September 2016 - NewsHausa NewsHausa: September 2016

Pages

LATEST POSTS

Thursday 29 September 2016

YADDA AKE TURO APPLICATION A WHATSPP A WAYAR ANDROID CIKIN SAUKI

yadda tura application a whatsapp cikin saunki
wanannan nasan wasu zasuyi mamakin ya za'ayi a tura application a whatsapp wasu kuma sunji labari amma basu san yadda akeyi ba to yau in sha allah komai yazo karshe
hanya da zakabi ka turawa abokinka ko budurwaka application a whatsapp
abu na farko shine kaje cikin file dinka inda application dinka suke sai ka danne sosai sai ka yi rename zakaga misali snapchat.apk to sai kayi rename zuwa text
mataki na biyu sai kaje whatsapp dinka ka kayi (press) inda kake tura hoto ko video zakaga inda folder document. take sai ka shga kaje folder  da ka san kayi rename na application sai ka danna
sai kayi send shikenan
shi wanda ka turawa yana download zai nuna masa yayi installing
shikenan ALLAH. ya bada sa'a
domin karin bayyani ka tuntubi wanannan number 09032038203

Wednesday 28 September 2016

FATAWAR RABON GADO (59)|DR JAMILU YUSUF ZAREWA

*FATAWAR RABON GADO (59)*
Tambaya:                                                                                                                            Assalamu alaikum, Dr Allah ya karawa rayuwa albarka, tambayata itace mace ce ta rasu tabar mujinta da mahaifiyarta da shakikanta su uku abinda tabari an lissafa jimla 800,000 ya rabon zai kasance.
Amsa:                                                                                                                                        Wa alaikum assalam, Za'a bawa mijinta 400,000, sai a bawa mahafiyarta:  133,333.33333333, ragowar sai a bawa 'yan'uwa shakikai su raba, duk namiji zai dau rabon mata biyu.                                                                                            Allah ne mafi sani.
*Dr Jamilu Yusuf Zarewa*
27/09/16

To fa! MTN a ciki matsala, za ta sha bincike (Karanta dalili)

A ranar Talata, 27 ga watan Satumba ne ‘yan majalisar dattawa a Najeriya suka amince a gudanar da bincike a kan zargin cewa kamfanin sadarwa na MTN ya fitar da kudin da yawansu ya kai dala biliyan 13.92 daga kasar ta haramtaciyyar hanya.

Sai dai zuwa yanzu kamfanin na MTN ya ki cewa komai a kan wannan shawara da majalisar ta yanke.
Mutane miliyan 62 ne dai ke amfani da layukan MTN a Najeriya, lamarin da ya sa kasar ta zama kasuwarsa mafi girma a Afirka.
Zuwa bayan sallar azahar a ranar Talatar dai darajar hannayen jarin kamfanin ta yi kasa da sama da kashi hudu cikin dari.
Ba dai wannan ne karon farko da kamfanin MTN ke takun-saka da hukumomin Najeriya ba.
A watan Oktoban bara ma, hukumar da ke sanya ido a kan kamfanonin sadarwa, NCC, ta ci tarar kamfanin dala biliyan biyar saboda ya ki rufe layukan mutanen da ba su yi rijista ba har wa’adin da aka diba domin yin rijistar ya wuce.
Sai dai daga baya hukumar NCC din ta rage tarar zuwa dala biliyan uku da miliyan dari hudu.

Attahiru Bafarawa ya rubuta wasika ga Shugaba Buhari

– Tsohon gwamnan jihar Sokoto a karkashin Jam’iyyar All Nigeria Peoples Party (ANPP), Attahiru Bafarawa
– Bafarawa tsohon gwamna ne a Jam’iyyar ANPP, wanda daga baya zama cikin Shugabannin ta, itace kuma Jam’iyyar da ta far aba Shugaba Buhari tikitin tsayawa takara a kasar nan

Shi kan sa Attahiru Bafarawa, ya taba neman takarar Shugabancin Kasar a karkashin Jam’iyyar DPP. Bafarawa ya rubuta budaddiyar wasika zuwa ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari game da yadda zai samu nasara a mulkin sa. Idan ba a manta ba, Attahiru Bafarawa yana cikin iyayen gidan Jam’iyyar APC lokacin da aka kaddamar da ita, sai dai, daga baya ya fice abin sa.
Alhaji Dalhatu Attahiru Bafarawa yace wannan ne karo na hudu da ya rubuta wasika zuwa ga Shugaban Kasar Najeriyar, Muhammadu Buhari. Sai dai wannan karo Attahiru Bafarawa yace ya rubuta wasikar ta sa a bude. A cewar tsohon Gwamnan dai Kasar na fama da tarin matsaloli, don haka dole a sa hannu gaba daya wajen ceto Kasar.
Attahiru Bafarawa yaba Shugaba Buhari shawarar cewa ya duba wajen Jam’iyyar sa ta APC domin neman wadanda za su iya kawo karhsen matsalar da Kasar ta ke ciki. A cewar sa bah aka Shugaba Jonathan yayi ba, kuma bai zargi shugabannin baya ba. Bafarawa yace dole Buhari ya rika matso da Gwamnonin adawa jika, duba da irin yadda Shugaba Obasanjo yayi da Gwamna Bakura na Zamfara a lokacin sa. Yace dole kuma Buhari ya rika karbar shawara dage mutane da dama, musamman wadanda suka taimaka masa ya samu wannan matsayi.
Attahiru Bafarawa ya kuma kira Shugaba Buhari da ya karfafa Hukumar EFCC domin yaki da rashawar ya fi da. Kuma idan abin da gaske ne, a binciki ‘Yan Jam’iyyar sa ta APC, musamman wadanda suka tsero cikin ta don samun mafaka.
Tsohon Gwamnan Jihar Sokoton, Attahiru Bafarawa yace dole Buhari ya shirya jin suke daga bakin Jama’a duk kuwa dacin hakan.

Obasanjo yayi magana akan tabarbarewan tattalin arziki

Obasanjo ya tuhumci gwamnoni da laifin rashin tattali
– Tsohon shugaban yace duk da rashawan da ke gwamnatin sa,ba’a taba kudin fansho ba
A jiya ne 27 ga watan Satumba, tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya tuhumci gwamnoni da laifin tabarbarewan tattalin arziki.
Obasanjo
Yace tsaffin gwamnonin sun bada gudunmuwa wajen kalubalen tattalin arziki da kasa ke fuskanta a yanzu sabida sun kasance suna fito na fito da shi lokacin y ace a dinga tattali lokacin da farashin mai ke da armashi.
Obasanjo yayi magana ne a taron Fanshon duniya a Abuja inda yace gwamnoni da dama ne suka hana shi yin tattali lokacin da kasa ke da ishasshen kudi. He said: “I remember when I was in government and I told, particularly, the governors, ‘please let us save for the rainy days.’ They said no!
Yace: “Na tuna lokacin da nike gwamnati, a fada ma gwamnoni ,mu dinga tattali, sukayi kunnen kashi!”
Lokacin akwai kudi, yanzu da babu; babu inda mukayi tattalι
Bayan haka, Obasanjo ya yabi yadda ake gudanar da fansho. Yace duk da cewan an dau shekaru ana rashawa a najeriya, ba’a taba kudin fansho ba.
“Daya daga cikin abubuwan da nike farin ciki da su shine a shekaru biyar,lokacin da komai na kudi ana babakeren, ba’a taba kudin fansho ba. Ina da fahimtar kudin fansho wani abu ne da ya wajaba muyi tattali.”
A watan agustan 2016, Najeriya ta shiga cikin wata halin tabarbarewan tattalin arziki a lokacin na farko cikin shekaru 20. Ana jingina tabarbarewan ga hare-haren yan bindigan Neja delta key i akan kafufuwan man fetur.

Tuesday 27 September 2016

‘Yan Majalisar Dattawa ba su amince da Shugaba Buhari ba

– ‘Yan Majalisar Dattawan Kasar nan ba su yi na’am da tsarin Shugaba Muhammadu Buhari ba, na saida kadarorin Kasar
– Sanatocin Kasar sun ce a dai san yadda za ayi a fita daga kangin tattalin arzikin da ake ciki ba tare da an saida manyan kadarorin Kasa ba
Majalisa Dattawar Kasar ta bayyana wannan ne a zaman ta na jiya, Talata

A zaman ‘Yan Majalisar Dattawan Kasar nan a ranar, Talata 27 ga watan yau sun ce ba su amince da maganar sayar da manyan kadarorin Kasar ba, saboda radadin tattalin arzikin da aka shiga ciki. Shugaban Majalisar, Bukola Saraki ya yaba da kokarin ‘Yan Majalisar da gudumuwar da suka bada wajen muhawar game da batun.
Shugaban Majalisar Bukola Saraki ya bayyana cewa su dai sun yi irin na su rawar wajen ganin Najeriyar ta fita daga halin da ta shiga ciki na durkushewar tattalin arziki. Majalisar za tayi aiki tare da masu zartarwar wajen shawo kan matsalar da aka shiga. Shugaban Majalisar dattawar, Bukola Saraki yace za suyi aiki hannu da hannu tare da Shugaba Buhari wajen bada shawarwari da zantar da dokokin da suka dace, abin da Saraki ya kira alfanun Damukaradiyya
Majalisar Dattawar tace tayi nata kokarin wajen kawo karshen matsalar durkushewar tattalin arzikin Kasar. Haka shima Tsohon Shugaban babban bankin Kasar yace idan har aka samu damina mai kyau, to za a fita daga kangin da aka shiga a Kasar.
A jiya ne kuma dai Majalisar ta rantsar da sababbin ‘Yan Majalisar guda biyu, daga Yankunan Kogi da kuma Imo.

Wasu abubuwa 13 da suka sauya a Najeriya daga 1960

Najeriya ta samun yancin kai daga hannun turawan mulkin mallaka na Birtaniya a shekara 1960, daga lokacin zuwa yanzu, tsawon l
okacin zuwa yanzu da akwai abubuwa da yawa da suka canza a kasar, ga wasu 13 daga cikinsu.
Firayi minstan Nigeria na farko Tafawa Balewa tare da Ahamadu Bello Sardaunan Sokoto kuma Firimiya Arewa
1.Salon mulki: Daya daga cikin muhimman abubuwan da suka canza a Najeritya tun lokacin da kasar ta samu ‘yancin kai. A waccan lokaci Najeriya na bin salon mulkin ‘Parliamentary’ ne irin na Britaniya, a inda Firayi Minista ne ke da wuka da kuma nama a gudanar da mulki, yanzu kuwa kasar ta sauya zuwa ga tsarin shugaba mai cikakken iko irin na Amurka, watau ‘Presidential’.
2.Canjin kudi: Wani a muhimmin al’amari da ya sauya a Najeriya shi ne sauyin kudin kasar daga Fam da zuwa Naira da Kwabo a shekarun 1970.
3.Lissafin mita-mita: An koma lissafin mita-mita a maimakon mil-mil a nisan tafiya. Nisan gari zuwa gari daga mil ya koma kilomita da dangoginsa, hankan ya sauya lisssafin a kasar.
4.Tuki ya koma dama: Haka ma fasalin tuki a kasar ya sauya daga hagu wanda aka gada daga turawan mulkin mallaka zuwa dama.
5.Juyin mulki na farko: wani babban al’amari da ya faru a tarihi kasar shi ne shigar sojoji harkar siyasa bayan da wasu sojojin suka yi juyin mulki na farko a shekara 1965, a inda aka hallaka shugaban gwamnatin kasar da wasu manya-manya daga arewa da kuma kudu. Da wannan yunkuri soja a kasar suka dandana mulkin siyasa.

Tashin hankali lokacin yakin basasan Najeriya
6. Yakin Basasa: Kokarin da ‘yan kabilar Igbo suka yi na ballewa daga Najeriya ya haifar da yakin basasa a shekarun 1965 zuwa 1970, wanda hakan ya sauya yadda sauran kabilu ke kallon ‘yan kabilar Igbon da ma sauran kabilun kasar ta fuskar mu’amilla da zamantakewa.
7.Ayyukan Noma: A lokacin da Najeriya ta samu ‘yancin kai noma ne ke rike da kasar, kudu na fitar da Koko, da kwakwar manja, arewa kuma na fitar da fata, da gyada, da shanu da sauransu zuwa kasahen waje, a yanzu kuwa abin ya sauya, a yayin da kasar ce ke shigo da abinci.
8.Man fetur: Gano man fetur a kudu ‘yan  kadan bayan samun ‘yancin kai, ya sa kasar ta zamo mai arziki, hakan kuma ya sa abubuwa da yawa sun sauya, ciki har da hali da kuma dabi’un ‘yan kasar.
9.Sabbin jihohi: Janar Murtala ne ya fara kirkiro jihohi 12 a shekarun 1970, daga yakuna hudu da ake da su a shekarun 1960. Babangida kuma ya kara yawansu a shekarun 1990, wadannan sauye-sauye sun canza fasalin kasar matuka.
10.Abuja: Fadar gwamnatin tarayya ta tashi daga Legas da aka saba tun karbar yancin kai, zuwa Abuja, wani wuri na daban a tsakiyar kasar, hakan ya sauya alkiblar ‘yan kasar ta hanyar gudanar da mulki.
11.Bunkasar birane: Manyan garuruwa a shekarun 1960 ba su da yawa, amma a yanzu sakamakon kirkiro jihohi da habbakar tattalin arziki, an samu wasu garuruwan da a shekarun 1960 kauyuka ne, amma a yanzu sun zama kayatattun birane, sun kuma shahara.
12.Kimiyya da fasaha: A shekarun 1960 babban ma’aikacin gwamnati ko attajiri ne za iya sa waya a gidansa, amma a yanzu da sauyin na fasaha da kimiyyar zamani musamman ta fusakar sadarwa kowa ya wadata da wayoyin hannu na wadanda ke taimakawa gudanar da rayuwa cikin sauki.
13.Yawan tashe-tashen hankula: Harkokin siyasa, da na kabilanci, da na addinai sun yi tasirin da kwanciyar hankali ya yi karanci a yanzu, ba kamar a shekarun 1960 ba, a inda ake zaune lafiya da kwaciyar hankali.

Ma'aurata Zasu Iya Kallon Tsaracin Junansu? !!! |Dr jamilu yusuf zarewa


Tambaya?
Assalamu alaikum mallam menene matsayin kallon tsaraicin ma aurata?

Amsa :

Wa'alaykumussalam. Ya halatta ma'aurata su kalli tsaraicin junansu, Saboda Annabi s.a.w. yana wankan janaba da matansa, kamar yadda hadisai suka tabbatar.

Allah ne mafi sani.

Dr Jamilu Zarewa

Monday 26 September 2016

FATAWAR RABON GADO (58)|Dr.jamilu yusuf zarewa

FATAWAR RABON GADO (58)
Tambaya:
Assalamu Alaikum. mal Allah saka da gidan Aljannah. malam inatambaya mahaifiyata ce Allah ya amshi rayuwarta ta bar mahaifiyarta da maigidanta da ni  namiji 1 sai mata su 6. ya gadon zai kasanche. Allah yakara wa Malam lafiya amin
Amsa:
Wa alaikum assalam, Za'a raba abin da ta bari gida:12, Sai a bawa mijinta kashi:3, mahaifiyarta kashi:2, ragowar sai a bawa 'ya'yanta su raba duk namiji ya dau rabon Mata biyu.      
Aĺlah ne mafi sani
Amsawa: Dr Jamilu Zarewa.

BREAKING:Buhari approves new appointments in 13 FG agencies

– New appointments have been approved 13 federal government agencies
– Some of the agencies include NRC, ITF, SON and others

President Muhammadu Buhari has approved new appointments in 13 federal government agencies.
This was contained in a statement issued by the director (press) ) in the Office of the Secretary to the Government of the Federation, Bolaji Adebiyi.
Those appointed include
1. Joseph Ari as director general of Industrial Training Fund (ITF).
2. Dr. Isa Ali Ibrahim (Pantami) as director general of the National Information Technology Development Agency (NITDA)
3. Engineer Simbi Kesiye Wabote was appointed as the executive secretary of the Nigerian Content Monitoring Board.
4. Aboloma Osita Anthony is the new director general of the Standard Organization of Nigeria (SON).
5. Mamman Amadu was made the director general of the Bureau of Public Procurement (BPP).
6. Barrister Sharon Ikeazor is the executive secretary of Pension Transitional Arrangement Directorate (PTAD).
7. Princess Akodundo Gloria is the national coordinator/CEO of the New Partnership for Africa’s Development (NEPAD).
8. Alhaji Ahmed Bobboi was appointed as the new executive secretary of the Petroleum Equalization Fund (PEF).
9. Umana Okon Umana is the managing director of Oil & Gas Free Zone Authority.
READ ALSO: President Buhari appoints new key executives for NDPHC
10. Sa’adiya Faruq was made the federal commissioner for the National Commission for Refugees, Migrant and Internally Displaced Persons.
11. Engineer Usman Abubakar is the new chairman of Nigeria Railway Corporation (NRC).
12. Dr. Bello Aliyu Gusau was made the executive secretary of Petroleum Technology Development Fund (PTDF).
13. Yewande Sadiku was appointed the executive secretary of the Nigeria Investment Promotion Commission (NIPC).

Yadda zakayi download na hoto ko video a INSTAGRAM a wayar android cikin sauki

Yadda zakayi download hoto ko video a wayar ta android cikin sauki
Bismillahi Rahamani Raheem
Sanu da xuwa wanannan shafi sadeeqmedia.ml nasan mutane da dama suna mamakin wae akwae yadda zakayi download direct daga instagram to ka kwantar da hankalinka yau kaxo karshe
Abu na farko shine kayi download na wanannan instagram domin download ka yi click a nan
Bayyan kayi download kayi log in sai kaje wajen pics zakaga wanannan abubuwa sai kayi click
Zai nuna maka download sai kayi click shi kenan hí

Zakaga folder a cikin gallary dinka kamar
haka
Domin karin bayyani
Whatapp/call:09032038203

Tonan asiri: Dalilin da yasa kasar Najeriya ke da lalatattun Shugabanni

Bankole yace Najeriya na fama da mummunan shugabanci saboda lalatattun malamai
Tsohon kakakin majalisar Wakilai yace makomar kasar nan baida kyau

Dimeji Bankole, tsohon kakakin majalisar wakilai, ya daura laifin matsalolin shugabancin Najeriya a kan lalatattun malamai.
Wannan yazo ne yayinda tsohon kakakin yace makomar kasar baida kyau, jaridar Vanguard ta ruwaito.
Dimeji Bankole, tsohon kakakin majalisar wakilai ya daura laifin matsalolin shugabancin Najeriya a kan lalatattun malamai
A cewar shi, lalatattun shugabanni dake kasar a yanzu, wanda lalatattun malamai suka karantar a shekarun baya ne.
Yace: “makomar kasar nan baida alamun kyau. Akwai babban matsala. Gwamnati bazata iya biyan albashi da fansho ba. Idan kasar ta lalace a yau. Idan muna da matsalar shugabanci, saboda lalatattun malamai ne. najeriya na bukatar gyara.”
Da yake Magana kan kalubalan da karatu ke fuskanta, Bankole yace: “A yanzu, samun shiga makarantun jami’a ko Poly, dole sai dalubai sun samu maki da ya kai 160 zuwa 180 ko sama da haka.
“Haka kuma idan mutun zai shiga makaranta koleji sai ya samu maki 130. Wannan na nufin cewa tsarin yana zaben marasa kokari sosai ya kuma horar da su a matsayin malaman yayanmu.
“Idan muna zaben marasa kokari don su horar da kuma karantar da dalibanmu, ta yaya zamu sa ran dalibanmu su zama masu manyan rabo, idan duk cikin tsawon lokacin da suka dauka sun karatu, an ware su daga masu ilimi sosai aka kuma ba’a tursasasu sun kai matsayin wadanda sun kuma wuce wadanda basu samu shiga jami’a ba?”
Ya kara da cewa: “A halin da kasar Najeriya ke ciki a yanzu daliban makarantunmu basu da kokari. Wannan babban matsala ne! Me yasa muka bari hakan na faruwa?
Wannan ba abun wasa mane. Makarantun kolejinmu ya zamana su ke da mafi yawan maki, ta yanda zai jawo hankalin dalibai masu hazaka , saboda suna da muhimmanci sosai ga makomar kasar nan.”

Rikicin APC: Tinubu ya nemi Oyegun ya yi murabus

Rikici ya barke a jam'iyyar APC mai mulkin Nigeria bayan da tsohon gwamnan Lagos Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga shugaban jam'iyyar na kasa da ya yi murabus.
Mista Tinubu ya zargi John Odigie-Oyegun da yi wa "demokuradiyya zagon kasa" sakamakon rawar da ya taka a zaben fitar da gwani na jam'iyyar a jihar Ondo.
A wata sanarwa da ya fitar a daren ranar Lahadi, jagoran na jam'iyyar APC ya ce Mista Oyegun ya karya ka'idojin demokuradiyya da aka shimfida jam'iyyar a kai.
Ya ce an kafa APC ne a kan turbar adalci da demokuradiyya, sai dai ya ce wadannan abubuwa na fuskantar barazana daga wadanda ba su da asali a jam'iyyar.
Sakamakon zaben na jihar Ondo, wanda Rotimi Akeredolu ya lashe, ya bar baya da kura, domin dan takarar da Tinubu ya ke goyon baya, Segun Abraham, ya yi watsi da shi.
Kawo yanzu dai Mista Oyegun ko kuma shugabancin jam'iyyar ta APC ba su ce komai game da wannan batu ba.
Martanin Shugaba Buhari
Sanarwar ta Mista Tinubu ta ce wadanda suka kafa jam'iyyar sun fahimci cewa adalci ne zai sa ta karbu sannan jama'a su aminta da tsarin cigaban da aka kafa ta a kai.
A cewarsa: "Idan jam'iyyar ba za ta yi adalci a kan kanta ba, to zai yi wuya ta samar tare da kafa gwamnati mai adalci
a fadin kasar".
Mista Tinubu ya ce a baya jam'iyyar ta zama abar misali na adalci da shimfida tafarkin demokuradiyya tsakanin 'ya'yanta da kuma 'yan kasar baki daya.
Amma, a cewarsa, "a yanzu wadancan alkawura abubuwa ne kawai da ake fada a baki wadanda babu su a aikace, kuma Oyegun ya yi watsi da wadannan turaku da aka kafa jam'iyyar a kansu".
Tsohon gwamnan, wanda ya taka rawa wurin hadakar da ta kai ga kafa jam'iyyar, ya ce an tafka kurakurai ta hanyar sauya sunayen wakilai a zaben fitar da gwanin da aka yi a Ondo.
Ya ce duk da cewa sakamakon bai masa dadi ba, amma ya rungumi kaddara saboda imanin da ya yi da tafarkin demokuradiyya, amma daga baya ta bayyana cewa an tafka magudi.
Wannan shi ne rikici mafi girma da yake fuskantar jam'iyyar ta APC a kasa baki daya tun bayan kafa ta da kuma hawan ta mulki a shekarar 2015.
Masu sharhi za su zuba ido su ga yadda za ta kaya - musamman irin martanin da Shugaba Muhamamdu Buhari ko na kusa da shi za su mayar.

Dalilai 7 da Arewacin Najeriya ba sa so Najeriya ta rabu

Kasar Najeriya kasa ce wadda take a yammacin Afrika
Hanyoyin yin safara na ruwa suna yankin kudancin Najeriya
-Yawancin masu ilmin Boko suna yankin Kudu
Najeriya kasa ce wadda take a yammacin nahiyar Afrika, wadda take da fadin kasa na fadi da tsawon kilo mita 923,768, kasar Najeriya tana da iyaka da kasar Chadi ta gefen Arewa maso gabas, iyakar kasar kum da Kamaru tana ta Arewa maso gabas, daga iyakar ta ta kudu kuma tayi iyaka da Atlanta, tayi iyaka da kasar Niger ta yankin arewa maso kudu, iyakokin Najeriya da Chadi da kuma Najeriya da Kamaru akwai lokacin da kowa ke gadarar gurin shi ne, har y kawo rikici tsakanin iyakokin.
Kasar Najeriya tana da yarurruka fiye da 50, amma yarurrukan da suka fi rinjaye su ne Hausa/Fulani masu kaso 28%, sai yaren Yarbanci wanda yake da kashi 21%, sai yaren Inyamuranci/Ibo wanda ke da kaso 18% na yarurrukan.
Hausa/Fulani suke zaune a arewacin Najeriya wanda ya hada da jahohin Sokoto, Adamawa, Kano, Jigawa, Bauchi, Nasarawa da sauransu, sai Yarbawa da suk mamaye yankin kudun masu yamma na kasar wanda ya hada da jahohin Oyo, Ondo, Osun, Ogun da sauran su, sai
Inyamurai/Ibo wadanda suke yankin Kudu maso gabashin kasar masu jahohin da suka hada da Imo, Abia, Anambra, Enugu da sauran su.
Yaren da ake amfani da shi na kasar a gwamnatance shine yaren turanci, sakamakon turawan mulkin mallaka da su ka raini kasar.
Najeriya tana da addinai da mabiya, amma addinai da suke da yawancin mabiya sune addinin musulunci da Kiristanci sai yan kalilan masu yin addinan gargajiya, kusan kaso 90 na mutanen da Ke arewacin Najeriya suna bin addinin Musulunci, sai kashi 85 na mazauna kudan cin da Ke bin addinin kiristanci, addinin musulunci yayi karfi a arewa a dalilin jahadin Shehu Usmanu Danfodiyo, shi kuma Kiristanci yana da karfi a yankin saboda fara saukar Mishinari a yankin na kudu.
Kasar Najeriya tan da jahohi 36 da babban birnin tarayya Abuja, Najeriya kasa ce mai arziki wadda ta dara kowacce kasa a Nahiyar Afrika saboda suna da sukayi na samar da man fetur, Kwallin kura, Roba, Zinare, Noma da sauran su.
Taswirar Najeriya
Wadan nan dalilan guda 7 a kasa sune suka sa arewacin Najeriya ba sa son Najeriya ta rabu.
1. Ilimin Boko
Ilimin Boko yana 1 daga cikin dalilan da yan arewa basa son a rabu, saboda yana da karfi a yankin kudu a dalilin fara saukar turawan mulkin mallaka a yankin, wanda a lokacin arewacin Najeriya suna ganin kamar wani ra’ayi ko akida za’a tura masu, wanda a halin yanzu arewacin suna gajiya da ilimin na boko.
2. Kasuwanci
Duk da yake kusan cibiyar kasuwanci ta Najeriya tana Kano arewacin Najeriya, amma kudancin Najeriya su suka fi kasuwanci, garuruwa kamar kamar Aba, Lagos, Onitsha, Ibadan ana huldodi na kasuwanci kuma ana kawo wasu abubuwa da babu su a Kano, wannan shima ze Iya zama dalili,
3. Masana’antu ko Kamfanoni masu zaman kansu
Yawancin ma’aikatu da Kamfanoni suna yankin kudancin kasar, kuma suna cikin abubuwan da suka habaka yankin, wanda in ka lura babu su a arewa, koma akwai to basu da yawa ko basa aiki.
4. Man Fetur
Rashin man fetur shima ze Iya zama babban dalili saboda shine kusan abinda kasar ta dogara da shi, dan haka in aka raba kasar, arewacin Najeriya zasu rasa tudun dafawa.
5. Hanyoyin safara na ruwa
In zaka yi la’akari yawancin hanyoyi da ake shigowa da kaya ko fita da su ta ruwa suna yankin kudan cin kasar, wanna shin abun da y daga Kasuwancin su da samun kudin shiga na yankin, in kasar ta rabu wannan ze kawo babban Kalu bale a yankin Arewa.
6. Samar da tsintsaye da kayan marmari
Tsintsaye da kayan mamari da abincin tsintsaye duk yawanci ana samun sune a kudancin kasar, wanda kuma wadan nan ababe sun zama abun amfanin yau da kullum, wannan kadai ze Iya kawo cikas a yankin na Arewa.
7. Kirkire-Kirkire
Yawancin yan Arewa sunfi yin noma su aika amfanun gonan a yankin Kudu, su kuma su sarrafa ta hanyoyi da dama, kuma har yau kudan cin Najeriya suna amfani da kayan al’ada wanda arewacin wasu suka watsar, wannan ma ze iya zama na kasu ga Arewa in kasar ta rabu.

FATAWAR RABON GADO (57)|Dr jamilu yusuf zarewa

FATAWAR RABON GADO (57)
Tambaya?
Assalamu alaikum Mlm ina da tambaya, idan mace ta mutu ta bar 'ya mace guda daya, da dan"uwa shaqiqi daya, da jikokinta na da namiji 24 maza 14 mata, dan Allah mlm yaya rabon gadon zai kasance?, Allah ya saka da"alkhairi.
Amsa:
Wa alaikum assalam, Za'a raba abin da ta bari gida biyu, a bawa 'Yarta kashi daya, ragowar sai a bawa jikokinta, duk namiji ya dau Rabon mata biyu.                          
Allah ne mafi sani.
Amsawa: Dr Jamilu Zarewa                                   24/9/2016

Sunday 25 September 2016

Tambuwal lays foundation for a new school in Gudu, the only LGA without senior secondary school in Nigeria

Tambuwal lays foundation for a new school in Gudu, the only LGA without senior secondary school in Nigeria
Governor Aminu Waziri Tambuwal at the weekend laid the foundation for the construction of a new secondary school in Balle, headquarters of Gudu Local Government, with it closing the chapter for the town being the only LGA without a secondary school in Nigeria.
Speaking at the event attended by development partners and religious and traditional rulers from within and outside Sokoto, Tambuwal said the his administration embarked on the project as the area had remained the only one out of the 23 local governments of the state without a Senior Secondary School.
"The school will be a co-educational one, both for boys and girls. We have decided to make it a unity school and will attract students from all parts of Nigeria and neighbouring Niger republic. Students of the school would be taught in both English and French," Tambuwal said.
According to him, the contractor had since been paid the required thirty per cent as mobilisation fee.
He said the project would be completed in the next four months, while the work commenced about two months ago.
The governor also promised to make funds available for the completion of the project on schedule, and according to specifications.
"Education is key to success both in this world and in the hereafter. The school is aimed at improving enrolment, retention and completion of students across the state. It is also aimed at improving equal access to education for both boys and girls in the state.
"As the adage goes, when you educate a girl, you educate the society but when you educate a boy, you educate only an individual," he added.
Tambuwal called on the contracting firm to complete the work on schedule, warning that compromise by supervising engineers would not be condoned.
Speaking at the occasion, Sultan of Sokoto, Muhammad Sa'ad Abubakar, commended the state government for embarking on the project.
He stressed the need for all children to have equal opportunities to education.
While describing illiteracy as a "disease" which forces people to follow others blindly, Abubakar decried street begging by some children, saying such obnoxious act was unIslamic.
The Sultan urged wealthy individuals to provide scholarship to the children of less privileged.
State Commissioner of Basic and Secondary Education, Dr. Jabbi Kilgori, said the project consists of 12 classrooms, laboratories, library, hostels, staff quarters and clinics, among others

Ba na tsoron duk wani bincike Inji Sarki Sanusi II

JBayan kiran da Babban Lauyan nan watau Femi Falana yayi da a binciki Tsohon babban bankin Kasar nan, Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, Sarkin ya fito ya bayyana cewa, ba ya tsoron hakan ko kadan, kuma a shirye yake da a nema shi ya amsa tamboyi. Femi Falana SAN ya kira Gwamnati da ta binciki Sarki Sanusi da kuma Charles Soludo game da wasu kudi da ake zargin su karkatar lokacin suna Gwamnan babban Bakin Najeriyar.
Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya bayyanawa Jaridar Premium Times cewa a shirye yake da a bincike sa, idan bukata ta tashi, zai mika kan sa ga Hukumomin da ke yaki da cin hanci da rashawa da sauran laifuffuka a Kasar. Sarki Sanusi II ya bayyana cewa a lokacin da yake Gwamnan bankin Najeriya watau CBN, bai taba biyan ‘yan kasuwa kudi da sunan tallafin man fetur ba. Sarki Sanusi II yace hakan bai kuwa taba faruwa ba tare da izinin Gwamnati ba. Gwamnan ya kuma bayyana yadda yayi fada da tallafin man fetur din aka ce ana biyan ‘Yan Kasuwa a wannan lokaci saboda rashin gaskiyar da ta dabaibaye tsarin.
Sarki Sanusi II yace zargin da ake yi, na kwato bankunan Kasar nan da aka yi a lokacin ya ba sa mamaki. Sarki Sanusi yace a lokacin da yake Gwamna sun kwato bankuna ne daga rugujewa, ba kuma ta hanyar mikawa Bankunan kudi ba, sai dai don ka da kudin mutane da ke bankin ya salwanta. Abin da ya faru kuwa shine masu bankunan sun barnatar da kudin Jama’a ko kuma sun bada wawan bashi. Hakan ta sa Bankin na CBN ya dauki wannan mataki, kuma aka kawo AMCON domin bankunan su biya duk kudin da aka ara masu.
Gwamnan bankin Kasar na yanzu, Godwin Emefiele yace laifin Gwamnonin da aka yi a baya ne Kasar ke fama da karancin kudin dala ta Kasar waje

Yadda zaka sanya kati a wayar ka daga account banks (All banks)

To recharge your phone from your bank account. (All banks)
1.Access bank:*901* amount#
Misali *901*1000#
2.Eco Bank*326*amount#
Misali *326*500#
3.Fidelity:*770*amount#
Misali *770*2000#
4.FCMB:*389*214*amount#
Misali *389*214*500#
5.First Bank:*894*amount#
Misali*894*1000#
6.GTB:*737*amount#
Misali *737*1500#
7.Heritage bank:*322*030*amount#
Misali *322*030*1000#
8.keystone:*322*082*amount#
Misali *322*082*1000#
9.Skye bank:*833*amount#
Misali *833*1000#
10.Stanbic IBTC: *909*amount#
Misali *909*1500#
11.Sterling:*822*amount#
*822*1000#
12.UBA:*389*033*1*amount#
Misali *389*033*1*1000#
13.Unity bank:*322*215*amount#
Misali *322*215*1000#
14.Zenith:*966*amount# or *302*amnt#
*966*1000# or *302*1000#
masu amfani da mtn
15.Diamond bank(yellow acct. only):*710*555*
phone no*amount*pin#
To know your BVN, dial *565*0#

MANOMI ZAI IYA SAYAR DA HATSINSA KAFIN YA GIRBE ?

MANOMI ZAI IYA SAYAR DA HATSINSA KAFIN YA GIRBE ? Tambaya: Assalamu Alaikum. Mutum ne yake bada kudin Gero ga manoma tun kafin ma amfanin ya girma. Misali, in ana saida Gero a lokacin shifka #450, to sai suyi lissafi akan tsammanin Geron zai sauko zuwa #150. Kaga duk #450 daya ba manomi, zai kawo mai Tiya 3 ta Gero kenan. Menene halaccin wannan ciniki ? Amsa: Wa alaikum assalam, Ya halatta mutukar sun cimma daidaito akan hakan, wannan shi ake kira Salam a wajan malaman Fiqhu(Kan ta gasu), Annabi (s.a.w) da ya zo Madina ya samu mutanen garin suna wannan cunikayyar, sai ya ce musu: (Duk Wanda zai yi, to ya yi a cikin Ma'auni sananne, zuwa lokaci sananne) . Allah ya halatta wannan nau'i na cinikayya saboda saukakawa mutane, Manomi zai iya bukatar kudi kafin amfaninsa ya zo. Allah ne mafi sani. Amsawa: Dr jamilu zarewa.

Saturday 24 September 2016

(mp3)Fatawoyinrahama weekly programme daga Dr.sani umar muhd r/lemo

Assalamu alaikum yan uwana musulmi barka mu da wanannan tambayoyin rahama wanda sheikh Dr.sani umar muhammad r/lemo kano domin sauraron wannan fatawoyinrahama kayi download sai ka dana inda nan inda blue rubutu yake
Weekly fatawoyinrahama da ya gabata
Ayi sauraro lafiya

FATAWAR RABON GADO (56)|Dr.Jamilu yusuf zarewa

FATAWAR RABON GADO (56)
Assalamu alaykum.
Malam inada tambaya? Allah gafarta malam, shin idan mace ta rasu batada miji da iyaye sai '' ya'ya uku mata batada namiji, shin '' yan uwanta da suke uba daya sunada gadonta?
Amsa :
Wa alaikum assalam, Za'a raba abin da ta bari kashi uku, sai a bawa 'ya'yanta kashi biyu, ragowar kashi dayan sai a bawa 'yan'uwanta da suka hada uba daya in har babu shakikai.
Allah ne mafi sani
Dr Jamilu Zarewa
19/Dhul-Hijjah /1437
21/09/2016

Friday 23 September 2016

(Mp3) sabuwar wakar Rararah Kutara ĸυтaraн burgu ya gudu

Sabuwar wakar rararah mai taken kutare burgu ya gudu
doмιn download ѕнιga nan вυrgυ
Ayi sauraro lapia

(mp3)sabuwar wakar rarara & вaввan cнιnedυ mai taken yan nigeria muyi hakuri

Sabuwar wakar Rararah shi da babban chinedu mai taken yan nijeriya muyi hakuri ,ma'ana yana baiwa talaka sharawa ѕυ  yayi hakuri duk cin gyara ne domin downloading din wanannan Waka
laтѕa вlυe rυвυтυn nan download мp3 

 ayι ѕaυraro laғιya

Yadda zaka sanya font style batare da kayi rebooting ba ,kuma wanda ka turawa sako ta message ko chat hakan zai ga style a wayar ka ta android

Yadda zaka sanya font style a wayar ka batare da kayi reboot dinta ba kuma haka wanda ka turawa mutum sako da wanannan font style
Nasan mutane da dama suna ganin idan wani yayi masu text a whatsapp or facebook suna posting or comment kana ganin style kamar irin wanannan nawa wada duk wanda yake da whatsapp dina or facebook yana ganin rubutuna ya chanza
To wanannan abune mai sauki shine kawae ka samu application mai suna "fancykey indic"
To sai kaje  a #playstore kayi search da wanannan suna fancykey indic
Bayan kayi installing idan kayi sucessfull installing

Zai nuna maka hakan sai kayi latsa inda anka rubuta fancy indic ka ka mayar da shi blue kamar yadda na Tochpal yake
Bayan kayi haka sai kayi enable dinsa sa'a nan kuma kayi click a Got it
Ko kuma ka dawo wajen typing zaka wani abu kamar haka wanda na zagaye sai latsa shi
Sai ka zabi wanda na zagaye
Bayan ka yi hakan sai kayi click akan 
  #F
Kamar yadda na zagaye
Za'a nuna maka  font,themes,setting
Sai ka shga font ka zabi kalar da kake so
Kamar ni na zabi wanannan da na zagaye shi nake so
Themes :shi kuma ka zabi kalar wanda kake so

Setting:sai kayi untick na soud, auto correction,auto captilazation
Shikenan Allah ya bada sa'a
Domin abinda baka gane zaka iya ajiye comment dinka ko ka tuntubeni ta wanannan lambar waya
09032038203

Hukumar DSS sun kama ‘Osinbajo’ saboda zamba

An kama wani mutumi dake kwaikwayon Osinbajo a Facebook
– An gurfanar da wni mutumi mai shekaru 44, Eseosasere Gift Osifo, a gaban wani babban kotun Osogbo kan zargin kwaikwayon mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo
– Mai shari’ar yace wanda ake zargi ya aikata laifin ne a tsakanin watan Janairu da watan Augusta kafin a kama shi a gurfanar da shi a gaban kotu
Abangaren sa, wanda ake zargi ya karyata laifuka duda biyu da kotu ke tuhumarsa a kai na kwaikwayo da zamba

Hukumar DSS sun zargi wani mutumi mai shekaru 44, Eseosasere Gift Osifo da bude shafin Facebook inda yake amfani da bayanan mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo yana rudar wadanda basu sani ba
Hukumar Department of State Services (DSS) sun kama wani mutumi mai shekaru 44 a duniya, Eseosasere Gift Osifo, kan zargin satar fasaha da zamba.
Jaridar Nation ta bada rahotanni cewa an gurfanar da wanda ake zrgi a gaban wani babban kotun Osogbo a jiya, Alhamis 22 ga watan Satumba, kan laifin bude shafin Facebook da bayanan mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo yana rudar wadanda basu saní вα
A cewar mai hukunci, Mr Onoche Ekwom, babban jami’in doka na hukumar DSS, wanda ake zargin ya aikata laifin ne a tsakanin watan Janairu da watan Augusta kafin a kama shi a gurfanar dashi a gaban kotu.
Ekwon ya fada ma kotu cewa wanda ake zargin yayi amfani da shafin gurin damfarar kudi daga mutanen da basu sani ba a lokuta da dama kafin ya fada a karkon mutun na karshe wanda ya kai ga kama shi.
Mai shari’ar ya ce laifin yayi karo da sashi na 484 da 422 na dokar jihar Osun ta shekara 2002.
A bangarensa, wanda ake zargin ya karyata laifuka guda biyu na satar fasaha da zamba da ake zargin sa a kai.

duвα Wani matashi dan Kaduna ya kirkiro manhaja da za ta ceci rai(hσtunα)

Wani matashi mai hidimar Kasa (Watau NYSC) a Garin Minna, ta Jihar Niger mai suna Musa Bello ya kirkiro wata manhaja da ta za ta sa a rage matsalar da ake samu idan an yi hadarin mota. Musa yayi karatu ne a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya.
Wannan manhaja ta wayar zamani tana dauke da lambobin ‘yan kwana-kwana da masu bada agaji domin ceton rai yayin da aka samu hadari ko a ina ne a kasar nan.
Wannan manhaja tana dauke da irin wadannan lambobi na neman dauki na Jihohin Kasar nan da dama, sai dai kawai mutum ya zabi Jihar da yake, kana ya nemi lambar da ya ke nema ya latsa
.
Akwai lambobin NEMA; Hukumar da ke bada agaji ta Kasa, akwai kuma lambar neman agajin gaggawa ta Kasar, haka dai kuma akwai lambar ‘Yan kwana-kwana domin hadarin gobara.
Ba nan kadai, ya zama da wannan manhaja mutum na iya aika sako na SMS zuwa wadannan lambobi irin na su Jami’an ‘yan Sanda, da NYSC ta kasa, dsr. Nan gaba ma dai wannan ta’ailiki yace zai kara da lambobi irin na su Hukumar KASTELEA da wasun su.
Wannan manhaja da wannan b nσawan Allah mai suna Musa Bello ya kirkiro zai dauki lambobin kanukawa da sauran masu gyaran motoci a Kasar nan, ko don nan gaba kana tafiya tayar ka ta sace.

Abin dai gwanin sha’awa, duk mai bukatar wannan Manhaj, sai ya garzaya Google Store don ya sauke, kuma kyauta ne ba sai an biya ko taro ba. Idan kuma akwai wasu shawarwari da za a iya badawa, sai a tuntube Malam Musa Bello.