May 2018 - NewsHausa NewsHausa: May 2018

Pages

LATEST POSTS

Wednesday 30 May 2018

Kalli Sababbin Hotunan Jaruma Amina Amal Kyawawa

Wannan hoton sune sababbin hotunan jaruma amina amal wanda wannnan jaruma yar asalin kasar kamaru ne wanda tazo Nigeria sanadiyar shahararren dan fim mai suna adam a zango wanda wannan hotuna sun samu comments da likes sosai daga masoyanta.







Wannan hotuna sune da jarumar tayi posting a shafinta na instagram.

Anyiwa Karuwai Da Mashaya Korar Kare A Jihar Borno ( Kalli Hotunan )


Daga Aliyu Ahmad

Gwamnatin jihar Borno karkashin jagorancin Kashim Shettima ta bada wa'adin kwanaki uku domin soma rushe gidajen badala dake yankin Galadima da sauran wuraren badala dake kewaye da garin Maiduguri.

Wani kwamiti mai karfa da aka kafa kan lamarin karkashin jagorancin kwamishinan shari'a na jihar, Barista Kaka Shehu Lawan tare da goyon bayan ma'aikatar filaye na jihar, sun baiwa gidajen karuwan da na mashayan ranar 29 ga Mayu zuwa 2 ga watan Yuni da su tattara su bar yankunan ko kuma su fuskanci hukunci mai tsanani.

Za a rushe wuraren ne bisa dalilai na rashin mallakar filayen ba bisa ka'ida ba ko kuma yin gini bisa muhallan da ba su dace ba. Ko kuma yin ginin ba tare da mallakar takardu ba.

Wasu daga cikin otal din dake yankin Galadima a Maiduguri sun hada da;

* New Travels Hotel.
* Gondola Hotel.
* paragon Hotel.
* Chinners Hotel.
* Pampas Hotel.
* Favour land Hotel.
* Blue Sport Hotel.
* Sea Never Dry Hotel.
* Rall View Hotel.
* Okonna Hotel.
* Easy Guest in Hotel.
*  Peace Hotel.
* Chicago Hotel.
* Chrbos hotel.
* Benue Hotel.
* New Travelers 2 Hotel.
* Moonlight Hotel.
* Chobados hotel.
* Chiners 2 Hotel.
* Wazobia Hotel.





Otal din dake kan titin Baga a yankin Maiduguri sune kamar haka;

* Barka Da zuwa 1 Hotel.
* Barka Da zuwa 2 Hotel.
* Loyal City Hotel.
* Make we Flex Hotel.
* Favour land Hotel.
* Maintenance  Hotel.





Kwamishinan ya kuma kara da cewa babu wani daga kafa ko nuna idon sani a yayin da wa'adin kwanaki ukun suka cika.

Tuesday 29 May 2018

Rahama Sadau Ta Bada labarin Yadda Ta Rasa Budurcin Ta

Rahama Sadau Ta Bada labarin Yadda Ta Rasa Budurcin Ta

Rahama Sadau ta bada labarin yadda ta rasa budurcin ta
- Tayi wannan bayanin ne yayin da take yin fira da majiyar mu a satin da ya gabata
- Ta ce an taba yi mata fyade ne sadda tana yarinya karama ne

Fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Hausa a masana'antar Kannywood Rahma Sadau ta yi karin haske game da yadda ta rasa budurcin ta kamar dai yadda ta taba bada labarin cewa ita ba cikakkiyar budurwa bace ba a watannin baya.Jarumar dai ta yi wannan karin haske ne yayin da take yin fira da majiyar mu ta Mujallar fim a satin da ya gabata karon farko tun bayan dawowar ta daga kasar Turkiyya inda taje karatu.

Jarumar ta bayyana cewa maganar da tayi a watannin bayan na cewa ita ba cikakkiyar budurwa bace ba wai tana nufin ta taba zina ba ne domin ita hasali ma ba ta taba zina ba tun da Allah ya halicce ta.

Jarumar ta kara da cewa abunda take so ta fadawa duniya shine an taba yi mata fyade ne sadda tana yarinya karama kuma a lokacin ne ma ta rasa budurcin na ta kamar dai yadda ta fada.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa muhawara ta zafafa a watannin baya lokacin da jarumar ta bayar da ansa ga wani masoyin ta da ya tambayeta matsayin budurcin ta a kafar sadarwar zamani ta Instagram inda ta ba shi ansa da cewar ita ba cikakkiyar budurwa bace.

Sunday 27 May 2018

Kalli Yanda Yan Mata Ke yaudarar samari ta hanyar bilicin

Kalli Yanda Yan Mata Ke cutar samari ta hanyar amfani da man karin haske

wannan hoton wata mace kenan kalli yanda fuskar ta ta koma sakamakon shafe shafen mai

shin wai tambaya bilicin da mata keyi laifin maza ne ko laifin matan ne ?

Ado Gwanja a kasar Saudiyya

 Ado Gwanja a kasar Saudiyya

Tauraron mawakin mata kuma jarumin fina-finan Hausa, Ado Isa Gwanja kenan a kasar Saudiyya inda yaje aikin Umrah, muna fatan Allah ya amsa Ibada.

Kalli wani kayataccen hoton Hadiza Gabon


Tauraruwar fina-finan Hausa, me taimakawa gajiyayyu, Hadiza Gabon kenan a wannan hoton nata da ta sha kwalliya, tayi kyau, muna mata fatan Alheri.

Mawakin Rarara Ya Awon Gaba Da Kudin Kungiyar Mawaka Har Naira Milyan Dari


Rarara Ya Awon Gaba Da Kudin Kungiyar Mawaka Har
Naira Milyan Dari
JARIDAR DIMOKURADIYYA
Anyi cirko-cirko a Ofishin kungiyar mawaka tun bayan
bullar rahoton mawaki Dauda Kahutu Rarara yayi kwana
da makuden kudade sama da nera milyan Dari.

Shugaban kungiyar mawakan na yankin Arewa Haruna
Aliyu Ningi dake jihar Bauchi shiya bayyanawa manema
labaru, yace Gwamnan Jihar Zamfara shiya basu kudin
bayan sun bukacin hakan kan irin gudun mawar da suka
bayar a gabanin zabukan 2015 gashi kuma sun shirya
bayar da gagarumar gudun mawa a zabukan 2019 dake

tafeTunda farko Dauda Rarara shiya shige gaba wajen karbo
kudaden kuma ya tabbatar mun da cewar Gwamnan Jihar
Zamfara AbdulAziz Yari ya fara basu nera Milyan Sittin
sai dai wadanda suka yi hanya har aka bayar da kudaden
ya basu nera milyan goma sha takwas inji Haruna Ningi.

Ya kara da cewar a matsayina na shugaban kungiya har
zuwa yau Dauda bai taba yi mun maganar ba, bayan
lokacin dana sake tun tuba sa sai yace har yanzu ba’a
cika ragowar kudaden ba amma na kusa dashi wanda
shima yana daga cikin mawakan mai suna Oris yace tuni
an baiwa Rarara ragowar nera milyan Arba’in din.

To a hakan dai muka bukaci nera milyan Arba’in da biyu
da suka rage a hannun shi ya kawo su azo a zauna a
tattauna a kan su sai yace wai asusun ajiyar shi na banki
ya sami matsala.

Friday 25 May 2018

Kalli yanda tauraron fina-finan China, Jet Li ya koma

Kalli yanda tauraron fina-finan China, Jet Li ya koma
Wadannan hotunan dan wasan kasar China ne da aka fi sani da Jet Li, wani masoyinshine ya dauki hotunan tare da Shi a Tibet inda suka hadu, mutumin ya saka hoton a dandalinshi na sada zumunta kuma hoton ya dauki hankulan mutane sosai inda masoyan jarumin suka rika nuna damuwa da irin halin da suka ganshi a ciki.

Jet Li ya taba tabbatar da cewa bashi da lafiya a shekarar 2013 amma yace ba abune wanda yayi tsanani ba, akwai kuma rashin lafiyar kasa tsayuwa na tsawon lokaci da Jet Li din yake fama da ita wadda ya samo dalilin ciwo da ya taba ji a kafa a yayin daukar wani fim.

Wasu da suka ga hoton sun rika kokwanton anya shine kuwa, ba hadawa akayiba?.

Saidai me magana da yawun Jet Li din ya bayyanawa Washington post cewa tabbas wannan hoton na Jet Li ne saidai yanayin daukar da akamai ce tasa mutane ke

ganinshi kamar ya galabaita sosai, ya kuma tabbatar da cewa Jet Lin bashi da lafiya amma ba wani abune da zai tayarda hankalin mutane ba.

Thursday 24 May 2018

Kalli wasu kayatattun hotunan Rahama Sadau


Tauraruwar fina-finan Hausa da turanci, Rahama Sadau kenan a wadannan hotunan nata da suka kayatar, tasha kyau, muna mata fatan Alheri.


Wednesday 23 May 2018

Dalilin Dayasa Nayi Kiss A Wakar Classiq "Rahama Sadau"

Dalilin Dayasa Nayi Kiss A Wakar Classiq "Rahama Sadau"

Rahama Sadau ta bayyana Dalilin dayasa Tayi ma classiq kiss a wakar shi

danna rubutun dake kasa domin kallon videon a lokacin da tike jawabi

Download Now

Iyaye sun kai dansu dan shekaru 30 kara kotu akan ya fita ya bar musu gida su


Wasu iyaye a kasar Amurka sun kai dan su daya tilo dan shekaru talatin kara kotu saboda yazo ya zaune musu a gida baya biya musu kudin haya OK taimaka musu ta kowace irin hanya, sunce shekara takwas kenan suna zaune tare dashi.

Mark da matarshi Christina Rotondos dake zaune a birnin New York n a kasar Amurka, sunce kusan watanni hudu kenan suna baiwa dansu notis akan ya tashi ya basu guri amma yaki ya, sunce sun aikamai a rubuce, kuma har kudi suka bashi yaje ya kama haya amma duk ya kiya.

Sun kara da cewa kuma yaki neman aiki yayi.

Alkalin kotun da suka kai kara dai ya yanke hukuncin cewa Micheal ya tashi daga gidan ya baiwa iyayenshi guri.

Amma bayan kammala shari'ar, Micheal ya fito ranshi a bace ya kuma shaidawa manema labarai cewa baya tunanin alkalin kotun ya karanta bayanan da aka bashi da kyau dan haka be yadda da wannan hukumnci ba, zai daukaka kara.

Kalli ainihin hoton fulanin nan dake bayan Naira Goma

Kalli ainihin hoton fulanin nan dake bayan Naira Goma

Da dama muna ganin hotunan wadannan matan fulanin dake dauke da kwarya akansu dake bayan Naira goma, amma ba kowane ya taba ganin ainihin hoton nasu da akayi amfani dashi wajan yin kudin ba, to Albishirinku, bude ku gani.


Wannan ne ainihin hoton da akayi amfani dashi wajan yin kudin Naira Goma.

Akwai hassada da bakin ciki a masana'antar fim Rahama Sadau

Tauraruwar fina-finan Hausa Rahama Sadau na daya daga cikin wanda suka taka rawa suka kuma bar tarihin da ba za'a taba mantawa dashi a masana'antar fina-finan Hausa ba, tun daga shigowarta masana'antar, cikin kankanin lokaci ta samu daukaka ta kere sa'anninta.

Wani abu da ya faru da jarumar wanda za'a iya kiranshi da koma baya da ta samu,

shine dakatar da ita da akayi a shekarun baya dalilin fitowa da tayi a wani faifan bidiyo da suka yi waka tare da Classiq,

amma sai abin ya zamar mata sanadin kara daukaka, shararren mawakin kasar Amurka, Akon ya kirata, ta kara samun karbuwa a gurin fina-finan kudu.

Duk wanda yake da wata daukaka a tsakanin sa'anninshi ba zai rasa hassada da kishi ba:

Jar umar ta rubuta a dandalinta na sada zumunta da muhawara cewa:
Ba sabon abu bane hassada, bakin ciki da rashin kishin juna a masana'antar fim, musamman tsakanin mata.

Tuesday 22 May 2018

Kalli Hotunan Da Suka Jawo Ma Adam A Zango Cece Kuce A Shafikan Sada Zumunta

Kalli Hotunan Da Suka Jawo Ma Adam A Zango Cece Kuce A Shafikan Sada Zumunta.

Wadannan Hotunan sun jawo ma jarumi adam a zango cece kuce a shafin sada zumunta sakamakon ya rungume ta.




Ammah Wasu suna cewa wai yar uwar sa ce wannan ba wani abu bane.

Kalli Hotunan Wata Masara Mai Kaloli a jikin ta

Kalli Hotunan Wata Masara Mai Kaloli a jikin ta 

wannan hotunan wata masara ce da wani mai gona ya samu a cikin gonar sa.





Monday 21 May 2018

Kalli wata mata da ta mutu amma sai gata tana daka sakwara a wajan da za'a binneta

Kalli wata mata da ta mutu amma sai gata tana daka sakwara a wajan da za'a binneta

Wata mata me sana'ar sayar da abinci da ta mutu a kasar Ghana kenan a wannan hoton, ana bikin binne tane sai aka samu kujera aka zaunar da ita aka kawo turmi da tabarya da kuma sakwara, irin dai sana'ar da takeyi lokacin tana da rai.

Irin wannan shagali da akayi wajan binne ta ya dauki hankulan mutane domin ba kasafai aka saba ganin hakan ba.

Kalli hotunan 'Mala'ika da aka dauka a kasar Amurka'

Kalli hotunan 'Mala'ika da aka dauka a kasar Amurka'

Wannan wasu hotunan da wani mutum me suna Thorman ya dauka ne dake Michigan a kasar Amurka, kyamarar dake gidanshice ta dauki hotunan da dare inda za'a iya ganin wata halitta me fiffike a saman motarshi, Thormas dai yace wannan hoton mala'ikane.

Ya dauki hotunan ya kai cocinshi inda limamin cocin nashi ya tabbatar da cewa Eh! Lallai wannan mala'ikane dake karesu da dare idan suna barci.

Cocin ta saka hotunan a shafukan sada zumunta, kuma sun dauki hankulan mutane sosai inda wasu suka yarda cewa Mala'ikane a wannan hoton wasu kuwa cewa sukayi wani kwarone kawai.

The mercury news.