HUKUNCIN HADA SITTU SHAWWAL DA RAMUWAR RAMADAN
Tambaya :
Malam idan ana binka ramuwar azimi za ka iya niyya biyu : wato da nufin sittu shawwal da ramuwar Ramadhana a guda daya ? don Allah mlm taimaka min da bayani.
Amsa :
To 'yar'uwa kowanne daban ake yinsa, saboda manufarsu ta banbanta, don haka ba za'a hada su da niyya daya ba, kamar yadda ake yi a wankan janaba da wankan juma'a, za mu fahimci haka, a cikin fadin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi :
"Duk wanda ya azumci Ramadhana sannan ya biyar da kwanaki shida na Shawwal, Allah zai ba shi ladan wanda ya yi azumin shekara"
Muslim ya rawaito shi a hadisi mai lamba ta : 1164, kin ga wannan yana nuna Ramadan daban, sittu-shawwal daban.
Fadin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi :
" Sannan ya biyar da kwanaki shida na Shawwal" ya sa wasu malaman sun tafi akan cewa : bai halatta ayi sittu-shawwal ba, sai bayan an kammala ramuwar Ramadan. Kamar yadda ya zo a : sharhurmumti'i 6\443
Allah ne ma fi sani
Amsawa
Dr jamilu zarewa
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment