October 2016 - NewsHausa NewsHausa: October 2016

Pages

LATEST POSTS

Monday 31 October 2016

Got the money (the video )

Got The Money (The Video)
Ellyman is back with a brand new JAM>
www.bit.ly/2eoX5wU .Rudeman here so
http://www.winthrillsnetwork.com/ppc.php?id=9024b7e25bc14383becda7f71c1e3248

Sunday 30 October 2016

FATAWAR RABON GADO (71)|DR JAMILU YUSUF ZAREWA


FATAWAR RABON GADO (71)
Tambaya?
Assalamu alaikum, malam ina da tambaya. Kanina ne ya rasu bai yi aure ba yana da uwa da uba a raye, yana da kannai 2 macce daya namiji daya, sai ni yayarshi, Dan Allah Yaya za'a raba gadonshi?. Allah ya saka da Alkhairi.
Amsa:
Wa'alaykumussalam,  za'a raba abin da bari kashi: 6, a bawa Mahaifinsa kashi: 5, Mahaifiyarsa kashi daya.
Allah ne mafi sani.
Dr. Jamilu Zarewa
29/10/2016

AIRTEL NG SUNA DAMUNKA DA SATA KO SAKO?


Assalamu alaikum warahmatullah
bismillahi rahamani raheem
sanu da zuwa sadeeqmedia blog yau munzo muku da wani sabon al'amari
AIRTEL NG SUNA DAMUNKA DA SATA KO SAKO?
Ka danna *902#  akan layin airtel NG dinka, kayi reply da 2, zasu cireka daga duk wani tsari da suke damunka da sako ko satar kudi.
duba wanannan pic

FATAWAR RABON GADO (70)|DR JAMILU ZAREWA

*FATAWAR RABON GADO (70)*
*Tambaya?*
Assalamu alaykum,
Don Allah Malam idan mace ta mutu ta bar mijinta da iyayenta amma ba '' 'ya''yafa, yaya rabon su zai kasance?
*Amsa:*
Wa alaikum assalam,
Za'a raba abin da ta bari gida shida, a bawa mijinta kashi uku, sai a bawa babanta kashi biyu, mahaifiyarta kashi daya.
Allah ne mafi sani
26/10/2016
Amsawa
*DR JAMILU ZAREWA*

FATAWAR RABON GADO (69)|DR JAMILU ZAREWA

FATAWAR RABON GADO (69)
Tambaya?
Assalamu Alaikum, Malam don girman Allah a taimake ni da Amsan tambaya ta kamar haka :
Mace ce ta mutu bata da iyaye ba Da ba jika sai qanwarta guda daya shaqiqiya sai kuma li'abbai guda biyar biyu maza uku mata.  Ya za'ayi rabon gadon ta?
Amsa:
Wa alaikum assalam, Za'a raba abin da ta bari gida 2, sai a bawa shakikiyar  rabi, ragowar kuma sai a bawa li'abban su raba a tsakaninsu, duk namiji zai dau RABON mata biyu.
Allah ne mafi sani
25/10/2016
DR JAMILU ZAREWA

Saturday 29 October 2016

Ellyman is back

Ellyman is BACK with A
brand new single titled GOT The MONEY
Ellyman na rastaman. bit.ly/2e7psCw
http://www.winthrillsnetwork.com/ppc.php?id=2090fb7a6d0c307aa7f4ca8e1d734add

DUKIYAR KASA TA GWAMNATI CE!!!|DR.JAMILU YUSUF ZAREWA

DUKIYAR KASA TA GWAMNATI CE ! ! !
Tambaya?
Assalamu alaykum, malam da fatan kana lafiya,
Tambayata itace :-
Shin wa yake da ikon tasarifi cikin dukiyar kasa, gwabnati kadai ko talakawa ma suna da rabo a ciki ?.
Saboda Na ji wani Malami a Radio yana cewa dukiyar kasa ta gwabnati ce, talaka baya da rabo a cikin ta.
Kubamu fatawa Allah shi saka muku da Alkairi.
Amsa :
Wa alaikum assalam, Shugaba shi ne yake da ikon tasarrufi a dukiyar kasa, saidai ya wajaba amfanin da zai yi da dukiyar ya zama gwargwadon maslahar talakawan da yake mulka saboda fadin Annabi S.a.w. (Dukkanku masu kiwo ne, kuma za'a tambaye ku akan abin da kuke kiwo) kamar yadda Muslim ya rawaito.                                                        Tabbas Allah zai tambayi Shugaba idan ya barnatar da dukiyar al'uma ba bisa ka'ida ba.
Bukhari ya rawaito hadisi, Annabi S.A.W. yana cewa: (Tabbas za ku yi kwadayin shugabanci amma kuma zai zama nadama, madalla da darbar da za'a samu a lokacin shugabanci, saidai abin da zai biyo baya a lahira ya munana),  wannan yana wajabtawa Shugaba taka-tsantsan da kuma tuna lahira idan yana kan kujerarsa.                           
Allah ne mafi sani:
27/10/2016
DR. JAMILU ZAREWA

Wednesday 26 October 2016

HUKUNCIN FADIN (JUMA'AT MUBARAK)|DR.JAMILU YUSUF ZAREWA

HUKUNCIN FADIN (JUMA'AT MUBARAK)
Tambaya?
Assalamu Alaikum. Dr ko ya halatta Musulmi yayi wa dan'uwansa murna da zagayowar juma'a ta hanyar sako a wayar sailula kamar ace JUMA'A KAREEM ko JUMA'A MUBARAK? Allah yaqara sani.
Amsa:
Wa alaikum assalam,  Akwai malaman da su ka hana hakan, suna ganin ba shi da asali a addini, Amma abin da yake zahiri hakan ya fi kama da al'ada, wannan yasa haramta shi yake bukatar Nassi, tun da babin al'adu da mu'amaloli a bude yake, sai abin da sharia ta haramta.                                            Duk Wanda yake yi ba tare da ya riya cewa ibada ba ce hana shi ko bidi'antar da aikinsa yana da wuya, kamar yadda Ibnu Uthaimin ya yi nuni zuwa haka a fatawar da aka yi masa.
Saidai duk da haka ya kamata kar Musulmi ya zamar da shi al-adarsa kowace juma'a, don kar wasu su fahimci ibada ne.
Allah ne mafi sani
23/10/2016
DR JAMILU ZAREWA

sabuwar fasaha:yadda ake banruwa da mashin banruwan lambu ,da shinkafa (kalli hotuna)

Assalamu alaikum warahamatullah
Bismillahi rahani raheeem
barka da zuwa wanannan shafi mai albarka shine  sadeeqmedia blog yau nazo muku da wani sabon al'amari shine yadda ake banruwa da lambu,shinkafa da dae makamantansu

Tuesday 25 October 2016

AIRTEL yadda zaka samu 8times bonus recharge card and Data

ASSALAMU ALAIKUM WARAHAMATULLAH
barka da asuba da fatan kowa ya tashi lafiya sanunku da zuwa wanannan shafi mai albarka na sadeeqmedia blog
a kwanankin bayyani nayi muku bayyani akan yadda zaka samu 6times bonus recharge card a airtel yau kuma nazo muku da bayyani 8times bonus recharge card
YADDA ZAKA SAMU WANANANN GARABASA
NA FARKO   saya sabon layin airtel sai kayi register shikenan
ko kuma kayi amfani da wanannn code *311# ,idan ka samu ya koma samrtconnect. kayi sa'a
NA BIYU  yadda zaka gane cewa kana cikin wanannan tsari shine kana check balance zaka ga an nuna maka haka times 8xvoice,8xData da dae sauransu
kamar wananan hoto da kuke gani shine percentage nawa

FATAWAR RABON GADO (68)|DR JAMILU YUSUF ZAREWA

*FATAWAR RABON GADO (68)*
*Tambaya:*
Assalamu alaikum tambaya mutum ne ya mutu yabar mace da yan'uwansa shakikai ba yara kuma mahaifansa sun mutu to Meye kason matar tasa?
*Amsa:*
Wa alaikum assalam, za'a raba abin da ya bari gida:4, a bawa matarsa kashi daya, ragowar ukun sai a bawa 'yan'uwansa shakikai.
Allah ne mafi sani
20/10/2016
Amsawa:
*Dr Jamilu Zarewa.*

Monday 24 October 2016

(mp3)complete wa'azin kasa A Garin kano Ta Dabo 2016


*Wa'azin 'Kasa A Garin Kano Ta Dabo 2016*
➖➖➖➖➖➖➖➖➖➖➖
☑ Wadannan Sune Wa'azin Da Kungiyar Jama'atul Izalatil Bid'ati Wa'iqamatis Sunnah Ta Shirya Gabatarwa A Filin Wasa Na Sani Abacha Dake Kofar Mata anan Cikin Garin Kano
*WA'AZIN RANAR ASABAR NA DARE*
➖➖➖➖➖➖➖➖➖➖
Jerin gwanon wa'azozin kasa wanda aka gabatar a garin kano
yau asabar
001- Sheikh muhammad Aliyu adarawa
002- Sheikh jamilu albani samaru
003- Sheikh Abubakar Gero Arugungun
004- Sheikh muhammad usman bin usman kano
005- sheikh abubakar muktar jalingo
DOWNLOAD MP3
006- sheikh Kabiru haruna gombe
007- Sheikh Abdullah bala lau
*WA'AZIN RANAR LAHADI DA SAFE*
➖➖➖➖➖➖➖➖➖➖➖
001- Tare da Shekh Ahmad Taraba
003- Tare da Shekh Isah Alawy gombe da Alaramma birnin gwari.
004-Tare da Shekh Abdullahi ishaq garangamawa da Alaramma sani mai shayi manummafashi.
005- Tare da Shekh Khalid usman Khalid.
006- Daga filin wa'azi na safe
Tare da Shekh Dr Alhassan Saed jos da Alaramma Ibrahim yahuza bauci.
007- Tare da Shekh Dr Abdullahi saleh Pakistan Kano.
008- Hon Abdurrahman kawo sumaila
009- Tare da Sheikk Abdullahi bala lau da Alibaba agama lafiya da wakilin gwamna
   
DOWNLOAD MP3
AYI SAURARE LAFIYA

Saturday 22 October 2016

WA'AZIN KASA NA JAHAR KANO 2016 MP3

WA'AZIN KASA NA JAHAR KANO 2016 Mp3.
Jerin gwanon wa'azozin kasa na dare da aka
gabatar a garin kano.
sai ka danna wajen da anka rubuta download mp3 zai kaika inda zakayi download successful wassalam
001- Sheikh muhammad Aliyu adarawa
    Download mp3 .
002- Sheikh jamilu albani samaru
      Download mp3 .
003- Sheikh Abubakar Gero Arugungun
      Download mp3 .
004- Sheikh muhammad usman bin usman kano
    Download mp3 .
005- sheikh abubakar muktar jalingo
    Download mp3 .
006- sheikh Kabiru haruna gombe
           Download mp3
007- Sheikh Abdullah bala lau
        Download mp3
Jibwis social media Kano State.
Ayi sauraro lafiya.

Friday 21 October 2016

Mutane 53 sun rasa rayukansu a hadarin Jirgin kasa

Mutane 53 sun rasa rayukansu a hadarin Jirgin kasa
Hadarin Jirgin kasa da ke kan hanyar zuwa Yaounde
Rahotanni daga kasar Kamaru sun ce akalla mutane 53 ne suka rasa rayukansu a wani hadarin jirgin kasa.
Jirgin fasinjan yana kan hanyarsa ta zuwa birnin Yaounde daga Douala, a lokacin da ya kauce daga kan titinsa.
Kafin wannan hadari dai, wata gada da ke hada cibiyar hada-hada da ke hada Douala da Yaounde ta karye, hakan yasa mutane zabin shiga jirgin kasa.
Shaidun gani da ido sun ce yawan da jama’a suka yi cikin jirgin ya taimaka, wajen sabbaba aukuwar hatsarin.

Audio:- Wakokin Aminu Ala Guda Biyar (5) Ala Shahara

Assalamu alaikum warahamatullah yan uwana barka da yau da fatan kuna lafiya
a yau wanannan shafi mai albarka sadeeqmedia blog nazo muku da wakokin shahararen mawakin arewa wato Aminu  Abubakar Ladan wanda anka fi sani da aminu alan wakan wakokin rayuwarsa da gwagwarma da ya sha a rayuwarsa.
don kayi download wananan wakoki sai ka latsa ko wane daya bayan daya bar zuwa biyar,kana latsawa zai baka damar download

ALA SHAHARA 1

AYI SAURARO LAFIYA

FATAWAR RABON GADO (67)|DR JAMILU YUSUF ZAREWA

FATAWAR RABON GADO (67)
Tambaya?
Assalamu alaykum
Dr. Mace ce ta rasu ta bar uwayenta guda biyu da diya mata guda biyar, shin yaya rabon gadon ta zai kasance?
Amsa :
Wa alaikum assalam,  za'a raba abin da ta bari gida: 6,  a bawa mahaifanta kashi dai-dai, sai kuma a bawa 'ya'yanta kashi hudun su raba.
Allah ne mafi sani
19/10/2016
DR JAMILU ZAREWA

Thursday 20 October 2016

labari da dumi duminsa:A'isha Buhari Ta Samu Lambar Yabo A Taron Da Ta Halarta A Birnin Brussels(kalli hotuna)

A'isha Buhari Ta Samu Lambar Yabo A Taron Da Ta Halarta A Birnin Brussels
Lambar yabon wanda mataimakin Firayin Ministan kasar Belgium kuma ministan harkokin kasashen waje da harkokin kasashen Turai, Mista Didier Reynders ya mika mata a taro kan rawar da mata suka taka a fannin tsaro da aka gudanar a birnin Brussels, Uwargidan shugaban kasa A'isha Buhari ta sadaukar da lambar yabon ga dakarun sojojin Nijeriya da kuma maza da matan da suka rasa ransu sakamakon rikicin ta'addanci da kuma jami'an tsaron da suke fagen daga domin tabbatar da tsaro a yankin arewa maso gabashin kasar nan.



 

Da Yardar Allah Buhari Zai Zarce A Zaben 2019, Idan Ya Gama Kuma Ni Zan Maye Gurbinsa A Zaben 2023, Inji Hanarabul Gudaji Kazaure


Da Yardar Allah Buhari Zai Zarce A Zaben 2019, Idan Ya Gama Kuma Ni Zan Maye Gurbinsa A Zaben 2023, Inji Hanarabul Gudaji Kazaure
Dan Majalisa mai wakiltar Kazaure, Roni, 'Yan Kwashi a Majalisar wakilai ta tarayya daga jihar Jigawa, Honorobul Muhammadu Gudaji Kazaure a wani hira da aka yi da shi ya bayyana cewar idan Allah ya kai mu a  shekarar 2019 Buhari zai zarce da yardar Allah ko da abokan gaba ba sa so. Sannan ya kara da cewar bayan Buhari ya gama shekarunsa 8 a shekarar 2023 shi zai mikawa mulkin Nijeriya, wannan shine fatanshi.
Dan Majalisar, dukda yadda ya shahara da ba da dariya a dakin majalisar wakilai ta tarayya, a hirar da aka yi da shi ya nuna da gaske yake yi, domin a cewarsa, Nijeriya na bukatar shugaban kasa matashi, shugaban majalisar dattijai da na wakilai duka matasa, bayan Buhari ya gama nashi mulkin.
Masu karatu me za ku ce kan hakan?

Wednesday 19 October 2016

MUSULMI ZAI IYA SALLAH A COCI!|DR JAMILU YUSUF ZAREWA

MUSULMI ZAI IYA SALLAH A COCI ! !
*Tambaya:*
Assalamu alaikum, Malam  Shin ya halatta musulmai su yi sallah a coci kamar ranar juma'a ?
*Amsa:*
Wa alaikum assalam, da yawa daga malamai sun tafi akan haramcin hakan ko kuma karhanci saboda coci ba ta rabuwa da hotuna, kuma mala'iku ba sa shiga dakin da yake akwai hotuna ko kare a ciki, kamar yadda ya zo a Sahihil Bukhari.                                                                    
Ibnu Khudaamah ya rawaito halaccin sallah a coci mutukar tana da tsafta daga Umar dan Abdulaziz da Auza'i, da wasu jiga-jigan magabata,  ya Kafa hujja da cewa: Annabi s.a.w. ya yi umarni da mutum ya yi sallah duk inda ta riske shi, kamar yadda ya yi bayanin hakan a Al-Mugni 1/407.                                                        
Zance mafi inganci, In har akwai lalura ta rashin wurin sallah ya halatta musulmi ya yi sallah a coci kamar su rasa inda za su yi jumaa, kamar yadda Abu Musa Al-ash'ary ya yi sallah a wata Coci mai suna Nahya a Damashka, hakan ya zo a Musannaf a hadisi mai lamba ta: 4871,  in babu kuma to haramun ne.                                  
Allah ne mafi sani.
*Amsawa:*
16/10/2016
*DR Jamilu Zarewa.*

Tuesday 18 October 2016

Kyakyawar Budurwa Mai Gemu Ta Shiga Kundin Tarihin Duniya(kalli hotuna)

Kyakyawar Budurwa Mai Gemu Ta Shiga Kundin Tarihin Duniya

Daga Ahmadu Manaja Bauchi

A wani sabon rahoton hukumar ajiyar abubuwan tarihi a duniya “Guinness World Records” a bana sun bayyanar da wata matashiya mai shekaru 24 a duniya, a matsayin wadda ta lashe kambun shekarar 2017.

Harnaam Kaur, ‘yar asalin kasar Birtaniya, wadda take da yawan gashin fuska kamar namiji, ta bayyanar da labarin ta, a matsayin wani abun da ta sha wahala, domin kuwa idan aka ganta da gemu da gashin baki, sai a dinga tsokalanta.

Haka ya sa ta shiga cikin damuwa, amma daga bisani ta dauki cewar, wannan wata baiwa ce da Allah yayi mata. Tun tana ‘yar shekara goma sha biyu 12, ta fara gemu, a wannan lokacin ne aka duba lafiyar ta, aka gano cewar, jikin ta yana dauke da wani sinadari dake hana fitowar gashi a jikin mata, ita nata yana da karfi, don haka gashi zai dinga fitowa a jikin ta kamar namiji. Tun dai a wannan lokacin ne ta daina yanke gashin fuskar ta, yanzu haka dai gashin nata yakai tsawon zira’I ko a ce inci shida 6.

A yayin wani bukin nuna kawar kaya, Harnaam, ta gabatar da kanta a matsayin mace da tafi yawan gashi a tsakanin mata, hakan ya jawo hankalin mutane da dama a kasar Ingila.

Ta bayyanar da cewar, wannan baiwa ce daga Allah, don haka kada wani ko wata su raina irin baiwar da Allah ya yi musu a rayuwa. Hasalima sai su gode mishi, domin yanzu gashi ta shiga cikin tarihin duniya.

LATESTNEWS:Hukumar EFCC ta kama wani tsohon Gwamna da dan sa

Hukumar EFCC ta karo tado maganar Tsohon Gwamnan Jihar Adamawa, Murtala Nyako
– Hukumar EFCC ta kama Tsohon Gwamnan da kuma dan sa, Abdul Azeez Nyako
– Abdul Azeez Nyako dai Sanata ne yanzu haka a Majalisar Dattawa
Tsohon gwamnan jihar Adamawa, Murtala Nyako
Hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa ta kara kakkabe takardun Tsohon Gwamnan Jihar Adamawa watau Murtala Nyako, da kuma ‘Dan sa; Abdul Azeez Nyako da kuma wasu mutanen na dabam. Hukumar EFCC ta dai maka su kara ne Babban Kotun Tarayya da ke zaune a Abuja.
Hukumar EFCC ta kara shigar da karar Tsohon Gwamnan Jihar Adamawa, Nyako a Kotun Kasar gaban Alkali Okon Abang. A bara dai Hukumar EFCC ta shiga da Tsohon Gwamnan Kotu gaban Marigayi Alkali Evoh Chukwu. A nan ne Alkali Chukwu ya bada belin tsohon Gwamnan da kuma dan sa na Miliyan 350
Ana dai zargin Tsohon Gwamnan na Jihar Adamawa, Murtala Nyako da sauran da laifi kusan guda 37; wadanda suka hada da satar kudin Gwamnatin Jihar Adamawa har biliyan 29. Rotimi Jacobs ne dai Lauyan da ke karar su Murtala Nyako, yayin da Kanu Agabi yake kare wadanda ake zargi, Nyako da dan sa dsr.
Ana zargin anyi amfani da wasu Kamfani wajen aikata wannan laifin irin su Blue Opal, Sabore Farms, Pagoda Fortunes, Tower Assets… Yanzu dai Alkali Abanga ya daga shari’ar da wata guda har zuwa Tsakiyar Nuwamba. Yace kuma za su cigaba da zama cikin belin da aka basu a baya.

Monday 17 October 2016

sakon malam Aminu Daurawa Ga Rahama sadau

Sakon Malam Aminu Daurawa Ga Rahma Sadau
RAHAMA SADAU, HAKIKA Ki SANI MUSULINCI ADDINI NE WANDA YA YARDA DA IDAN MUTUM YA YI KUSKURE A KIRA SHI A GAYA MASA GASKIYA, A TUNATAR Da sHI AYOYIN ALLAH, KO YA GYARA.
KI SANI ALLAH YA YI NUFIN YA JARRABE KI YA GWADA IMANINKI SHI YA SA 'YAN UWANKI MASU HARKA FIM SUKA GUJE KI SAI KUMA GA WASU SUNA NEMANKI.
IDAN  AL'AMARIN YA INGANTA, TO MU SHAWARAR MU A NAN KAR KI AMSA KIRAN WANI KAFIRI DOMIN KE DAI MUSULMA CE KUMA MU MUSULINCIN KI SHINE ABIN DUBAWA A GAREMU.
DA ZA KI YI AURE MA SHINE ABINDA YA DACE DA KE. WANNAN HAKKI NE A KANMU MU SANAR DA KE ABIN DA ALLAH YA FADA, DOMIN AURE SHINE YA DACE DA 'YA MACE KO 'YAR WAYE A MUSULINCI.
WANNAN SAKO NE, JAMA'A A ISAR ZUWA GARETA.

Dole Buhari Ya Duba Korafin Uwargidansa Aisha- Majalisar Wakilai

Dole Buhari Ya Duba Korafin Uwargidansa Aisha- Majalisar Wakilai
* An Yi Wa Hirarrakin Buhari Da Aisha Gurguwar Fahinta - Gwamna Okorocha
________________________________________________
'Ya'yan majalisar wakilai na APC sun nuna goyon baya ga ikirarin Uwargidan Shugaban kasa, Hajiya Aisha Buhari inda ta nemi mijinta ya sake duba salon mulkinsa tun kafin wasu tsiraru su karbe ikon jagorancin kasar nan.
A cewarsu, alkawurran da aka yi 'yan kasa na sahihiyar canji yana neman ya zama mafarki kasancewa wasu sun yi katutu a gindin mulki tare da hana ruwa guda inda suka nemi a yi garanbawul a majalisar ministoci.
A bangarensa, Gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha ya bayyana cewa an yi wa hirar da Aisha Buhari ta yi da BBC gurguwar fahimta inda ya ce manufarta shi ne na neman hadin kan 'yan jam'iyyar da ke rikici da juna.
Haka ma, Gwamnan ya nuna cewa amsar da Buhari ya ba matarsa ba yana nufin ya kaskantar da jinsin mata ba ne yana mai cewa a gabansa Shugaban kasa ya yi wannan korafin na cewa aikin matarsa shi ne ta dafa masa abinci kuma ya yi shi ne a cikin raha.

Sunday 16 October 2016

FATAWAR RABON GADO (66)|DR JAMILU YUSUF ZAREWA

FATAWAR RABON GADO (66)
Tambaya?
Assalamu alaikum
Da fatan Malam yana cikin koshin lafiya. Don Allah a taimakeni da wannan: mata ta rasu babu miji, uwa ko uba, saidai diya mace da 'yan uwa mata guda biyu shakikai. Yaya rabon gadon zai kasance? Ka huta lafiya, na gode.
Amsa :
Wa alaikumus salam,
Za'a raba abin da ta bari gida biyu, a bawa' Yarta kashi daya, sai a dauki ragowar a bawa 'yan'uwan ta.
Allah ne mafi sani                      16/10/2016
DR JAMILU ZAREWA

BREAKING:customs Dismisses 17 officers for Drug Addiction certificate forgery

Customs Dismisses 17 Officers for Drug Addiction, Certificate Forgery
Seventeen (17) Junior Officers of the Nigeria Customs Service have been dismissed from the Service for offences ranging from drug addiction, certificate forgery, theft and absence from duty from January to September 2016.
2. The appointment of two other Officers have been terminated for absence from duty while one Officer was retired for drug addiction.
3. Investigations into offences committed by the Officers in the senior category are now being concluded. Officers found guilty are expected to face similar stiff penalties.
4. These disciplinary measures were taken after series of investigations and deliberations by the disciplinary committee and recommendations were made to the Management.
5. This process is a continuation of the reform agenda the Comptroller-General of Customs, Col. Hameed Ibrahim Ali (Rtd) promised upon his assumption of office which emphasized discipline, good conduct and transparency.
Signed
Wale Adeniyi
Public Relations Officer
For: Comptroller-General of Customs

LATEST :Ana zaman dar-dar a Kaduna

Rahotanni daga jahar kaduna dake arewacin Najeriya na cewa al’umma na zaman dar-dar sakamakon wani rikici da ya barke a jiya asabar a yayin da wasu mambobi na ‘yan uwa musulmi ta ‘yan Shi'a ke kokarin sake gina makarantarsu.
Wasu matasa ne suka soma far ma ‘yan shian a lokacin da suke kokarin gyare gyare a makarantar, rikicin ya sa mutane tserewa zuwa gidajensu, yanzu haka ma mazauna yankin sun ki fitowa don gudanar da ayyukansu na yau da kullum don gudun abinda zai biyo baya kamar yadda wani sheddun ganin da ido ya tabbatar.
Rahotanni na cewa ‘yan shia biyu ne suka mutu yayin da wasu goma suka sami rauni.

AN DAKATAR DA WASU JAMIAAN GWAMNATIN TARAYAR NAJERIYA BAKIN AIKI

Kakakin Ministan tarayyar Abuja Abubakar Sani yayi wa wakilin sashen Hausa Hassan maina Kaina dalilin wannan dakatarwan.
‘’Ba shakka wadannan jamiaan an dakatar dasu ne sabo da irin zarge-zargen da ake musu
Hukumar yaki da masu yiwa arzikin kasa zagon kasa wato EFCC, ta gurfanad dasu gaban kotu tana zargin su.
Kasan shi jamiin gwamnati yana iya gudanar da ayyukar sa kamar yadda doka ta tanadar, to kuma a duk lokacin da aka samu akasin haka, to kaga za a dauki matakai ire-iren wadannan, to wannan yakai ga har hukumar EFCC ta shigo cikin wannan batu.
Hukumar babban birnin tarayya ta yi haka ne, wato dakatar dasu domin ta baiwa hukumar ta EFCC cikaken damar gudanar da ayyukan ta.
Shiko Barister Aliyu Abdulahi lauya ne dake zaune a Abuja ga kuma abinda yake cewa game da wannan dakatar da maaikaran

Saturday 15 October 2016

HUKUNCIN WANDA YA SABAWA AYOYIN RABON GADO?|DR JAMILU YUSUF ZAREWA

*HUKUNCIN WANDA YA SABAWA AYOYIN RABON GADO*?
*Tambaya?*
Assalamu alaikum mallam menene hukuncin wanda ke kokarin ganin an baiwa mace  kason da aka bawa namiji wajen rabon gado?
*Amsa* :
Wa'alaykumussalam,
Ya sabawa Allah, Hakan kuma zai iya fitar da Shi daga musulunci in har ya yi gangancin hakan, saboda kokari ne na warware hukuncin da Allah ya zartar.                                                            Allah ya yi alkawarin wuta mai kuna ga duk Wanda ya sabawa ayoyin rabon gado a  cikin aya ta 14 a suratun Nisa'i.                      Wanda ya yi kira a daidaita namiji da mace a rabon gado saboda jahiltarsa da sharia ba za'a kafirta shi ba, Saboda ba duk Wanda ya aikata kafirci ba ne yake zama kafiri kamar yadda aya da hadisai da yawa suka tabbatar.  
Allah ne mafi sani.
04/10/2016
*DR JAMILU ZAREWA*