IDAN MASABUKI YA RISKI LIMAN A RAKA'A TA BIYAR YA SAMU JAM'I ?
Tambaya:
Assalamu alaikum,
Akramakallahu idan liman ya yi kuskuren kara raka'a daya, masbukin da aka tsere ma da rakaa daya za ta ishe shi idan Anyi baadiyya tare da shi?
Amsa:
Wa alaikum assalam, Allah ya taimaki shehinmu, malamai sun yi sabani akan wannan mas'alar zuwa zantuka biyu :
Akwai wadanda suke ganin za ta isar masa.
Sai dai abin da na fi nutsuwa da shi a raina, shi ne ba za ta isar masa, saboda mamu sallarsa tana like da ta liman ne, shi kuma liman ya zo da raka'ar a kuskure, wannan ya sa kamar yadda ba za ta amfani liman ba, haka ba za ta amfani mamu ba, wannan ita ce fatawar Sheik Ibnu Bazz da Sheik Abdulmuhsin Al-abbad.
Yana daga cikin ka'idojin sharia: mabiyi ba ya kebanta da hukunci.
Allah ne mafi sani.
Dr Jamilu Zarewa. 23 Ranadhan 1437
No comments:
Post a Comment