HUKUNCIN BIN SALLAH DAGA LASIFIKA Tambaya : Malam gidanmu yana kusa da masallaci, muna jiwo kiran sallah da ikama ta lasipika, ko ya halatta in bi sallar jam'i daga laspika ?
Amsa : To 'yar'uwa wannan mas'alar ta kasu kashi biyu :
1- Idan ya zama dakinki yana like da masallacin, to tabbas wannan ya halatta, saboda nana A'isha ta bi sallar kisfewa rana daga dakinta, a zamanin Annabi s.a.w. kamar yadda Bukhari ya rawaito hakan a hadisi mai lamba ta : 184, sannan Abdurrazak ya rawaito cewa : takan bi ragowar salloli daga dakinta" kamar yadda ya zo a littafinsa na Musannaf a hadisi mai lamba ta : 4883,
saboda dakinta a jikin masallacin yake.
2.idan ya zama dakin ba ya hade da masallacin, to zance mafi inganci shi ne : bai halatta ki bi ba, saboda a zamanin Annabi s.a.w. sahabbai suna haduwa ne a wuri daya ne idan za su yi sallar jam'i, ba sa rarrabuwa, wannan sai yake nuna cewa,
hakan shi ne siffar sallar jama'i, sannan jera sawu a sallah, wani yana bin wani, dole ne . Allah ne masani . Don neman karin bayani duba : Fiqhunnawazil na Khalid Al- mushaikih shafi na : 50
Amsawa
Dr.jamilu zarewa
Dr.jamilu zarewa
BY Abubakar Rabiu Yari
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment