NewsHausa: FATAWA NewsHausa: FATAWA

Pages

LATEST POSTS
Showing posts with label FATAWA. Show all posts
Showing posts with label FATAWA. Show all posts

Friday, 24 August 2018

hukuncin wanda yake wasa da azzakarin sa maniyyi ya fito, Ko Kuma matar da take sanya yatsa a cikin farjinta

Malam menene hukuncin wanda
yake wasa da azzakarin sa
maniyyi ya fito ? Ko Kuma matar
da take sanya yatsa a cikin
farjinta ?
Amsa
..... Yin haka bai halatta ba kuma
yana daga cikin manyan laifu a
musulinci.

..... Yana janyowa mai yin hakan
fushi da kuma tsinuwa daga
ubangiji ( S.W.A )

..... Manzon Allah ( S.A.W ) yana
cewa "Mutum bakwai, Allah ya
tsine mu su. Kuma bazai dube su
da rahama ba ranar al-qiyamah.

..... Zai ce mu su Ku shiga wuta
tare da masu shigar ta.

1. Wanda yake yin Luwadi
2. Wanda ake yin Luwadin dashi
3. Mai yin zina da dabbobi
4. Mai yin zina da uwa/Mahaifiya
5. Sannan kuma yayi da 'yar ta
6. Mai yin zina da hannayen sa
(wato mai yin wasa da azzakarin
sa da kuma
7. mace mai yin hakan ga al'aurar
ta)

.....sannan shi kuma wannan aiki
yana daga cikin irin laifukan da
mutanen Annabi Lut ( A.S ) suka
aikata.

...... Sannan kuma an Ruwaito
cewar duk masu yin hakan idan
har basu tuba ba.

..... Zasu tashi a ranar al-qiyamah
Hannayen su dauke da ciki
( wato juna biyu )

..... Sannan kuma Likitoci masu
ilimin sanin lafiyar jikin Bil-adama
sun fadi wasu illoli da dama
wadan da yin hakan yake
haifarwa.

1. Mantuwa mai tsanani
( mantuwar karatu e.t.c )

2. Raunin idanu masu yin hakan
idan basu dai na ba, suka
makancewa kafin wani lokaci
mai nisa

3. Raunin Al-aura duk mai yin
haka, Idan suka yi Aure sukan yi
fama da rashin karfin Azzakari,
saboda duk maniyyin da aka fitar
dashi da gan-gan baya fita gaba
daya. Wannan wanda yayi saura
sai ya daskare maka a cikin
marar ka.

4. Rashin haihuwa: wan an
daskararren maniyyin yana kashe
kwayoyin halitta daga jikin
Namiji ko Mace.

5. Ciwon hauka da Kuma
kaskanci.

Wannan kadan na tsakuro daga
cikin irin illolin da yake haifarwa.
A jikin Namiji ko Mace.

Dan girman ALLAH kayi/kiyi
posting din wannan abin akallah
a cikin friends ka/ki koda guda
10 ne. Yadda kusan kowa zai
samu. Da groups din ka/ki
Wannan wadannan matsalolin a
halin yanzu muna facing din su a
rayuwa,

Allah yasa mu amfana
Via====> SADEEK M BAPPARU

Saturday, 9 June 2018

KARANTA WATA TAMBAYA DA AKA WA MALAM ISAH ALI PANTAMI DA TA SA YAYI KUKA YA ZUBAR DA HAWAYE

KARANTA WATA TAMBAYA DA AKA WA MALAM ISAH ALI PANTAMI DA TA SA YAYI KUKA YA ZUBAR DA HAWAYE

A tafsirin Al-Qur'ani Maigirma wanda Babban Malaminmu Ash-sheikh Dr. Isah Ali Ibrahim Pantami yake gabatarwa a darasin jiya Talata 20 ga watan Ramadan, wani bawan Allah ya rubuto takarda yake rokon Malam akan ya yiwa 'dan uwansa nasiha sakamakon bijirewa mahaifiyarsa da yayi har yace babu shi babu ita, kuma sunyi iya kokarin da zasuyi domin yaje ya baiwa mahaifiyarsa hakuri amma yaki
Da malam ya tashi gabatar masa da nasiha sai ya fara da cewa ashe har ana iya yin fada da iyaye a kaurace musu?

Babbar magana!, bil hakki ni dai tun da muka shiga Ramadan ban taba jin wata fitina da ta kai wannan girma ba ace mutum da iyayensa yayi fada har an rokeshi don ya basu hakuri amma yaki
Daga nan Malam ya kawo bayanan ayoyin Qur'ani da Hadisai na Annabi (saw) wanda suke nuni da falalar yiwa iyaye biyayya musamman mahaifiya, sannan ya kawo wata kissa wacce daga karshe sai da Malam ya fashe da kuka
Kissar itace kamar haka:

A zamanin sahabbai wani mutum ne yana neman budurwa sai ya kasheta saboda taki aurensa, sai yazo wajen Ibnu Abbas (ra) sai yace masa nayi zunubi maigirma, ban san me zanyi Allah ya gafarta min ba, ban san me zanyi ba a rayuwata na shiga damuwa
Sai Ibnu Abbas ya tambayeshi mai ya faru gareka? Sai yace wallahi budurwa nake nema taki aure na sai na kashe ta, Ibnu Abbas yace Innalillahi wa innaa ilaihi raji'un haka ka aikata? yace eh!, yanzu don Allah yaya za'ayi Allah Ya yafe min?
Tambayar farko da Ibnu Abbas ya masa shine shin mahaifiyarka tana raye? sai mutumin yace masa a'a bata raye, sai Ibnu Abbas yayi shiru, bayan tsawon lokaci sai yace to kaje kayi ta tuba kayi ayyukan alheri.

Sai daliban Ibnu Abbas sukace masa me yasa ka tambayeshi ko mahaifiyarsa na raye kuma da yace bata raye sai kayi shiru?
Sai Ibnu Abbas yace Wallahi ban san wani aiki na nagarta da mutum zaiyi ya nemi gafarar Allah Ya yafe masa ba kamar BIYAYYA ZUWA GA MAHAIFIYA, yace ban san wani aikin dake kaffara na zunnubai a duniya ba kamar biyayyan da mutum yake yiwa Mahaifiyarsa.." daga nan wajen ne sai Malam Isah Ali Pantami ya fashe da kuka har ma ya kasa cigaba da bayanin kawai sai ya umarci Alarammansa Malam Abdullahi Abba Zaria ya karanto ayoyin Qur'ani.

Ni kuma nace Malam Ya tuna da tashi mahaifiyar wacce Allah Yayiwa rasuwa watannin baya shi yasa yake kuka, ga wani kuma tashi mahaifiyar tana raye amma yayi fushi da ita (Allah Ya sauwake)
Wanda yake da bukatar karatun ya nemi tafsirin Qur'ani na ranar 20 ga watan Ramadan wanda ya gabata jiya talata
Gaskiya duk wanda Mahaifiyarshi take raye ashe yana da wata babban alfarma wanda zai iya gyara lahirarsa da ita.

Mu kyautatawa iyayenmu da suke raye domin mu gama da duniya lafiya mu kuma hadu da Allah lafiya
Allah Ka shiryar damu ka bamu ikon kyautatawa iyayenmu, wadanda suka rasa nasu iyayen Allah Ka jikansu Ka basu Aljannah don RahamarKa Amin
Sarauniya.

Monday, 21 May 2018

Mazan Aure: Abubuwa Da Ke Rage Karfin Namiji

Mazan Aure: Abubuwa Da Ke Rage Karfin Namiji

Binciken masana sun bayyana cewa wasu abubuwa da dama da kan rage karfin namiji daga cikin su akwai na’ukan abinci wadanda ke raunana karfin namiji wanda kuma ya zama wajibi duk wani magidanci ya rika Kiyaye wa don samun natsuwa da kima a idon iyali.

Shin ka taba samu kanka cikin wani yanayi na rashin jin sha’awar jima’i ko kuma kasa tabuka wani abu bayan samun biyan bukata, duk wannan zai iya kasancewa daga abincin da ka ci ne.

(1) Duk wani nau’in abinci wanda ke sa kiba, to yana raunana karfin gaban namiji misali nau’ukan abincin da ake soyawa da man gyada.

(2) Nau’ukan lemun kwalba da wadanda ake jikawa a ruwa da suka kunshi sikari ( Sugar) kamar su ‘ Soda’ da ice cream da sauransu duk suna tasiri wajen rage karfin namiji yayin jima’i.

(3) Duk wani nau’in abinci wanda aka sarrafa shi daga ainihin yadda yake a da kamar shinkafa da Alkama. Binciken masanan ya nuna cewa ya kamata magidanta su mayar da hankali wajen cin kayan marmari da na lambu.

Sunday, 8 April 2018

KOYAR DA KIMIYAR AURE Abubuwan Da ZAMZAM ISLAMIC COLLEGE Zata Koyar Guda (41) - Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa



Wannan makaranta ta ZAMZAM ISLAMIC COLLEGE ta shirya tsaf domin koyar da kimiyar zamantakewar aure, ga bangarori guda uku na maza mata
Zawarawa maza da mata 
Samari da Yammata
Mazan aure da matan su. 
Domin kara inganta rayuwa ta maaurata wadannan kwasa kwashe sun hada
1- Manufar yin aure
2 Hikimar yin aure
3 Falalar yin Aure
4-Hukuncin yin aure
5 - Yadda ake neman aure
6 - Irin matar da ake so a aura
7- Irin mijin da ake so a aura
8- Yadda ake zuwa zance da yadda ake yi
9_ Yadda ake bincike kafin aure da abubuwan ake bincikawa guda biyar
10- Mata guda 42 da suka haramta mutum ya aure su saboda nasaba ko shan nono ko surukuta.
11 Rukunan Daurin aure.
12 - Sadaki da hukunce hukuncin sa
13 Wanene Waliyyi da sharuddan zama Waliyyi da kashe kashen waliyyai na aure
14 Sigar daurin aure da yadda ake yin ta.
15 - Shedun aure da siffofinsu.
16- Sanya sharudda a cikin aure.
17 - Yadda ake bukukuwan aure a musulunci, da aladun da suka shigo cikin aure marasa kyau. 
18- Yadda ake walima da shagalin aure.
19- Ladubban tarewar amarya da Ango.
20 Hakkokin mata akan miji
21 Hakkokin miji akan mata.
22 Ladubban kwanciyar aure
23 Abubuwan da suke kara soyayya tsakanin maaurata.
24 Yadda ake gyara matsalolin aure idan sun taso.kafin akai ga saki 
25 Abubuwan da suke kawo albarka a gidan aure
26 Abubuwan da suka halatta, da wadanda suka haramta tsakanin maaurata a lokacin da mace take al'ada
27 Abubuwan da suke kawo mutuwar aure
28 Hukuncin hana daukar ciki, ko zubar da ciki, da Tsarin iyali a musulunci.
29 Sharuddan da mutum, zai cika kafin ya kara aure.
30 Wanda ya kasa daukan nauyin iyalinsa. 
31 Hukuncin wanda ya kauracewa iyalinsa. bisa zalunci ko larura ko horo. da sanin lokacin da shari'a ta iyakan ce. 

32 Mutuwar aure, da hukunce hukuncan sa,
33 Hakkokin matar da aka saka, 
34 Wa yake da hakkin rike yaya bayan mutuwar aure? 
35 - Yadda ake kul'i (mace ta nemi rabuwa) da abubuwan da suke jawo shi. 
36- Hukuncin komai bayan saki. 
37- Idda da hukuncin ta a musulunci 
38 - Hukuncin Ila'i Rashin kusantar iyali da rantsuwa ko saka sharadi. 
39-  Hukuncin Zihari kamanta jikin mahaifiyar sa da matarsa. Ko sauran mahramansa. 
40 Hukuncin lia'ni idan mutum yana zargin matarsa da zina. 
Reno da tarbiyya tun daga daukar ciki har zuwa haihuwa da yaye, 
Hakkokin yaya akan iyaye da hakkokin iyaye akan yaya. 
41 Yadda ake Takaba idan. Miji ya mutu.

Illolin Hassada Da Maganinta - Dr Jabir Sani Maihula


1) Hassada shine mutum yaji zafin wata ni'ima da Allah yayiwa wani bawan sa, koda baiyi fatar gushewar ni'imar ba. [Ibn Taymiyya da wasu malamai]
2) Hassada halin yahudawa ce [ Qur'an 2: 109, 4:54, 48:15]
3) Hassada tana kama wanda akayiwa ita, komai imanin sa; ta kama Annabi Yusuf (A.S), kuma Allah ya umurci Annabi (S.A.W) daya nemi tasri daga sharrin mai hassada [Qur'an 113:5].

4) Karanta azkar na safe da yamma, da karanta Fatiha, da karshen suratul Bakara, da ayatul Kursiy da suratul Falaq da Nas ya na kariya da ga hassada da bala'oi [hadissai da yawa]
5) Boye ni'ima ga wadan da ka ke tsammanin zasuyi ma hassada yana kareka daga hasada ya yardar Allah [quran 12:5].

6) Annabi (S.A.W.) yahana hasada, cikin hadissai dayawa cikin su akwai [ Muslim 2559]
7) Mai hassada yana fada ne da Allah, domin Allah shi yake yin ni'ima ga wanda yaga dama, kuma Allah shiyafi sanin wanda ya cancanta. [Malamai]
8) Mai hassada kullum yana cikin bakin ciki da bacin rai wanda ba lada akai [ laa tahzan, A'ed alQarny].

9) Hadisin da ya shahara na "Hasada tana cin ayyukkan..." bai inganta ba.
10) Allah yayi mana tsari daga hassada, yasa kada muyiwa wani, kuma ya tsare mu daga masu yi mana.

Monday, 12 March 2018

Yawun Bakin Budurwa Yana Kara Karfin Hadda Al-kur'ani inji Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum

 Sumbantar mace a baki yana da fa’ida matuka inji wani Shehin Malami

 Sheikh Guruntum yace miyau na Budurwa yana dada kaifin kwakwalwa

⏩Mai bukatar haddar sa ta zauna da kyau ya yawaita sumbantar iyalin sa

Wani Malamin addinin Musulunci ya bayyana cewa miyaun bakin mace yana da matukar amfani musamman ga masu kokarin hadda.



Sheikh Ahmad Tijjanu Yusuf Guruntum wanda babban Shehin Malamin addinin Musuluni ne a Garin Bauchi a wani karatu da yayi ya bayyana cewa miyaun mace yana da amfani kwarai domin yana kara kaifin harda sosai.


A addinin Musulunci ma dai sumbantar iyali abu ne mai kyau inda wannan malamin ya bayyana wani babban fa’idar da ‘daliban ilmi ba su san shi ba. Malamin ya kafa hujja da wani hadisin Annabi a littafin Sahihul Bukhari.

Dama dai masana a kimiyya tuni sun ce sumbanta a baki yana taimakawa wajen maganin ciwon kai da rage ciwon hawan jini, haka kuma ana so mata masu al’ada su rika yawan sumbanta domin rage radadin al’adar.

Saturday, 17 February 2018

Khudubar Ranar Juma'a Mai taken Sulhu Alheri ne Dr Muhammad Sani Umar R/lemo

Khudubar Ranar Juma'a

Mai taken Sulhu Alheri ne.

Dr. Muhammad Sani Umar R/Lemo

 Daga Masallacin Juma'a na Dorayi Kano

22/5/1439 = 9/2/2018


Download Audio Here

Source Darulfatawa.com

Sunday, 23 July 2017

[Audio] Download Raddi Mai Taken 'Babban Bola' ? Sheikh Bello Yabo Sokoto



RIGIJI GABJI! LALLAI ZA'A 'KARA MAIMAITA WATA RADDI KENAN MAI TAKEN BABAN BOLA KAMAR YADDA AKA YI NA MANI MAYE! TABBAS ASH-SHEIKH BELLO YABO SOKOTO YA KARKATO YEKUWAR MAGANARSHI IZUWA MASALLACIN SULTAN BELLO KADUNA. MAI GURI YA ZO, MAI TABARMA DOLE YA NADE. DON HAKA DOLE MU JANYE MU BAR MA MALLAM FAGEN.
!
 Mu'uzilanci  insha'Allah(T) karshen ki tazo a Sultan bello mosque  kaduna
!
"Za mu yiwa Malam Bola raddi ba zamu kyale shi ba" inji Ash-Sheikh Bello Yabo Sokoto

Mallam yayi wannan jawabin ne jiya asabar a majalisin karatun shi asa'ilin da yake karantun littafin Attargib wattarhib.



Ga Kadan Daga cikin Abubuwan da Wanannan Goron Gayyata Ya kunsa kafin ku saukar da shi 
!
ASH-SHEIKH BELLO YABO SOKOTO YACE; " Duk Wanda ya tabbatar da cewa Annabi Muhammad (SAW) manzon Allah ne toh shin ana cewa ga hadisi mallammai masana hadisi sun tabbatar da ingancinshi yace amma ai Mallam wa'ni bai ce haka ba ko kuma Mallam wa'ni bai yi aiki da hadisin ba?? Wai yanzu wassu mallammai aka sawa sharadi wai ko hadisi ya tabbata daga Annabi sai wai idan sunyi aiki dashi ko sun yi fatawa dashi. Toh kenan da wannan mallamin da manzon Allah (SAW) waffi wani girma?? Kenan in munka bi wanga 'ka'ida kenan wannan mallamin ya fi manzon Allah (SAW) girma. Don haka wannan rashin sanin addini ne yaa ku jama'a, wannan rashin ganin girman Allah ne. Imamu Malik aka so a sanya mana wai bamu isa muyi aiki da hadisin Annabi ba wai sai Imamu Malik ya bada approval.............
!
Jama'a akwai ban mamaki mutumin dake iddia'in Sunnah ya 'dauko 'kiyayya ya 'dora ma hadisan manzon Allah (SAW). Duk Nigeria Malamai na Sunnah da na bidi'a, mutumin da ya fito da hadisan manzon Allah (SAW) shine Ash-Sheikh Abubakar Mahmud Gumi Allah yayi mishi rahama. Mallam kullum zai yi karatun hadisi taken da yake yi shine; Karatun hadisi da aiki dashi shine zaman lafiya ga musulmi. Toh yau ga abun mamaki wani wadda adda alaka dashi shi ke bude baki yana cewa karatun hadisi da aiki dashi shine fitina ga al'ummar musulmi. Jama'a akwai ban mamaki ko babu?? Allah ka shiryar da Baban bola.
!
Amma Baban bola ya 'bace 'bata mai nisa tunda yaddauko 'kiyayya ya aza ma hadisan manzon Allah (SAW). Wallahi Tallahi Billahilladhi la'ilaha'illahuwa wannan 'bata ce ba shiriya bace. Wannan Sharri ne ba alkhairi bane kuma abun bakin ciki ne gare mu baki 'daya. Mun yi bakin cikin faruwar wannan lamarin kuma musamman ace a cikin zuri'ar Mallam Abubakar Mahmud Gumi ne anka samu wanga lamari akwai bakin ciki. Muna rokon Allah ka janye mana wannan fitinan kayi mana maganin wannan musibar. Kaga inda wani ne ba shi ba da sai muce 'kiyayya yake yi ga da'awar Mallam Abubakar Gumi don haka da'awarce ta Mallam yake so ya karya. Mallam ya ce karatun hadisi da aiki dashi kaiko ka ce duk fitintunun da muke ciki duniyar musulunci ba abunda ya kawo fitintunun illa hadisan nan. Kenan yayi ma Mallam raddi ko bai yi ba?? Yayi ma Mallam RADDI mu ko zamu bashi namu. Allah ya sani muna girma Abubakar Gumi amma girman da muke gani na manzon Allah (SAW) ya fi na Abubakar Mahmud Gumi domin shima Mallam Abubakar Gumi ya samo na shi girman ne ta hanyar manzon Allah (SAW). Saboda girmama manzon Allah (SAW) da yayi shiyyassa munka girmamashi.
!
Toh wallahi ko wacce zai taba manzon Allah (SAW) toh wallahi bamu ganin girma nai kuma baza mu 'kyale shi ba. Don haka wadannan tabargazozin da yayi wallahi zamu bi su 'daya bayan 'daya mu tarwatsa su baza mu 'kyale su ba. Manzon Allah (SAW) ya fi kowa girma a wurin mu. Duk wanda ya nuna 'kiyayya da hadisi zamu zare takobin 'kiyayya da shi, kuma 'kiyayya mai muni. Mai ya raba mu da 'yan bidi'a da 'yan 'darika?? Ba 'kiyayya ga Sunnah ba?? Sannan wani sai yazo don yana cikin mu ya ya'ki Sunnah kuma mu 'kyale?? Wallahi baza mu 'kyale shi ba.
!
......................... An wayi gari wai hadisin Sitta shawwal ne Baban bola zai ce wai akwai gwaranci a cikin larabcin. Kenan Shi yanzu Baban bola ya hi Annabi iya larabci, ya hi Imamu Malik da ya kawo hadisin iya larabci, duk dattijan da ac-cikin isnadin hadisin haddasana fulan, an fulan, an fulan an ayyubal ansari duk ya hi su iya larabci duk Baban bola ya hi su iya larabci. In baccin wani abu sai ince sakaran banza. Allah ya shiryar damu! Allah ya shiryar damu!! Abunda na fadi daidai Allah ya bani lada da ni daku da kunka saurara. Inda kuskure ya auku Allah ya yafe mini ya share shi cikin zukatanku. Subhanakallahuma was bihamdika Ash'hadu anla'ilaha'illa anta Astagfiruka wa'atubu ilaik.


Latsa wanannan adireshi na kasa don sauraren somin tabin wanannan anticipate  raddin, ko kuma ince Goron Gayyata Daga Bakin ASH-Sheikh Bello yabo Sokoto.


Download Audio Now


Sources: Engr Abu ibn Kamis

Monday, 29 May 2017

Addu’a A Asirce (1) Dr Muhammad Sani Umar R/Lemo

Ramadaaniyyat-Kashi Na Biyu - 2
                      Dr. Muhd Sani Umar
                       Addu’a A Asirce (1)

1. Allah (S.W.T) ya yabi Annabi Zakariyya (A.S) da cewa, ya roƙi Allah a asirce, yana mai cewa, (Lokacin da ya kira Ubangijinsa ya roƙe shi a asirce). Wannan ya nuna mahimmancin yin addu’a a asirce.


2. Yin Adda’a a asirce ita ce al’adar magabata na ƙwarai cikin wannan al’umma, Alhasan Al-Basri yana cewa, “Musulmai sun kasance masu matuƙar ƙoƙarin roƙon Allah, amma ba a jin su suna daga muryoyinsu wajen addu’a, suna yin ta ne da murya ƙasa-ƙasa, saboda Allah yana cewa, (Ku roƙi Ubangijinku cikin ƙasƙantar da kai da sussauta murya). [Al-A’raf, aya ta55”].[Ibnul Mubarak, Azzuhud, #140].


3. Allah ya yi umarni da a roƙe shi da murya ƙasa-ƙasa, kamar yadda ya gabata, domin yin haka ya fi nuna ikhalasin bawa da ƙasƙantar da kansa ga Allah.


4. Don haka yin gangamin addu’a abu ne da ba shi da madoga a cikin aikin magabata, in ban da a cikin ibadu da aka san ana yin su ne cikin jama’a, kamar addu’ar shayar da ruwa ko kusufin Rana da Wata, ko addu’ar alƙunut ko addu’ar liman a kan minbarin juma’a da makamantansu wadanda nassi ya zo da su.


Sources:darulfatawa.com

Thursday, 25 May 2017

Tsotson farjin Mace Yayin Saduwa!!! Dr Jamilu Yusuf Zarewa

Tsotson Farjin Mace Yayin Saduwa !!!

Tambaya :
Assalamu alaikum, M. Na kasance ina tsotsan azzakarin mijina, shi kuma yana wasa da gabana da harshensa kafin mu sadu, ina matsayin haka a addinin musulunci.

Amsa :

To 'yar'uwa hakan ya halatta, ba matsala a sharian ce, saboda an rawaito halaccin haka, daga magabata, daga cikinsu akwai Imamu Malik, saidai ya wajaba a tabbatar an tsaftace wurin musamman farjin mata, saboda a bude yake, sannan kuma wuri ne da ake yin haila, ake kuma zuba maniyyi, ga shi kuma yana kusa da wajan yin bahaya, wasu masana likitanci suna bada shawarar cewa : 

a dinga wanke wurin da gishiri kafin a tsotsa, saboda neman kariya
Allah madaukakin sarki a cikin suratul Bakara aya ta : 223, ya kwatanta mace ga mijinta da gona, wannan sai ya nuna dukkan bangarorin jikinta ya halatta a ji dadi da su, in ban da cikin dubura wacce nassi ya togace.

Allah ne mafi sani.

Duba : Mawahibul-jalil sharhin Muktasarul Khalil 3\406

©www.Darulfatawa.com

Friday, 17 March 2017

Sunayen Wadanda Suka Je Yakin Badar - Sheikh Aminu IbrahimDaurawa

Sunayen Wadanda Suka Je  Yakin Badar.

1shugaba Muhammad
(SAW).

2. Abu Bakar as-Shiddiq (RA)

3. Umar bin al-Khattab (RA)

4. Utsman bin Affan (RA)
5. Ali bin Abu Tholib (RA)

6. Talhah bin ‘Ubaidillah (RA)

7. Bilal bin Rabbah (RA)

8. Hamzah bin Abdul Muttolib (RA)

9. Abdullah bin Jahsyi (RA)

10. Al-Zubair bin al-Awwam (RA)
11. Mus’ab bin Umair bin Hasyim
(RA)

12. Abdur Rahman bin ‘Auf (RA)

13. Abdullah bin Mas’ud (RA)

14. Sa’ad bin Abi Waqqas (RA)

15. Abu Kabsyah al-Faris (RA)
16. Anasah al-Habsyi (RA)

17. Zaid bin Harithah al-Kalbi (RA)

18. Marthad bin Abi Marthad al-
Ghanawi (RA)

19. Abu Marthad al-Ghanawi (RA)

20. Al-Husain bin al-Harith bin Abdul Muttolib (RA)

21. ‘Ubaidah bin al-Harith bin Abdul
Muttolib (RA)

22. Al-Tufail bin al-Harith bin Abdul
Muttolib (RA)

23. Mistah bin Usasah bin ‘Ubbad bin Abdul Muttolib (RA)

24. Abu Huzaifah bin ‘Utbah bin
Rabi’ah (RA)

25. Subaih (maula Abi ‘Asi bin
Umaiyyah) (RA)

26. Salim (maula Abu Huzaifah) r.a. 27. Sinan bin Muhsin (RA)

28. ‘Ukasyah bin Muhsin (RA)

29. Sinan bin Abi Sinan (RA)

30. Abu Sinan bin Muhsin (RA)

31. Syuja’ bin Wahab (RA)

32. ‘Utbah bin Wahab (RA)
33. Yazid bin Ruqais (RA)

34. Muhriz bin Nadhlah (RA)

35. Rabi’ah bin Aksam (RA)

36. Thaqfu bin Amir (RA)

37. Malik bin Amir (RA)

38. Mudlij bin Amir (RA)
39. Abu Makhsyi Suwaid bin
Makhsyi al-To’i (RA)
40. ‘Utbah bin Ghazwan (RA)

41. Khabbab (maula ‘Utbah bin
Ghazwan) (RA)

42. Hathib bin Abi Balta’ah al- Lakhmi (RA)

43. Sa’ad al-Kalbi (maula HathiB-)
(RA)

44. Suwaibit bin Sa’ad bin
Harmalah (RA)

45. Umair bin Abi Waqqas (RA)
46. Al-Miqdad bin ‘Amru (RA)

47. Mas’ud bin Rabi’ah (RA)

48. Zus Syimalain Amru bin Amru
(RA)

49. Khabbab bin al-Arat al-Tamimi
(RA)
50. Amir bin Fuhairah (RA)

51. Suhaib bin Sinan (RA)

52. Abu Salamah bin Abdul Asad
(RA)

53. Syammas bin Uthman (RA)

54. Al-Arqam bin Abi al-Arqam (RA) 55. Ammar bin Yasir (RA)

56. Mu’attib bin ‘Auf al-Khuza’i (RA)

57. Zaid bin al-Khattab (RA)

58. Amru bin Suraqah (RA)

59. Abdullah bin Suraqah (RA)

60. Sa’id bin Zaid bin Amru (RA)
61. Mihja bin Akk (maula Umar bin
al-KhattaB-) (RA)

62. Waqid bin Abdullah al-Tamimi
(RA)

63. Khauli bin Abi Khauli al-Ijli (RA)

64. Malik bin Abi Khauli al-Ijli (RA) 65. Amir bin Rabi’ah (RA)

66. Amir bin al-Bukair (RA)

67. Aqil bin al-Bukair (RA)

68. Khalid bin al-Bukair (RA)

69. Iyas bin al-Bukair (RA)

70. Uthman bin Maz’un (RA)
71. Qudamah bin Maz’un (RA)

72. Abdullah bin Maz’un (RA)

73. Al-Saib bin Uthman bin Maz’un
(RA)

74. Ma’mar bin al-Harith (RA)

75. Khunais bin Huzafah (RA)
76. Abu Sabrah bin Abi Ruhm (RA)

77. Abdullah bin Makhramah (RA)

78. Abdullah bin Suhail bin Amru
(RA)

79. Wahab bin Sa’ad bin Abi Sarah
(RA)
80. Hatib bin Amru (RA)

81. Umair bin Auf (RA)

82. Sa’ad bin Khaulah (RA)

83. Abu Ubaidah Amir al-Jarah (RA)

84. Amru bin al-Harith (RA)

85. Suhail bin Wahab bin Rabi’ah (RA)

86. Safwan bin Wahab (RA)

87. Amru bin Abi Sarah bin Rabi’ah
(RA)

88. Sa’ad bin Muaz (RA)

89. Amru bin Muaz (RA)
90. Al-Harith bin Aus (RA)

91. Al-Harith bin Anas (RA)

92. Sa’ad bin Zaid bin Malik (RA)

93. Salamah bin Salamah bin
Waqsyi (RA)

94. ‘Ubbad bin Waqsyi (RA)
95. Salamah bin Thabit bin Waqsyi
(RA)

96. Rafi’ bin Yazid bin Kurz (RA)

97. Al-Harith bin Khazamah bin ‘Adi
(RA)

98. Muhammad bin Maslamah al- Khazraj (RA)

99. Salamah bin Aslam bin Harisy
(RA)

100. Abul Haitham bin al-Tayyihan
(RA)

101. ‘Ubaid bin Tayyihan (RA)
102. Abdullah bin Sahl (RA)

103. Qatadah bin Nu’man bin Zaid
(RA)

104. Ubaid bin Aus r.a.

105. Nasr bin al-Harith bin ‘Abd r.a.

106. Mu’attib bin ‘Ubaid r.a.
107. Abdullah bin Tariq al-Ba’lawi
r.a.

108. Mas’ud bin Sa’ad r.a.

109. Abu Absi Jabr bin Amru r.a.

110. Abu Burdah Hani’ bin Niyyar
al-Ba’lawi r.a.
111. Asim bin Thabit bin Abi al-
Aqlah r.a.

112. Mu’attib bin Qusyair bin Mulail
r.a.

113. Abu Mulail bin al-Az’ar bin Zaid
r.a.
114. Umair bin Mab’ad bin al-Az’ar
r.a.

115. Sahl bin Hunaif bin Wahib r.a.

116. Abu Lubabah Basyir bin Abdul
Munzir r.a.

117. Mubasyir bin Abdul Munzir r.a. 118. Rifa’ah bin Abdul Munzir r.a.

119. Sa’ad bin ‘Ubaid bin al-Nu’man
r.a.

120. ‘Uwaim bin Sa’dah bin ‘Aisy
r.a.

121. Rafi’ bin Anjadah r.a. 122. ‘Ubaidah bin Abi ‘Ubaid r.a.

123. Tha’labah bin Hatib r.a.

124. Unais bin Qatadah bin Rabi’ah
r.a.

125. Ma’ni bin Adi al-Ba’lawi r.a.

126. Thabit bin Akhram al-Ba’lawi r.a.

127. Zaid bin Aslam bin Tha’labah
al-Ba’lawi r.a.

128. Rib’ie bin Rafi’ al-Ba’lawi r.a.

129. Asim bin Adi al-Ba’lawi r.a.

130. Jubr bin ‘Atik r.a.
131. Malik bin Numailah al-Muzani
r.a.

132. Al-Nu’man bin ‘Asr al-Ba’lawi
r.a.

133. Abdullah bin Jubair r.a.

134. Asim bin Qais bin Thabit r.a. 135. Abu Dhayyah bin Thabit bin
al-Nu’man r.a.

136. Abu Hayyah bin Thabit bin al-
Nu’man r.a.

137. Salim bin Amir bin Thabit r.a.

138. Al-Harith bin al-Nu’man bin Umayyah r.a.

139. Khawwat bin Jubair bin al-
Nu’man r.a.

140. Al-Munzir bin Muhammad bin
‘Uqbah r.a.

141. Abu ‘Uqail bin Abdullah bin Tha’labah r.a.

142. Sa’ad bin Khaithamah r.a.

143. Munzir bin Qudamah bin
Arfajah r.a.

144. Tamim (maula Sa’ad bin
Khaithamah) r.a.
145. Al-Harith bin Arfajah r.a.

146. Kharijah bin Zaid bin Abi
Zuhair r.a.

147. Sa’ad bin al-Rabi’ bin Amru r.a.

148. Abdullah bin Rawahah r.a.

149. Khallad bin Suwaid bin Tha’labah r.a.

150. Basyir bin Sa’ad bin Tha’labah
r.a.

151. Sima’ bin Sa’ad bin Tha’labah
r.a.

152. Subai bin Qais bin ‘Isyah r.a. 153. ‘Ubbad bin Qais bin ‘Isyah r.a.

154. Abdullah bin Abbas r.a.

155. Yazid bin al-Harith bin Qais r.a.

156. Khubaib bin Isaf bin ‘Atabah
r.a.

157. Abdullah bin Zaid bin Tha’labah r.a.

158. Huraith bin Zaid bin Tha’labah
r.a.

159. Sufyan bin Bisyr bin Amru r.a.

160. Tamim bin Ya’ar bin Qais r.a.

161. Abdullah bin Umair r.a.
162. Zaid bin al-Marini bin Qais r.a.

163. Abdullah bin ‘Urfutah r.a.

164. Abdullah bin Rabi’ bin Qais r.a.

165. Abdullah bin Abdullah bin Ubai
r.a.

166. Aus bin Khauli bin Abdullah r.a. 167. Zaid bin Wadi’ah bin Amru r.a.

168. ‘Uqbah bin Wahab bin Kaladah
r.a.

169. Rifa’ah bin Amru bin Amru bin
Zaid r.a.

170. Amir bin Salamah r.a.
171. Abu Khamishah Ma’bad bin
Ubbad r.a.

172. Amir bin al-Bukair r.a.

173. Naufal bin Abdullah bin
Nadhlah r.a.

174. ‘Utban bin Malik bin Amru bin al-Ajlan r.a.

175. ‘Ubadah bin al-Somit r.a.

176. Aus bin al-Somit r.a.

177. Al-Nu’man bin Malik bin
Tha’labah r.a.

178. Thabit bin Huzal bin Amru bin Qarbus r.a.

179. Malik bin Dukhsyum bin
Mirdhakhah r.a.

180. Al-Rabi’ bin Iyas bin Amru bin
Ghanam r.a.

181. Waraqah bin Iyas bin Ghanam r.a.

182. Amru bin Iyas r.a.

183. Al-Mujazzar bin Ziyad bin
Amru r.a.

184. ‘Ubadah bin al-Khasykhasy r.a.

185. Nahhab bin Tha’labah bin Khazamah r.a.

186. Abdullah bin Tha’labah bin
Khazamah r.a.

187. Utbah bin Rabi’ah bin Khalid
r.a.

188. Abu Dujanah Sima’ bin Kharasyah r.a.

189. Al-Munzir bin Amru bin
Khunais r.a.

190. Abu Usaid bin Malik bin
Rabi’ah r.a.

191. Malik bin Mas’ud bin al-Badan r.a.

192. Abu Rabbihi bin Haqqi bin Aus
r.a.

193. Ka’ab bin Humar al-Juhani r.a.

194. Dhamrah bin Amru r.a.

195. Ziyad bin Amru r.a.
196. Basbas bin Amru r.a.

197. Abdullah bin Amir al-Ba’lawi
r.a.

198. Khirasy bin al-Shimmah bin
Amru r.a.

199. Al-Hubab bin al-Munzir bin al- Jamuh r.a.

200. Umair bin al-Humam bin al-
Jamuh r.a.

201. Tamim (maula Khirasy bin al-
Shimmah) r.a.

202. Abdullah bin Amru bin Haram r.a.

203. Muaz bin Amru bin al-Jamuh
r.a.

204. Mu’awwiz bin Amru bin al-
Jamuh r.a.

205. Khallad bin Amru bin al-Jamuh r.a.

206. ‘Uqbah bin Amir bin Nabi bin
Zaid r.a.

207. Hubaib bin Aswad r.a.

208. Thabit bin al-Jiz’i r.a.

209. Umair bin al-Harith bin Labdah r.a.

210. Basyir bin al-Barra’ bin Ma’mur
r.a.

211. Al-Tufail bin al-Nu’man bin
Khansa’ r.a.

212. Sinan bin Saifi bin Sakhr bin Khansa’ r.a.

213. Abdullah bin al-Jaddi bin Qais
r.a.

214. Atabah bin Abdullah bin Sakhr
r.a.

215. Jabbar bin Umaiyah bin Sakhr r.a.

216. Kharijah bin Humayyir al-
Asyja’i r.a.

217. Abdullah bin Humayyir al-
Asyja’i r.a.

218. Yazid bin al-Munzir bin Sahr r.a.

219. Ma’qil bin al-Munzir
bin Sahr r.a.

220. Abdullah bin al-Nu’man bin
Baldumah r.a.

221. Al-Dhahlak bin Harithah bin Zaid r.a.

222. Sawad bin Razni bin Zaid r.a.

223. Ma’bad bin Qais bin Sakhr bin
Haram r.a.

224. Abdullah bin Qais bin Sakhr
bin Haram r.a.
225. Abdullah bin AbuTausif di
Manaf r.a.

226. Jabir bin Abdullah bin Riab r.a.

227. Khulaidah bin Qais bin al-
Nu’man r.a.

228. An-Nu’man bin Yasar r.a.
229. Abu al-Munzir Yazid bin Amir
r.a.

230. Qutbah bin Amir bin Hadidah
r.a.

231. Sulaim bin Amru bin Hadidah
r.a. 232. Antarah (maula Qutbah bin
Amir) r.a.

233. Abbas bin Amir bin Adi r.a.

234. Abul Yasar Ka’ab bin Amru bin
Abbad r.a.

235. Sahl bin Qais bin Abi Ka’ab bin al-Qais r.a.

236. Amru bin Talqi bin Zaid bin
Umaiyah r.a.

237. Muaz bin Jabal bin Amru bin
Aus r.a.

238. Qais bin Mihshan bin Khalid r.a. 239. Abu Khalid al-Harith bin Qais
bin Khalid r.a.

240. Jubair bin Iyas bin Khalid r.a.

241. Abu Ubadah Sa’ad bin Uthman
r.a.

242. ‘Uqbah bin Uthman bin Khaladah r.a.

243. Ubadah bin Qais bin Amir bin
Khalid r.a.

244. As’ad bin Yazid bin al-Fakih r.a.

245. Al-Fakih bin Bisyr r.a.

246. Zakwan bin Abdu Qais bin Khaladah r.a.

247. Muaz bin Ma’ish bin Qais bin
Khaladah r.a.

248. Aiz bin Ma’ish bin Qais bin
Khaladah r.a.

249. Mas’ud bin Qais bin Khaladah r.a.

250. Rifa’ah bin Rafi’ bin al-Ajalan
r.a.

251. Khallad bin Rafi’ bin al-Ajalan
r.a.

252. Ubaid bin Yazid bin Amir bin al-Ajalan r.a.

253. Ziyad bin Lubaid bin Tha’labah
r.a.

254. Khalid bin Qais bin al-Ajalan
r.a.

255. Rujailah bin Tha’labah bin Khalid r.a.

256. Atiyyah bin Nuwairah bin
Amir r.a.

257. Khalifah bin Adi bin Amru r.a.

258. Rafi’ bin al-Mu’alla bin Luzan
r.a. 259. Abu Ayyub bin Khalid al-Ansari
r.a.

260. Thabit bin Khalid bin al-
Nu’man r.a.

261. ‘Umarah bin Hazmi bin Zaid
r.a. 262. Suraqah bin Ka’ab bin Abdul
Uzza r.a.

263. Suhail bin Rafi’ bin Abi Amru
r.a.

264. Adi bin Abi al-Zaghba’ al-
Juhani r.a.
 265. Mas’ud bin Aus bin Zaid r.a.

266. Abu Khuzaimah bin Aus bin
Zaid r.a.

267. Rafi’ bin al-Harith bin Sawad
bin Zaid r.a.

268. Auf bin al-Harith bin Rifa’ah r.a.

269. Mu’awwaz bin al-Harith bin
Rifa’ah r.a.

270. Muaz bin al-Harith bin Rifa’ah
r.a.

271. An-Nu’man bin Amru bin Rifa’ah r.a.

272. Abdullah bin Qais bin Khalid
r.a.

273. Wadi’ah bin Amru al-Juhani
r.a.

274. Ishmah al-Asyja’i r.a.
275. Thabit bin Amru bin Zaid bin
Adi r.a.

276. Sahl bin ‘Atik bin al-Nu’man
r.a.

277. Tha’labah bin Amru bin
Mihshan r.a.
278. Al-Harith bin al-Shimmah bin
Amru r.a.

279. Ubai bin Ka’ab bin Qais r.a.

280. Anas bin Muaz bin Anas bin
Qais r.a.

281. Aus bin Thabit bin al-Munzir bin Haram r.a.

282. Abu Syeikh bin Ubai bin Thabit
r.a.

283. Abu Tolhah bin Zaid bin Sahl
r.a.

284. Abu Syeikh Ubai bin Thabit r.a. 285. Harithah bin Suraqah bin al-
Harith r.a.

286. Amru bin Tha’labah bin Wahb
bin Adi r.a.

287. Salit bin Qais bin Amru bin
‘Atik r.a.
288. Abu Salit bin Usairah bin Amru
r.a.

289. Thabit bin Khansa’ bin Amru
bin Malik r.a.

290. Amir bin Umaiyyah bin Zaid
r.a. 291. Muhriz bin Amir bin Malik r.a.

292. Sawad bin Ghaziyyah r.a.

293. Abu Zaid Qais bin Sakan r.a.

294. Abul A’war bin al-Harith bin
Zalim r.a.

295. Sulaim bin Milhan r.a.
295. Sulaim bin Milhan r.a.

296. Haram bin Milhan r.a.

297. Qais bin Abi Sha’sha’ah r.a.

298. Abdullah bin Ka’ab bin Amru
r.a.

299. ‘Ishmah al-Asadi r.a.
300. Abu Daud Umair bin Amir bin
Malik r.a.

301. Suraqah bin Amru bin ‘Atiyyah
r.a.

302. Qais bin Mukhallad bin
Tha’labah r.a.
303. Al-Nu’man bin Abdi Amru bin
Mas’ud r.a.

304. Al-Dhahhak bin Abdi Amru r.a.

305. Sulaim bin al-Harith bin
Tha’labah r.a.

306. Jabir bin Khalid bin Mas’ud r.a.
307. Sa’ad bin Suhail bin Abdul
Asyhal r.a.

308. Ka’ab bin Zaid bin Qais r.a.

309. Bujir bin Abi Bujir al-Abbasi r.a.

310. ‘Itban bin Malik bin Amru al-
Ajalan (RA) 311. ‘Ismah bin al-Hushain bin
Wabarah (RA)

312. Hilal bin al-Mu’alla al-Khazraj
(RA)

313. Oleh bin Syuqra. (RA)
Allah Ya Yarda dasu amen

ku kasance da sadeeqmedia.com.ng domin yada sunnah

Wednesday, 15 March 2017

Ana Biyana Albashi, Amma Bana Zuwa Wurin Aiki, Yaya Hukuncina ? - Dr Jamilu Yusuf Zarewa

Ana Biyana Albashi, Amma Bana  Zuwa Wurin Aiki, Yaya Hukuncina ?

Tambaya

Assalamu Alaikum WarahmatulLAH? Barka da dare Dr dafatan kawuni lafiya Allah Yasa haka Shaikh Inada wata Tambayane ataimakamin da amsa. Dr, Matace tana aikin Gwamnati a wata jaha sai kuma barin Jahar ya kama su ita da mijinta ma'ana suka tashi kwata-kwata daga Wannan Jahar sai ya zama bata zuwa aikinta amma kuma Ana bata Salary duk wata amma Principal din makarantar da take aiki yana sane shi ya amince mata ta tapi sai kuma wani Ma'aikacin ma'aikatar Ilmi to amma ma'aikatar ba ta da masaniya to Dr Yaya kudin datake karba duk wata Ya halatta taci gaba da karba ko ta daina karba? don Abun yana damunta tana ta tunanin abun koda yaushe. Ataimaka min da Amsa Dr. Bissalaam

Amsa
Wa alaikum assalam,

Bai halatta ta ci ba, saboda albashi ana bayar da shi ne ga wanda ya yi aiki, halattawar da principal ya yi mata ba zai ba ta damar cin kudin ba tun da ba mallakarsa ba ne, kudin al'uma ne mabukata.

Hukuncin yana zagayawa ne tare da sanuwar dalilinsa ko rashinsa.

Zunubi shi ne abin da ya maka kaikayi a rai,kuma ka ji tsoran kar mutane su tsinkayo kai, kamar yadda hadisi ya tabbatar.

Allah ne mafi sani 

Amsawa

Dr.JamiluYusuf  Zarewa

22/02/2017

ku kasance da sadeeqmedia.com.ng a koda yaushe muna bukatar comments dinku na tambaya gyra ko karin bayyani

Kundin Masu Tuba Fitowa Ta Daya 001

KUNDIN MASU TUBA (001
Akwai wata Mace karuwa (Daga cikin Banu Isra'eel) tana da Sulusin kyawu. wato kamar yadda aka bama Annabi Yusuf (as) rabin kyawu, ita kuma kashi ɗaya cikin uku aka bata. 

Ita Karuwa ce amma Bata yarda wani yayi Zina da ita har sai ya bata Dinare 'dari. 

Akwai wani Mutum mai yawan ibadah watarana ya kalleta ta bashi sha'awa don hala yaje yayi ta aiki da hannunsa yana tara kudin har sai da ya tattaro dinare 'dari din nan sannan ya taho wajenta. 

Ya bata labarin dukkan abinda ya faru, sannan ta umurceshi ya shigo wajenta tana zaune akan wani gadon zinare. 

Har sai da ya kusa afkawa gareta sai ya tuna da tsayuwarsa agaban Allah. Nan take sai tsoro ya kamashi, jikinsa ya rika rawa. 

Sai ya tashi yace mata ki kyaleni in fita na bar miki dinare 'dari din nan. Sai tace "Menene ya faru gareka? Kace na baka sha'awa har kaje kayi aiki da hannunka ka tara wannan kudi, amma yanzu kuma gashi ka samu abinda kake nema amma ka tashi?".

Sai yace "Naji tsoron Allah ne kuma ina tuna ranar da zan tsaya agabansa, Don haka sai naji ina Qinki. Hakika yanzu kece wacce nafi Qi daga cikin Mutane".

Sai Matar tace "In dai abinda ka fada din nan gaskiya ne, to lallai babu wanda yafi chanchanta in aureshi sai kai".

Sai yace "To ki kyaleni dai in fita". 

Tace "Sai dai kayi mun alkawarin cewa zaka aureni".

Sai yace "To ki kyaleni in fita tukunna". Sai tace "To lallai ni nayi alkawarin zan biyoka domin ka aureni".

Sai yace "Watakil"... Sannan ya tashi ya sanya suturarsa ya fita ya koma garinsu. 

Ita kuma wannan Karuwa sai ta fito ta tuba tana yin nadama bisa abinda ta aikata a baya. 

Ta fito har sai da tazo garin da wannan mutumin yake, ta tambayi sunansa da kuma gidansa har aka nuna mata. 

Da aka sanar dashi cewa "Ga wata sarauniya nan tazo nemanka". Yana fitowa da ya kalleta (ya tuno da abinda ya kusa faruwa atsakaninsa da ita) sai yaja numfashi ya fadi akan hannunta ya rasu!. 

Sai tace "To wannan dai ya tsere mun. Amma shin yana da wani Makusanci?". Sai aka ce mata "Ga wani 'San uwansa nan amma Faqiri ne".

Sai tace "Na yarda zan aureshi saboda soyayyar da nake yiwa 'Dan uwansa".

Sai ta aureshi kuma Allah ya albarkaci auren nasu har sai da ta haifi Annabawa guda Bakwai.

Ibnu Qudaamah ne ya kawo wannan Qissar acikin littafinsa "KITABUT TAWWABEEN".

Ya Allah ka karbi tuban al'ummarmu ka gafarta mana zunubanmu ka sanyamu cikin Salihan bayinka ameeen.

Fassara daga Zauren Fiqhu  (14-03-2017).

Tuesday, 14 March 2017

Illar Munafinci - Sheikh Amin Ibrahim Daurawa

ILLAR MUNAFINCI

Alamomin Munafiki Hudu ne, Kamar yadda ya
tabbata a hadisin Bukhari da Muslum, da wuya
yanzu ka sami wanda bshi da ko daya daga cikin
wannan halin, sai wanda Allah ya tsare, Allah ya
kiyaye mu, ya gyara halayan mu. 

1-Karya

2- Saba Alkawari

3- Cin Amana

4- Yaudara

Allah ka rabumu da munafinci

Bacci Bayan Sallar Asuba - Dr Jamilu Yusuf Zarewa

Bacci Bayan Sallar  Asuba!!

 Tambaya

Assalamu alaikum, malam INA da wata
tambaya shin menene hukuncin yin bacci
bayan sallar asuba? Allah ya taimaki malam!

 Amsa:

Wa alaikum assalam.To malam babu wani hadisi mai inganci wanda ya hana bacci bayan sallar asuba, sai dai bayan sallar asuba lokaci ne mai albarka, wannan yasa Annabi S.A.W idan ya yi sallar asuba baya tashi daga wurin sallar sai rana ta fito, haka ma sahabbansa Allah ya yarda da su, kamar yadda Muslim ya rawaito a hadisi mai lamaba ta: 670.

Kuma Annabi s.a.w yana cewa: "Allah ka sanyawa al'umata albarka a cikin jijjifinta" Tirmizi a hadisi mai lamba ta: 1212, kuma ya kyautata shi.

Wannan yake nuna cewa lokaci ne mai
albarka, wanda bai dace da bacci ba,
wannan ya sa ko da rundunar yaki Annabi
s.a.w. yake so ya aika, yakan aikata ne afarkon yini saboda albarkar lokacin.

Wasu daga cikin magabata, sun karhanta
yin baccin bayan sallar asuba, Urwatu dan Zubair yana cewa : "Idan aka ce min wane yana baccin safe na kan guje shi' kamar yadda Ibnu Abi-shaiba ya ambata a
Musannaf dinsa 5\222.

Ya kamata ka shagala da neman ilimi ko
kosuwanci a irin wannan lokacin.

Allah ne mafi sani.

Amsawa

Dr. JamiluYusuf Zarewa
30/01/2015

Wednesday, 8 March 2017

Mace ,Za Ta Iya Yin Fitsari A Tsaye!!! -Dr Jamilu Yusuf Zarewa

Mace, Za Ta Iya Yin Fitsari A Tsaye!   !   !  ! 

Tambaya:

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakaatuhu, Don Allah malam mene hukuncin yin fitsari a tsaye ga mace ko namiji a Musulunci?

Amsa:

Ya halatta ga namiji ya yi fitsari a tsaye, saboda hadisin da Bukhari  ya rawaito cewa: "Annabi S.a.w ya je jujin wasu mutane sai ya yı fitsari a tsaye"kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi na 222... 
Tare da cewa duk hukuncin da ya zo dağa Annabi s.a w. yana hada mace da namiji, in ba'a samu abin da ya kebance shi ba, Tabbas fitsarin mace a tsaye zai jawo matsala wajan cikar tsarkinta, saboda yanayin halittar da Allah ya yı mata.
 Yana daga cikin Ka'idojin sharia gabatar da wajibi akan abin da aka halatta, yin fitsari a tsaye ya halatta ga mace, saidai zai kai ga kunci wajan tabbatar da Dhahara, wacce sallah ba ta ingantuwa saida ita.

Duk hadisan da suka zo cewa Annabi ya hana yin fitsari a tsaye ba su inganta ba, sai hadisin Nana A'isha wanda HakiM ya inganta, in da take cewa : "Duk wanda ya ce muku Annabi s.a.w ya yi fitsari a tsaye kar ku gaskata shi" kamar yadda  Nasa'i ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 29.
Malamai suna cewa : za'a dau maganarta akan tana bada labari ne, akan abin da ta gani, wannan ba ya kore a samu wani abin daban wanda ba ta sani ba, tun da  ba koyaushe take zama tare da shi ba, yana daga cikin Ka'idoji a wajan malaman Usulul-fiqhi : Duk  wanda ya tabbatar da abu za'a gabatar da maganarsa akan wanda ya kore, saboda wanda ya tabbatar yana da Karin ilimi na musamman wanda ya buya ga wanda ya kore.
Don neman Karin bayani duba : Sharhu Assuyudy ala Sunani Annasa'I 1\26.
Allah ne mafi sani. 

Dr Jamilu Zarewa 


8\3\2016


Monday, 6 March 2017

Musulunci A Mahangar Makiya -Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Musulunci A Mahangar Makiya

A kullum makiyan musulunci sun sawo mu a gaba,
 kamar masu laifi,  da tuhumai tuhumai,  akan
addninmu da al'adummu,
Suna tuhumar addininmu da cewa,  akwai abubuwa
goma da muke yi na takurawa mata,  Abin yana damun mu, amma Hanyoyin da ake bi
wajan magance , matsalar sai ake kokarin a biye
musu.

Masu Yin haka sun kasu kashi biyu, masu niyya mai
kyau, amma basu bi hanya mai kyau ba, wajan
kalubalantar wadananan akidu na turawa.

Na biyu masu Mummmunar aniya, Wadanda suke
so abiya wa wadannan turawa bukata, ta yadda
zamu karbi wadananan akidu na su na sukar
addini yadda suke bukata.

Abubuwan sune kamar haka:
Na daya maganar gado da ake bawa mata daya a bawa maza biyu.

a wasu guraran.

Na biyu kaciyar mata.

Na uku saka hijabi da nikab.

Na hudu shigar mata harkokin siyasa da
shugabanci.

Na biyar hukuncin kulle da neman izni kafin fita.
Na shida shekarun aure da auran wuri .

Na bakwai Maganar duka.

Na takwas auran mata fiye da daya.

Na tara AURAN DOLE .

Na goma haihuwar y'ay'a da yawa.

Wadannan abubuwa duka muna da amsoshi gamsassu akansu.
A biyo mu domin jin matsayin
addini akan wadannan abubuwa yadda addinin yake kallonsu.
Ba yadda turawa da yan korensu suke Fassara su ba.

Sunday, 5 March 2017

Dattin Zina !!! - Sheikh Aminu Ibrahim. Daurawa Kano

Dattin  Zina  !!!


Tabbas ! Duk zuciyarda ta cudanya da zina, to
wannan zuciya ta zama mai ha'inci kuma
ma'abocinta bazai taba zama cikakken mumini,
har se in ya tuba.


Bincike ya nuna cewa, idan mace tayi nisa cikin
zina, to babu minti daya a rayuwarta face ta
aikata zina, ko sha'awarta ta taso, kuma idan
bata samu biyan bukata ba, takan shiga wani
mummunan hali. 


Haka shima namiji idan zuciyarsa ta cudanya da zina, to zuciyarsa takan kawo masa sha'awar yi
da muharramansa, kamar uwarsa data haifeshi
ko
qannensa mata, wani lokacin zuciyar kan qawata
masa sha'awarsu.


Zina mugun ciwo ne da yake kashe ma'abocinsa
ta ciki kafin ya fito waje.


Zina idan tayi nisa a zuciyar mutum takan lalata
zuriyarsa, koda bayan ransa, za'a dinga samun
masu irin halinsa mazinata.


Dan haka Manzon Allah S.A.W yace, "mai zina
ba
mumini bane, ai bashi da imani lokacinda yake
aikata zina"


'Yan uwana, abokaina, mata da maza mu nisanci
zina, mu nisanci masu yinta, domin ita dabi'a ce
takanyi naso ne kuma matuqar kana tareda
mazinaci, to wataran shaitan zai qawata maka
sha'awar aikatata.


Ya Sarkin Sarakuna,
Ya Maji Roqon bayinsa
Ya Allah ka karemu da fadawa a cikin wannan
masifa, masuyi kuma Allah shiryesu su daina, ya
Allah gafarta mana zunubanmu .Amin

Saturday, 4 March 2017

Signs Of Weak Imaan -Dr Zakir Naik

.Signs Of Weak Imaan..!!

1. Committing sins and not feeling any guilt.

2. Having a hard heart and no desire to read the Quran.

3. Feeling too lazy to do good deeds, e.g. being late for salat

4. Neglecting the Sunnah.

5. Having mood swings, for instance being upset about petty things and bothered and irritated most of the time.

6. Not feeling anything when hearing verses from the Quran, for example when Allah warns us of punishments and His promise of glad tidings.

7. Finding difficulty in remembering Allah and making dhikr.

8. Not feeling bad when things are done against the Shariah.

9. Desiring status and wealth.

10. Being mean and miserly, i.e. not wanting to part with wealth.

11. Ordering others to do good deeds when not practising them ourselves.

12. Feeling pleased when things are not progressing for others.

13. Being concerned with whether something is haram or halal only; and not avoiding makroo (not recommended) things.

[Remember the Prophet P.B.U.H said if u have knowledge pass it on even if it is just one verse. So Forward this message and help us in our Mission to keep the Muslim Youth on the right path, ISLAM] #DrZakirNaik

Friday, 3 March 2017

Many Of Us Are Used To Missing Salah Giving Lame Excuses- Dr Zakir Naik

Many  Of Us Are Used To Missing Salah  Giving  Lame Excuses.

Are the excuses really Valid?

Allah (SWT) has said in the Noble Qur'an:
I have not created the jinn and humankind for any other purpose except that they should worship Me." (Noble Qur'an 51:56)
It is clear from the above verse of Noble Qur'an that the purpose of our birth and of our life is no other than that of the worship of Allah (SWT). 

There are many acts of worship (Ibadah, Ibadat) in Islam, and Salah is one of the most important obligatory acts.
Salah (Salat, Namaz) strengthens the foundations of our faith.

 It prepares a person to live the life of goodness and obedience to Allah (SWT), and it builds courage and determination. Every time we perform Salah, we renew our commitments to Allah (SWT) and we rid ourselves from worldly pressures five times a day.

According to a Hadith a companion of Holy Prophet Mohammad (pbuh) came to him one day and asked him "What is the thing that Allah (SWT) loves most?" Holy Prophet Mohammad (pbuh) replied "The thing that Allah (SWT) loves most is when his people pray Salah on time."

Salah (Salat, Namaz) is a practical sign of obedience to the commands of Allah (SWT). Its importance has been emphasized about 500 times in the Noble Qur'an.

Once Holy Prophet Mohammad (pbuh) shook a dry branch of a tree so that all of the leaves of the branch fell off than the Holy Prophet Mohammad (pbuh) said "The sins of those who pray Salah, drop off as the leaves of this branch fell off."

The last thing that Holy Prophet Mohammad (pbuh) emphasized at his death bed was Salah. He also said the first thing we will have to answer about on the day of judgement is Salah.

[Remember the Prophet P.B.U.H said if u have knowledge pass it on even if it is just one verse. So Forward this message and help us in our Mission to keep the Muslim Youth on the right path, ISLAM]