan hausa kowa yake faden albarkacin bakinsa.

Jaruma Aisha Aliyu Tsamiya tabi sahun takwarorinta jarumai wajen bayyana ra’ayinta akan dawowar Rahma Sadau Kannywood.

Acewar Aisha Tsamiya: “Wallahi, nayi murna da farin ciki alokacin da naji Rahma Sadau ta dawo kannywood sabida dana gaba ake gane zurfin ruwa; ma’ana, idan Rahma tayi laifi akoreta to Aisha zan iya laifi akore ni domin dan adam tara yake bai cika goma ba.”

“Bayan haka duk mai kishin ma’aikatar da yake aiki to za’a same shi yana murna idan an samo sababbin ma’aikata. amma idan aka kori abokin aikinsa dole shima ya yi fargabar kada gobe shima akore shi ko akore ta.
Wannan duk misali ne don haka ina murna da Rahma Sadau ta dawo kannywood. kuma inayi mata fatan alkairi akan fim dinta maisuna RARIYA.

Ronaldo Yana Shirin Barin Real Madrid Sannan Kuma Ya Bayyana Inda Zai Koma


Ba mamaki Tauraron Kungiyar Real Madrid zai bar kulob din kwanan nan Babban Dan wasa Cristiano Ronaldo na shirin komawa Man Utd Ronaldo bai ji dadin yadda aka budo masa wuta game da maganar haraji ba Kuna da labari cewa ana zargin Babban Dan wasa Ronaldo da rashin biyan haraji.

Dan wasan bai ji dadin wannan abu ba ya kuma shirya barin Kulob din. Babban Dan wasan yace so yake ya koma Kungiyar Manchester United.
Ronaldo na neman barin Real Madrid ya kuma bayyana inda zai koma Ronaldo zai koma kulob din sa na da? Rahotanni daga Kasar Sifen na nuna cewa Tauraron Dan wasan Kungiyar Real Madrid na shirin tashi bayan an fusata sa game da zargin kin biyan haraji a Kasar.

Ana zargin ‘Dan wasan da kin biyan kusan Dala Miliyan 16 ga Hukuma,Ronaldo na so koma Kungiyar Manchester Unite Ronaldo ya bayyana cewa zai so ya koma Kungiyar sa ta da watau Manchester United ta Ingila inda yace yake da abokan da ya shaku da su.

Ronaldo dai na ganin Real Madrid ta yi watsi da shi a cikin yanayin da yake ciki asali ma an yi tallar riga ba tare da shi ba. Kun ji jiya cewa Shugaban Kungiyar kwallon kafan kasar Faransa Noel Le Graet yace wata rana Koci Zinedine Zidane na Real Madrid zai horar da Kasar Faransa.

Talakawa Ne Ke Haddasa Matsaloli A Kasar Nan, Cewar Solomon Dalung

Talakawa Ne Ke Haddasa Matsaloli A Kasar Nan, Cewar Solomon Dalung 

Barista Solomon Dalung, wanda shine ministan matasa da wasanni, ya ce ko shakka babu talakawa sune matsalar Nigeria. Yace duk sanda kaji wata matsala ko tashin hankali ya kunno kai, to za ka samu talaka ne ya kirkiro ta. Saboda talaka shine bai yadda da dan uwansa ba, bai yadda da addinin wani ba sannan ga bakin ciki da hassada ga junansu. 

Barista Dalung ya bayyana haka ne a wajen taron cin abincin dare na shekara-shekara da hukumar UFUK Dialogue Foundation ta shirya a Abuja.

Masu karatu ko kun amince da kalaman ministan?

©Rariya

Friday 16 June 2017

An Baiwa Ahmed Musa Sarautar Jagaban Matasan Arewa

An Baiwa Ahmed Musa Sarautar Jagaban Matasan Arewa 

Kungiyar daliban Arewacin kasar nan sun nadawa dan wasan kwallon kafa Super Eagles Ahmed Musa sarautar Jagaban Matasan Arewa. 

An yi bikin nadin sarautar Ahmed Musa wanda ya auri sabuwar amarya a ranar Alhamis, 15 ga watan Yuni, 2017 a lokacin kaddamar da gurin wasansa a jihar Kano.

Taron ya samu halartar manyan mutane ciki har da shugaban wasanni na jihar Kano, Ibrahim Galadima.

 Mahaifiyar Ahmed Musa da sauran ‘yan uwansa sun halarci taron a Kano a jiya Alhamis.

Ganawar Mukaddashin Shugaban Kasa Da Dattawan Arewaci Da Kudanci Na Iya Zama Taron Shan Shayi ? Inji Kungiyar Matasan Arewa

Ganawar Mukaddashin Shugaban Kasa Da Dattawan Arewaci Da Kudanci, Na Iya Zama Taron Shan Shayi Matukar Ba A Dauki Matakan Da Suka Dace Ba, Inji Kungiyar Matasan Arewa

Daga Ibrahim Ammani Kaduna

An bayyana ganawar da Mukaddashin Shugaban Kasa Yemi Osibanjo yayi da Dattawan kasashen Inyamurai da wasu Dattawa daga yankin Arewa, a matsayin wani mataki da ya dace amma a hannu guda ganawar na iya zama taron shan shayi, muddin ya zamana ba'a dauki matakan da suka dace ba na warware asalin rikicin. 

Bayanin haka ya fito ne daga bakin daya daga cikin Shugabannin gamayyar Kungiyoyin Matasan Arewa 16 wadanda suka bada wa'adin watannin uku ga dukkanin Inyamurai na da su fice daga nahiyar Arewa mai suna Alhaji Nastura Ashir Shariff, lokacin da yake tattaunawa da Manema Labarai a Otel din Quarter House dake Garin Kaduna. 

Alhaji Sharrif ya cigaba da cewar babu wani babba daga yankin Inyamurai wanda ya fito ya soki lamirin abinda tsagerun Inyamurai karkashin jagorancin Nnamdi Kanu suke yi, face yaba musu da kuma mara musu baya da suke yi, saboda haka ganawar su da Mukaddashin Shugaban Kasa zai iya zama aikin Baban Giwa, kasancewar tsofaffin na Kasar Inyamurai na goyon baya Dari bisa Dari ga tsagerun Matasan Inyamuran masu rajin kafa yankin Biafra, saboda haka kamata yayi Shugabannin Kasa suyi zama kuru-kuru da Matasan Inyamuran domin suyi bayani na zaba cikin biyu Nijeriya ko Biafra. 

Dangane da ziyarar da tsohon Dogarin tsohon Shugaban Kasa Marigayi Sani Abacha wato Manjo Hamza Al Mustafa mai ritaya ya kawo kwanakin baya a garin Kaduna, inda ya gana da wasu daga cikin shugabannin Inyamurai, Ashir Shariff ya tabbatar da cewar su a matsayinsu na shugabannin Kungiyoyin Matasan Arewa ba su aiki kowa ya gana da Inyamurai ba, Hakazalika su a matsayinsu na wadanda suka yi wancan magana ta bayar da wa'adin korar Inyamurai babu wanda ya gayyace su wannan taro, wanda hakan ya nuna cewar da akwai akasi kenan, kuma Inyamurai Matasan su da tsofaffin su sun san su waye Matasan Arewa, kuma sun san hanyar da zasu nemi ganawa dasu, amma sai su kayi kwana suka gana da Al Mustafa, wanda hakan ke gwada cewar sun bar Jaki da gangan sun koma dukan taiki kenan. 

Kungiyar Matasan Arewan sun kara da cewar, ko kadan ba su da bukatar cigaba da zama da Inyamurai a tarayyar Nijeriya muddin Inyamuran na cigaba da nuna kyama da wariya ga Jama'ar Arewa, sannan lallai ne Shugaban Kasa ko Mataimakin shi suyi zama a fili da Matasan Inyamurai su furta da bakin su suna bukatar cigaba da zama a Nijeriya ba wai an yi musu dole ba ne, kuma duk wanda suka zaba a ciki Kungiyar Matasan Arewa na marhabin da shi ba tare da wani jinkiri ba. 

Matasan Arewan sun kuma tabbatar da cewar wannan fafutuka da suke yi na neman 'yancin Jama'ar Arewa su nayi ne bakin rai bakin fama, kuma basu shakkar dukkanin wani bara gurbi dake da mukami a Arewa wanda zaiyi barazanar kama su ko kuma wasu tsofaffi da zasu ki mara musu baya, domin ko an ki ko an so dole sune zasu gaji Arewa, wadancan tsofaffi tasu ta riga ta kare, saboda haka ya dace suyi shiru shine alkhari a garesu. Daga karshe Matasan sun bayyana cewar za suyi wani gagarumin taro a ranar Talata mai zuwa a garin Kaduna domin kara fito da matsayinsu akan dukkanin wani Inyamuri ko wani bara gurbi a yankin Arewa.

Sources:Rariya

Thursday 15 June 2017

kannywood:An kaddamar da kannywood box office



Sun bayyana haka a wani taron ganawa da manema labarai da sauran kungiyoyi dake karkashin Kannywood

Masana’antar Kannywood ta kasance masana’anta wadda ta fi kowacce a arewacin Nigeria samar da ayyukan yi ga matasa cikin kankanen lokaci, amma kasuwanci a cikinta ya gurgunce tsawon shekaru sakamakon dogaro da hanya daya ta samar da kudaden shiga (wato kasuwannin siyar da CD/DVD). A lokatai da dama mutane da dama sun yi yunkurin kawo canji a tsarin kasuwanci amma abin ya ci tura.

Da alama cewa a wannan karo haka zai cimma ruwa. Dalili kuwa shine kamfanin shirya fina-finai na MOTION PICTURE PRODUCTIONS LTD tare da hadin gwiwar CERTIS NIGERIA LTD sun zaburo da sabon tunani wanda zai tafi tare da zamani wajen ganin cewa an farfado da harkar kasuwancin fina-finai yadda kowa zai ci moriyar abin, kama daga Gidajen Kallo, Masu shirya fina-finai, kungiyoyin yan fim har ma da gwamnati.
Kannywood Box Office , zai kasance sabon dandamali a daidai lokacin da harkar tattalin arziki ta tabarbare kuma satar fasaha ta kai tsaiko yadda masu saka jari cikin harkar ke guduwa kuma fasaha ke dakushewa. Hanya daya tilo da za’a fito daga cikin wannan duhu shine ta hanyar farfado da Sinimomi. Kiyasi na baya bayan nan na nuna cewa a Jihar Kano kawai, akwai kimanin kananan sinimomi 8,000, wadanda ta hanyar amfani da tsari da fasahar zamani za’a iya cin cikakkiyar moriyar su, wadda zata kawo dinbin arziki ga masana’anatar.

Wannan tunani ya sa shugabannin wadancan kamfuna guda biyu suka yunkura wajen farawa da samar da wata na’ura, wadda su ka kira da YODA. Ita wannan na’ura ta majigi (projector) an tsara ta yadda sai da kati mai ajiyar fasaha kawai za ta iya amfani da ita (memory card) kuma ba wani mai irinta a fadin duniya sai kamfanin CERTIS. Ta wannan hanya za’a tsare duk wani fim da aka saki daga barayin fasaha, domin ko ka sami wannan kati ka saka a wata komfuta ba zai yi amfani ba sai a na’urar YODA.
Dandamanlin zai kasance waliyyin daura aure tsakanin gidajen kallo da masu shirya fina-finai ta hanyar hada yarjejeniya yadda kamfunan za su karbi fina-finai daga hannun masu shiryawa su rika nunawa a gidajen kallo ta hanyar wannan na’ura ta YODA.

An sami gidajen kallo kimanin 200 da za’a fara gwaji da su a karshen watan June, 2017 kuma a kididdigar da su ka yi ya nuna cewa a kalla a rana guda kowanne gidan kallo zai iya samun 7000, wato kaso 47% cikin dari na kudaden da za’a samu, yayin da masu fim za su iya samun 4000 wato kaso 27% a gidan kallo guda inda masu shirya tsarin da kula da shi za su sami 2000 wato kaso 14%, sai hukumar fina-finai wadda za’a rika cire wa harajin 1400 wato kaso 9.8% (maimakon kusan kaso 10-38% da gwamnati za ta iya karba kai tsaye).
Dandamalin ya fitar da tsarin bawa fina-finai aji kama daga A, B da C, wanda kudin da mai shiryawa zai samu ya danganta da ajin fim dinsa, hikimar itace samar da inganci wajen irin fina-finai da za’a rika fitarwa. A shekara guda, wanda yayi fim mai inganci zai iya tashi da kimanin miliyan 42,000,000.

Hakika wannan tsari zai zama wani juyin-juya-hali a wannan masana’anta domin a halin da ake ciki babu wani fim da zai iya wuce sati biyu a kasuwa kuma ribar da za’a samu ba ta taka-kara-ta karya ba.

Wannan sabon tsari zai samar da hanyar kudin shiga kai tsaye ga masu gidajen kallo, da masu shirya fim har ma da gwamnati, ya kuma samar da sabuwar hanya da ake kishirwarta a wannan lokaci da kasuwar fim ta kusa rugujewa.

Sannan gagara-badau shine yakar masu satar fasaha wadanda a yanzu ke lashe kusan kashi 90% na gumin masu shirya fim, domin wannan na’ura ita kadai ce tilo kuma ta sami sahalewar British Council da Alu ja cikin jami’o’in fasaha a duniya wato Massachusetts Institute of Technology (MIT). Sannan za’a bawa kungiyoyi damar samun bayanai da kuma cudanya da sauran masu ruwa da tsaki yadda za’a iya samun cikakken tsari da kowa zai amfana daga gare shi.
A yau, masana’anatar Kannywood ta dogara da siyar da DVD, wanda idan tsarin da aka zo da shi yayi tasiri DVD zai kasance a mataki na 4 bayan matakan Sinimomi da gidajen kallo, gidajen talabijin da na’urar sadarwa (Online irinsu Netflix, IrokoTV da sauransu) sannan ne za’a fara maganar DVD, wanda a kaida lokacin da fim ya kai ga DVD, kamata ya yi a ce mai shirya fim din ya gama mayar da kudinsa har ya fara samun riba, yadda DVD zai kasance ribar kafa.

A karshe muna ganin cewa farawa da tsarin sinimomi da gidan kallo zai kasance dan ba na ganin cewa duk wadannan tsaruka sun zama zahiri yadda wannan masana’anta da ke da dimbin arzikin da ba’a tatsa ta farfado daga cikin mawuyacin halin dakushewar kasuwancinta zuwa ga matakin arziki da fadada izuwa ga sauran jihohin Nigeria da Afurka har ma da duniya.
Hotuna daga ganawan




©pulse.ng

Kannywood: Hukumar Moppan Zata Hukunta Sulaiman Bosho

HUKUMAR MOPPAN ZATA HUKUNTA SULAIMAN BOSHO.

Daga Haruna Sp Dansadau.

Kungiyar ladabtar da jarumai maza da mata Moppan ta fitar da wata sanarwa a safiyar Jiya talata cewa: zata hukunta jarumin barkwanci Sulaiman Bosho bisa laifin dori akan abinda darakta ya umarce shi wato over role kenan.

Acewar Moppan: “Mun jima muna ganin kura kuran da Bosho Yake Yi acikin fim, mun kira shi dan ya gyara amma ya kasa gyarawa.” “Mun tuhumi daraktocin da suke da suke sa shi acikin fim amma sunce, su basu ga laifi ko munin kalamansa ba.

Dan hakane muka yanke hukuncin hukunta daraktocin da kuma shi jarumi Bosho”. Inji Moppan. Dandalin Mujallarmu.com ta samu labarin cewa hukuncin da za’ayi jarumi Bosho akwai tara wanda aka ci Bosho dan wannan ya zama izna agare shi dama daraktocin da suke bashi umarnin furta kalaman da basu dace ba.

Da muka tambayi Bosho akan da wacce fuska ya kalli wannan hukunci? Sai ya amsa da cewa: “Wannan hukunci son ransu suka aikata, domin mutane sune ya kamata su gane laifin da muka aikata basu ba, domin mutane sune masu kallon mu, sune alkalai ba Moppan ba.”

An Sayar Da Dabinon Da Kasar Saudiyya Ta Aiko Nijeriya A Matsayin Sadaka

An Sayar Da Dabinon Da Kasar Saudiyya Ta Aiko Nijeriya A Matsayin Sadaka

Wani lamari mai ban takaici ya auku a kasar nan, inda wasu suka sayar da dabinon da kasar Saudiyya ta aiko da shi sadaka ga al'ummar Nijeriya domin a raba wa mabukata masu azumi.

A kwanakin baya ne hukumomin Saudiyya suka aiko da dabino tan dari biyu, domin a raba wa mabukata a iajeriya, inda maimakon a raba sadaka, sai wasu suka karkatar da shi suka sayar.

Mai magana da yawun ma'aikatar al'amuran kasashen waje, Clement Aduku ya tabbatar da cewa dabinon ya iso ma'aikatarsu, amma an raba shi ga hukumomin da suke da alhakin rabawa. Ya ce ba da miyan ma'aikatarsu bane wasu suka karkatar da dabinon zuwa na sayarwa. Don haka ya ce za a gudanar da bincike domin gano, wadanda ke da hannu cikin badakalar domin hukunta su.

©Rariya

Wednesday 14 June 2017

Bajintarsa A Gasar Kur'ani Ta Sa Limamin Harami Ya Sumbace Shi Daga Abu Abdur

Bajintarsa A Gasar Kur'ani Ta Sa Limamin Harami Ya Sumbace Shi

Daga Abu Abdurrahman

Limamin Harami Shaykh Sudais ya sumbaci goshin yaron nan (Amer Falatah) ya kuma fada masa cewa insha Allah shine zai zama limamin Harami nan gaba.

Wannan yaro dan Albarka wanda ya zama abin Alfahari ga mahaifansa, Musulinci da musulmin duniya ya taka rawar gani a musabukar Alqur'ani ta Duniya.

Ameer Falatah dan kasar Malawi shine ya zo na daya a gasar karatun Kur'ani na duniya da aka gudanar.

Da wannane muke kara kira ga iyaye lallai a rage fifita karatun boko na yara sama da karatun Addini 

Domin halin da muke ciki yanzu akwai bukatar kowa ya yi tunani gina al'umma ta gari, mu fara daga gidajen mu, 

✔Kayi tunani da kanka wai shin a family dinku kuna da background na ilimin addini ? 

✔Idan babu ka fara tsarawa daga 'yay'anka, don kuma ku shiga cikin mafificiyar al'umma. Shima ilimin zamanin yana da amfanu, amma kar a nunawa yara tun suna kanana cewa ilimin bokon yafi daraja. 

Domin Allah (SWT) yayi yabo na musamman ga bayinsa masu haddace Alqur'ani a cikin littafinsa yake cewa:

*"بل هو ايات بينا ت في صدرالذين اوتواالعلم"* 

Ku saurari karatun yaronnan....subunallah

©Rariya

Tuesday 13 June 2017

Gwamnatin Jihar Sokoto Ta Dauki Nauyin Tura Malamai 90 Zuwa Umra Domin Yi Wa Shugaba Buhari Da Nijeriya Addu'a

Gwamnatin Jihar Sokoto Ta Dauki Nauyin Tura Malamai 90 Zuwa Umra Domin Yi Wa Shugaba Buhari Da Nijeriya Addu'a

Daga Aminu Dankaduna Amanawa

Gwamnatin jihar Sokoto karkashin ma'aikatar lamurran addini ta jihar ta dauki nauyin tura malaman addinin musulunci 90, domin gudanar da umrah a kasar Saudiyya.

Yayin da Malaman suke a Saudiyya za su gudanar da addu'oi na musamman domin samun lafiyar shugaba Buhari da cigaban jihar Sokoto da kasa baki daya.

An dai bawa malaman naira dubu 50 ko wannen su domin bukatocin iyalansu na gida, yayin da suke a kasa mai tsalki.

Malamman dai ana sa ran tashin su zuwa Saudiyya a gobe Laraba.

©Rariya

Damfarar Naira Miliyan 29 A Sokoto: Iyalan Abdullahi Saka-Samu Milgoma Sun Nemi Kwamishinan Shari'a Da Cif Jojin Jiha Da Su Tsoma Baki

Alh Abdullahi saka-samu Milgoma

Wasu 'yan uwa da abokan kasuwanci na Alhaji Abdullahi Saka-Samu Milgoma dan kasuwa da aka yi wa damfara ta makudan kudade har naira miliyan ishirin da tara da dari uku da tsamanin (29,380,000) a watanni baya da sunan kudin cinikin buhunan shinkafa da man gyada da yayi ciniki ta hannun wasu da ake zargin yan damfara ne na neman ceton Kwamishinan Shari'a na jahar Sokoto, Barrister Suleiman Usman da Cif Jojin Jaha Mai Shari'a Bello Abbas dangane da zargin nuna alamun rashin adalci ga yadda ake sauraren Shari'arsu a Kotun Kasuwa dake Sokoto.

Bayanin koken wanda Malam Ibrahim Tambuwal ya sanya wa hannu a madadin yan uwa da abokan hulda na Mai koken ya zargi cewar ana yunkurin amfani da wasu hanyoyi na dubarun Shari'a don baiwa wadanda ake zargin da samun wata hanya tserewa bayan duk binciken da akayi da bayanin da masu laifin suka yi sun amince da cewar, sune da kansu suka yi damfara kuma har sun gina gidaje da sayen motoci daga cikin kudaden da suka damfarari Alhaji Abdullahi Saka-Samu Milgoma na makudan kudaden jama'a. 

Malam Ibrahim Tambuwal yace wadanda ake zargin Faruku Dan Dubai Birnin Kebbi da Alh Sani Gwandu sun yiwa Alhaji Abdullahi Saka-Samu Milgoma yaudara ta fitar hankali tare da damfararsa ta 419 kusan watanni 4 da suka wuce  na karbar kudaden kamun ciniki har naira miliyan N29,380,000 daga cinikin da suka yi na sayar masa da shinkafa buhu dubu biyar da man gyada jalka dubu biyar da aka kiyasta sun tashi akan kudi naira miliyan dari da ishirin (N120,000 000) amma da suka karbi kudin a matsayin somin tabi na biyan kayayyakin sai suka yi ko kasa ko sama har tsawon watani ukku ana cigiya da wahalar nemansu babu bayani. 

Bayanin nasa ya zargi cewar, Faruk Dan Dubai ne ya zo a wurin Alhaji Abdu Milgoma da cewar, shine babban jami'in Kwastam, Watau Mataimakin AC (AC Comptroller Customs)  na Hukumar Kwastam dake kula da jihohin Sokoto, Kebbi da Zamfara,  inda yace yana da shinkafa har dubu biyar da man Gyada jalka dubu biyar. 

Bayan kulla ciniki ta hannun yaron sa, Abubakar Nahantsi, watau Abu Dange wanda shine yayi masa rakiya sai wasu yaransa Aliyu Sabon Birni da Hassan Sani Suleja suka nemi a basu kudi amma Alhaji Abdullahi yaki da cewar sai har ya ga kayan.

Sakamakon irin damuwa da tabbacin da abokin huldarsa Abubakar Nahantsi (Abu Dange) ya bashi ya samu kwarin guiwa dangane da nemo cikon kudaden daga wasu abokan hulda da yan uwa don hada kudaden da zai bayar a matsayin kashi 1/3 na kudaden cinikin kayan. 

Alhaji Sani Gwandu ne ya karbi kudin bisa umurnin Faruk Dan Dubai  kamin su wuce Illela don dauko kaya, amma da akaje Illela babu kaya kuma Faruk Dan Dubai yaci layar zana ya bace.

Duk yunkurin da akayi na maido da kudin wadanda mallakar wasu yan kasuwa ne da suka yi karo karo don ciniki, abin yaci tura. Bayan kama su da gabatar dasu gaban yan sanda sun amince da yin damfara da karbar kudaden ga hannun Alhaji Abdullahi Milgoma har ma da kama motoci biyu da suka saya, sai kuma gidan da aka gina a GRA na Birnin Kebbi cikin kudin damfara, inji bayanin Ibrahim Tambuwal. 

Zuwa yanzu dai yan uwan na zargin akwai wata munakisa daga Kotun Kasuwa dake Sokoto wadda Mai Shari'a Fati Dewa take jagoranci na kokarin rashin adalci, inda baya ga bayar da belin yan damfara da akayi an hana musu shiga kotu don bayar da shaida akan wadanda ake zargi, mussaman ma wadanda shaidu ne. 

Koken na yan uwan Abdullahi Milgoma yayi mamakin yadda za a ci gaba da tsare masu shaida amma a bayar da belin wadanda ake zargin sun aikata laifi, duk kuwa da sanin cewar, hakan na da illa mai yawa ga shari'a ta gaskiya da adalci. 
Alh Ibrahim Tambuwal

Alhaji Ibrahim Tambuwal ya baiyana cewar, dasu da dan uwansu basu gamsu da yadda Mai Shari'a Fati Dewa take gudanar da wannan shari'a ba, sakamakon zargin cewar ba zata yi musu adalci ba ganin yadda wadanda ake zargin suka yi ma Abdullahi Milgoma barazana a gaban kotu tare da katsalandan ga ci gaban shari'a da ake gudanarwa. 

Don haka sun bukaci Kwamishinan Shari'a na jahar Sokoto da Cif Jojin Jaha da Hukumar Kula da Harakokin Shari'a na jahar Sokoto dasu binciki wannan matsalar tasu tare da dauke shari'a zuwa wata kotu saboda adalci da gaskiya akan wannan lamari. 
Yace hakika ko kadan hankalinsu bai kwanta da irin yadda take-taken da da Mai Shari'a Fati Dewa take amfani dasu wajen karba da sauraren bayanai na shaida ga wadanda akayi abin a idonsu ba. 

Kokarin jin ta bakin Mai Shari'a Fati Dewa ko wani na kusa da Kotun Majistare ta Kasuwa yaci tura, inda Mataimakiyar Rajistara akace bata fito aiki ba, saboda daya daga cikin ya'yyanta na fama da rashin lafiya.

©Rariya