HAILA TA SAME NI BAYAN MIJINA YA SADU DA NI ?|DR JAMILU YUSUF ZAREWA - NewsHausa NewsHausa: HAILA TA SAME NI BAYAN MIJINA YA SADU DA NI ?|DR JAMILU YUSUF ZAREWA

Pages

LATEST POSTS

Monday 7 November 2016

HAILA TA SAME NI BAYAN MIJINA YA SADU DA NI ?|DR JAMILU YUSUF ZAREWA

HAILA TA SAME NI BAYAN MIJINA YA SADU DA NI ?
Tambaya:
Assalamu alaykum, Malam ina da tambaya,mace ce bayan mijinta ya sadu da ita, kafin ta yi wanka Sai jini  ya xo mata ya xa ta yi wanka, shin gabadai xatayi niyya ko kuma wannan na biyun xa tayi?
Amsa:
Wa alaikum assalam, za ta jira in ta samu tsarkin haila sai ta yi wanka daya kawai.                           
Yana daga cikin ka'idojin SHARIA Idan ibadoji guda biyu suka hadu, kuma manufarsu ta zama guda daya, sannan za'a iya hada su a lokaci guda, to sai daya ta shiga cikin dayar.
Wannan yasa mai janabar da jinin haila ya same ta kafin ta yi wanka, za ta wadatu da WANKAN karshe, saboda saukin musulunci da kuma daukewa jama'a abin da zai kuntata musu, kamar yadda aya ta karshe a suratul Hajj ta tabbatar  da hakan.            
Allah ne mafi Sani.
Amsawa: Dr Jamilu Zarewa.


Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment