NewsHausa: News NewsHausa: News

Pages

LATEST POSTS
Showing posts with label News. Show all posts
Showing posts with label News. Show all posts

Sunday, 24 June 2018

Kasar Lebanon ta dauke 'yan mata sanye da gajerun wanduna aikin 'yansanda dan jan hakalin turawa

Kasar Lebanon ta dauke 'yan mata sanye da gajerun wanduna aikin 'yansanda dan jan hakalin turawa

Kasar Lebanon ta fara baiwa 'yan sanda 'yan mata gajerun wanduna dan su rika jawo hankulan turawa masu yawon bude ido kasar, magajin garin Baroummana inda abin ya faru me suna pierre Achkar ya bayyan cewa wanan tsari da suka fito dashi sunyi ne dan canja tunanin kasashen yamma akan kasar.

Lamarin dai ya Jawo cece-kuce tsakanin 'yan kasar amma wasu na ganin cewa hakan ba komai bane.

Wani dan kasuwa da kafar watsa labarai ta Reuters tayi hira dashi yace yana da shago a bakin kasuwa kuma 'yan matan 'yansandan na tsayuwa a bakin shagon nashi suna aiki, shi bega aibun wannan abinba, ya kara da cewa duka matan sun san abinda suke, sun kuma kammala jami'a dan haka ba zasu yarda su yi abinda be dace ba.

Itama wata ma'ikaciyar 'yarsandan da aka yi hira da ita tace ba a tilasta mata yin aikin ba da kanta ta nema kuma tana jin dadin aikin.

Wednesday, 11 April 2018

Kyan da ya gaji uban sa: Dan Ronaldo ya kwaikwayeshi

auraron dan kwallo, Cristiano Ronaldo kenan a wadannan hotunan yake kokarin kwaikwayar irin abinda mahaifinshi yayi na cin kayatacciyar kwallo, Ronaldo dai yaci Juventus kwallo wadda ta dauki hankulan Duniya. To ga dukkan alamu danshi zai gajeshi.

A jiya, Lahadine gurin atisaye dan Ronaldon yayi wannan bajinta, kamar yanda Daily Mail ta kasar Ingila ta ruwaito.

Saturday, 7 April 2018

Kalli Mutum ya hadiye burushin da yake wanke baki da shi

Likitoci a kasar Kenya sun yi nasarar cire burushin wanke baki daga cikin wani mutum bayan da ya hadiye shi.

David Charo ya ce ya hadiye burushin ne bisa kuskure ranar Lahadi, lokacin da yake wanke bakinsa.

Ya shafe kwana biyar yana yawo tsakanin asibitocin yankin a kokarin da yake ne neman magani.

ibitocin sun ki karbarsa suna masu cewa ba su da kwarewar da za su iya yi masa tiyata.

Bayan da abin ya ci tura ne aka mika shi ga Dokta Ramadhan Omar a wani asibiti mai zaman kansa, wanda ya yi nasarar yi mata tiyata.

Hoton wurin da aka dauka ya nuna yadda burushin ya makale a cikin Mista Charo.

Jama'a da dama sun nuna dimuwa kan labarin a shafukan sada zumunta.

Rahatanni sun ce a yanzu Mista Charo na ci gaba da murmurewa a asibitin da ke birnin Mombasa.

Wadansu bayanai sun nuna cewa ya shafe shekara 20 yana amfani da shi.
© bbchausa.

Kalli yanda aka yiwa wani mamaci makara me siffar Zaki

Kalli yanda aka yiwa wani mamaci makara me siffar Zaki

Wani attajirin mutum ne da ya mutu a jihar Enugu dake kudancin Najeriya aka mai makara me siffar Zaki dan binneshi da ita, lamarin dai ya dauki hankulan mutane sosai inda da dama suka bayyana hakan da almubazzaranci.

Hadiza Gabon na son yin abota da wannan kyakkyawar budurwar, gurguwa

Wannan wata kyakyawar baiwar Allah ce gurguwa da tauraruwar fina-finan Hausa, Hadiza Gabon tace tana son yin abuta da ita, bayan saka hoton wannan baiwar Allahn a dandalinta na sada zumunta da muhawara, mutane sunyi ta yabawa da kyawun da Allah ya mata..

Kuma itama ta cewa Hadizar tuntuni dama ita abokiyartace saidai yanzu abutar tasu zata yi karfi su shaku.
Muna musu fatan Alheri

Kalli yanda wani Ango ya bayar da Amaryarshi

Kalli yanda wani Ango ya bayar da Amaryarshi

Wannan hoton wani Angone da Amaryarshi a gurin bikinsu da Angon ya zage yana cin abinci da hannu, irin yanayin fuskar Amaryar da alama bataji dadin abinda ya faru ba, irin ya bayar da ita dinnan.

Hoton ya dauki hankula.

Saidai ko a gaskene kokuwa shirin fim ne shine be bayyana ba amma ya kayatar.

Salman Khan zai yi shekara 5 a gidan yari saboda kashe dabbar daji da yayi shekaru 20 da suka gabata

Salman Khan zai yi shekara 5 a gidan yari saboda kashe dabbar daji da yayi shekaru 20 da suka gabata: Ya zubar da hawayen nadama

Wata kotu a kasar India ta yankewa jarumin fina-finan Bollywood Salman Khan, hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekara biyar saboda ya yi farautar gwanki da ba kasafai ake samunta ba ba bisa ka'ida ba.

Kotun, wadda ke zamanta a Jodhpur, ta kuma ci tarar jarumin rupee 10,000 kwatankwacin dala 154. Salman Khan dai ya kashe wasu nau'in gwanki da ake kira blackbucks guda biyu a yammacin jihar Rajasthan a yayin da ake daukar fim din Hum Saath Saath Hain a shekarar 1998.

Kotun dai ta wanke sauran jaruman da suka fito a fim din tare su hudu.

Jarumin mai shekara 52, zai iya daukaka kara a kan hukuncin da kotun ta yanke masa.

Rahotanni sun ce dole ne Salman Khan ya zauna a gidan yari na wasu kwanaki.

Wannan ne dai karo na hudu da ake shigar da karar jarumin a kan farautar dabbobi a lokacin da ake daukar fim dinsa na Hum Saath Saath Hain a shekarar 1998.

An wanke shi a kararraki ukun da aka shigar a baya.

A shekarar 2006, wata kotu ta tuhumi jarumin da laifuka biyu na farauta, inda aka yanke masa hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekara biyar.

To amma da shekara ta zagayo, wata babbar kotu a Rajasthan, sai ta yi watsi da hukuncin.

Ainahin shari'ar dai al'ummar yankin Bishnoi ne wadanda suke bauta wa dabbar da ya yi farautar ne suka shigar da ita.
Gwamnatin kasar dai ta daukaka kara a kan wanke jarumin a kotun koli.

An dai tuhumi jarumin da wasu mutum bakwai da kisan dabbobin daji da suka hada da gwanki a arewacin jihar Rajasthan.

Ya matsayin Salman Khan ya ke a India?
Salman Khan, na daya daga cikin jaruman Bollywood da suka yi fice, da kuma farin jini a wajen jama'a, ba ma a kasar kadai ba, har ma da wasu kasashen duniya.

Jarumin ya fito a fina-finai fiye da 100.
An fi sanin jarumin da fina-finan soyayya da ma na fada.

Ya kuma samu lambobin yabo da dama.
Sama da mutum miliyan 36 ne suke binsa a shafinsa na Facebook, inda ya ke da mutum miliyan 32.5 a shafinsa na Twitter.

Tausayin da aka ce ya ke da shi ga jama'a musamman tsofaffi da marayu, ya kara masa farin jini musamman a wajen

talakawa.
bbchausa.

Wasu kafafen watsa labarai na kasar Indiya sun ruwaito cewa Salman Khan ya zubar da hawayen takaici da nadama bayan da kotu ta bayyana hukuncin dauri da tara a gareshi.

Haka wasu mata biyu 'yan uwanshi dake cikin kotun suma sun rushe da kuka dan taya dan uwan nasu alhini.

Lauyanshi dai ya daukaka kara zuwa yanzu

Kalli inda ruwa kala biyu suka hadu a wani bangaren Najeriya

Kalli inda ruwa kala biyu suka hadu a wani bangaren Najeriya

Wannan wani kayataccen hotone inda ruwa kala biyu suka hadu, hoton yayi kyau.
Punch.

Kalli yanda wani limamin addinin gargajiya ke sawa jarirai Albarka a kasar Indiya

Kalli yanda wani limamin addinin gargajiya ke sawa jarirai Albarka a kasar Indiya

Wannan hoton ya nuna irin yanda wani limamin addinin gargajiya yake sakawa jarirai Albarka kenan ta hanyar takasa su da kafarshi a wani yanki na kasar Indiya kamar yanda kafar Aljazeera ta ruwaito, lallai Allah daya gari ban-ban.

An Bayarda Belin Salman Khan

Wata kotu a kasar India ta bayar da belin jarumin fina-finan Bollywood Salman Khan, wanda ta yanke wa hukuncin daurin shekara biyar a gidan yari.

 Ranar Alhamis Din Da Ta Gabata ne kotun ta yanke wa jarumin hukuncin bisa samunsa da laifin yin farautar gwankin da ba kasafai ake samunsa ba, ba bisa ka'ida ba.

Kotun, wadda ke zamanta a Jodhpur, ta kuma ci tarar jarumin rupee 10,000 kwatankwacin dala 154.

Salman Khan dai ya kashe wasu nau'in gwanki da ake kira blackbucks guda biyu a yammacin jihar Rajasthan a yayin da ake daukar fim din Hum Saath Saath Hain a shekarar 1998.

Kotun dai ta wanke sauran jaruman da suka fito a fim din tare su hudu.

Tun da fari dai, lauyan jarumin mai shekara 52, ya gabatar wa kotun hanzarin mutumin da yake Wakilta A cewarsa, daurin shekara biyar zai haifar da koma-baya a sana'arsa ta fim.

Rahotanni sun ce dole ne Salman Khan ya zauna a gidan yari na wasu kwanaki.

An Yanke Wa Jarumin Bollywood Salman Khan Hukunci Shekara Biyar A Gidan Yari

Al-Mustapha Ya Bayyana Yanda Anka Kashe sani Abacha

Al-Mustapha Ya Bayyana Yanda Anka Kashe sani Abacha

Ya ce tun ranar wata lahadi bakwai ga wata shida na shekarar alib dubu daya da Dari Tara da casa'in da takwas (7-6-1998) lokacin da Tsohon Shugaban kasa Sani Abacha ya gaisa da wani daga cikin masu tsaron shugaban kasar Palestine Yaseer Arafat a filin sauka da tashi na jirgin sama dake babban birnin tarayya Abuja hada hannun su keda wuya shikenan yanayin tsohon shugaban kasar ya canja
Tsohon mai tsaron lafiyar,

 tsohon shugaban mulkin soja a Najeriya Janar Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha yayi karin haske akan yadda shugaban nasa ya rasa ran shi. Hamza Al-Mustapha ya karyata zacen da ake na cewar wai Abacha Tufa (Apple) yaci ya mutu.

Ya ce tun ranar wata lahadi bakwai ga wata shida na shekarar alib dubu daya da Dari Tara da casa'in da takwas (7-6-1998) lokacin da Tsohon Shugaban kasa Sani Abacha ya gaisa da wani daga cikin masu tsaron shugaban kasar Palestine Yaseer Arafat a filin sauka da tashi na jirgin sama dake babban birnin tarayya Abuja hada hannun su keda wuya shikenan yanayin tsohon shugaban kasar ya canja.

Da gari ya waye likitan da yake duba shi yazo yayi mishi Allura ya kuma bashi shawara akan ya samu ya kwanta ya dan huta, da misalin karfe 9 na dare baki suka fara shigowa wurin shugaban, wanda ya shigo daga karshe shine Janar Jeremiah Timbunt Usteni wanda a lokacin shine ministan Abuja, sunyi ta hira dashi har zuwa karfe 3:35 na dare.

Da misalin karfe biyar 5 na Asuba sai daya daga cikin masu tsaron gidan shugaban kasar ya rugo a guje gidana yace maigida yana cikin wani hali mai ban tsoro saboda haka in zo ana bukatar gani na cikin gaggawa,

 a wannan lokacin sai nayi tunanin ko dai ana so ayi mana juyin mulki ne? Sai nace wa matata taje ta dauke wa Sojan hankali tace ya jira ni, ni kuma sai nabi ta kofar baya na je inda shugaban kasar yake; ina zuwa sai na tarar dashi yana Huci, numfashin sa na fita sama-sama,

 a lokacin bazai yiwu in taba shi ba kamar yadda tsarin dokar aikin mu yake. Banyi kasa a gwiwa ba sai naja da baya na kame na kwala mishi kira da karfi da nufin ya bani dama in taba shi, sau biyu ina yin haka amma baice dani komai ba.

Daga wannan lokacin sai na gane akwai babbar matsala sosai nan da nan na kira babban likitan shi Dakta Wali ya bayyana a cikin mintuna da basu wuce 8 ba, take ya yiwa maigida Allurori guda biyu daya a kirji shi daya kuma a kusa da wuya shi; ba a jima ba Likitan ya bayyana mini cewar gaskiya sai dai muyi hakuri domin maigida ya riga mu gidan gaskiya.

Daga wannan lokacin na umarci Dakta Wali ya jirani naje gidana don shirya wa dukkan matsala da zan iya fuskanta saboda mutuwar maigidan. Saboda haka a zance na gaskiya babu wata magana dake nuna cewar Tsohon Shugaban Kasa Sani Abacha guba yaci a Apple ya mutu; inji Manjo Hamza Al-Mustapha.
Sources :naij.com

Friday, 6 April 2018

An Yanke Wa Jarumin Bollywood Salman Khan Hukunci Shekara Biyar A Gidan Yari

An Yanke Wa Jarumin Bollywood Salman Khan Hukunci Shekara Biyar A Gidan Yari

Wata Kotu a Kasar Indiya ta yankewa shahararen jarumin finan-finan Indiya Salman Khan hukuncin zaman shekaru biyar a gidan yari saboda laifin kashe wasu dabobi wadanda basu da yawa a duniya a wata farauta da yayi.

Lauya mai shigar da kara, Mahipal Bishnoi ya shaidawa manema labarai a birnin Rajasthan da ke Jodhpur cewa: "Kotu ta yanke ma Salman Khan hukuncin shekaru biyar a gidan yari da kuma tarar rupees 10,000 ($150)."

Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, Lauyan ya cigaba da cewa a yanzu ana shirye-shiryen kama jarumin mai shekaru 52 a duniya don tisa keyar sa zuwa gidan yari na garin Jodhpur.

Sai dai Salman Khan ya musanta aikata laifin da ake tuhumar sa dashi kuma yana da damar daukaka kara a wata kotun.

'Yan'yan Rabi'u Rikadawa sunyi saukar Qur'ani

A yaune 'Ya'yan tauraron fina-finan Hausa, Rabi'u Rikadawa, Fatima da Al-Amin sukayi saukar karatun Qur'ani a makarantar Isilamiyarsu, Mahaifin nasu ya saka hotunan 'ya'yan nashi yana tayasu murna.

Muna musu fatan Allah yasa karatun nasu ya amfanesu da sauran Al'umma baki daya.

Kannywood: Shararriyar jaruma Maryam Booth ta rabawa marayu kayan sallah

  Image © Mujallarmu.Com

Jaruma Maryam Booth tayi rabon kayan sallah ga marayu kananun yara maza da mata a Nasarawa dake kano,jarumar ta raba shaddoji da yadika masu din ki da ado na zamani.

Dandalin Arewafresh.com ta samu labarin cewa awajen rabon ne wakiliyar majiyar mu Maryam Hotoro ta sami sukunin

 zantawa da jarumar kamar haka:
Maryam kin rabawa marayu kayan sawa, kuma da alamu wadan nan yara marayune, wanne hange ki kayi wanda yasa ki ka rabawa marayu kayan sallah amadadin ki ba masu iyaye? Wannan

 tambaya tana da saukin amsawa.
Domin amsarta yana cikin tambayarki. Duk yaron yake da iyaye to tabbas yana da tabbacin samin kayan sallah, amma maraya bashi da tabbas.

Dan haka naga gwara in ba marayu zaifi kyautuwa.

Me za kice da yan uwanki jarumai akan irin wannan abin alkairi da ki ki gudanar a yau? Abinda zance shine, su ma Allah ya basu ikon gudanar da wannan abin alkairi.

Duk da yake da yawan jarumai maza da mata suna irin wannan abin alkairin, nima da wasu nayi koyi irinsu A Zango, Sani Danja, Ali Nuhu.

Mawaki Alan Waka Yakai Abokinsa Da Mutanen Gidan Su Makka

Mawaki Alan Waka Yakai Abokinsa Da Mutanen Gidan Su Makka

Shahararren Mawaki Alan Waka Tare Mahaifiyarsa Da Kuma Kannuwarsa Da Kuma Aminin Abokin Sa Acikin Jirgin Sama Zasu Je Umrah

Diyar Mawaki Mamman Shata Zata Fito Takarar Yar Majilisar Katsina

Daya daga cikin yaran marigayi Alhaji Mamman Shata, fitaccen mawaki kuma wanda ya raya kasar hausa da wakoki wato Hajiya Halima Mamman Shata ta bayyana anniyarta na fitowa takarar majalisar dokoki na jihar Katsina.

Hirar ta da jaridar RARIYA Hajiya Halima tana mai cewa ta gaji mahaifin ta a bangaren siyasa don haka zata daukaka wanan gado na fitowa takara domin wakiltar yankin Funtua a zaben 2019 dake nan tafe.

Ta bada dalilan daya sa zata fito takara kamar haka; "Na fito domin in bada guddumuwa ga cigaba karamar Hukumar Funtua da kawo kudurorin da za su kawo cigaban Matan da inganta rayuwar su a jihar Katsina da kasa baki daya.

"Mata suna da rawar da za su taka, a harkar siyasa amma mun yi barci an bar mu a baya musamman a arewacin Nijeriya, kalilan ne ke fitowa takara, saboda wadansu dalilai.

Kuma mu mata mune muka fi fitowa a ranar zabe, kuma kullum mune ake bari a baya. Idan Allah ya bani nasara zan tabbatar da an yi dokoki da za ta inganta rayuwar matan jihar Katsina da kuma karfafa rayuwar su".

Halima Shata ta kara da cewa "koda yaushe ina kara samun kwarin gwiwa a harkar siyasa saboda mahaifinmu dan siyasa ne, Amma ni na taso naga yana harkokin siyasa wadda har ya taba zama shugaban jam'iyyar da kuma takarar shugabanci kasar nan kuma cikin yayansa ina alfahari da na gaje shi bangaren siyasa, kuma zan cigaba da jajircewa domin ita ce matakin nasara.

Daga karshen yar gidan shaharen mawakin tayi ma Gwamna Aminu Bello Masari godiya bisa kokarin yake na bude kofofi ga mata don fitowa a dama dasu a harkar siyasa.

Daga: Pulse Nigeria

An Yanke Wa Jarumin Bollywood Salman Khan Hukunci Shekara Biyar A Gidan Yari

An Yanke Wa Jarumin Bollywood Salman Khan Hukunci Shekara Biyar A Gidan Yari

Wata Kotu a Kasar Indiya ta yankewa shahararen jarumin finan-finan Indiya Salman Khan hukuncin zaman shekaru biyar a gidan yari saboda laifin kashe wasu dabobi wadanda basu da yawa a duniya a wata farauta da yayi.

Lauya mai shigar da kara, Mahipal Bishnoi ya shaidawa manema labarai a birnin Rajasthan da ke Jodhpur cewa: "Kotu ta yanke ma Salman Khan hukuncin shekaru biyar a gidan yari da kuma tarar rupees 10,000 ($150)."

Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, Lauyan ya cigaba da cewa a yanzu ana shirye-shiryen kama jarumin mai shekaru 52 a duniya don tisa keyar sa zuwa gidan yari na garin Jodhpur.

Sai dai Salman Khan ya musanta aikata laifin da ake tuhumar sa dashi kuma yana da damar daukaka kara a wata kotun.

An Bayarda Belin Salman Khan

Kasar China ta hana sayar da baibul

Kasar China ta haramta sayar da littafin bibul a shafukan yanar gizo, kasar ta bayar da wannan umarnine a wani shiri da take na dakile ayyukan addinan Musulunci da na Kiristanci inda tafi baiwa addinan Buddah dana gargajiya muhimmanci dan daukaka al-adun kasar.

Shafin the Australian ya ruwaito cewa neman littafin baibul na sayarwa a shafukan yanar gizo na sayar da litattafai beyi nasara ba bayan da aka kafa dokar, yayin da idan mutum ya nemi ya siya baibul din sai dai yaga wayam, babu komi.

Amma mutum zai iya samun baibul din a coci-coci da suran guraren Ibada.

'Ko wuta shugaba Buhari yace in fada zan fada' || Gwamna Yahaya Bello

Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi ya bayyana cewa shi masoyin shugaban kasa Muhammadu Buharine na gani na fada kuma yana mishi biyayya sosai ta yanda koda zai umarceshi ya fada wuta babu wata-wata zai mishi biyayya.

Gwamna Bello ya bayyana hakane da yake bayar da amsa akan goyon bayan shugaba Buhari akan kin amincewa da karawa shuwagabannin jam'iyyar APC wa'adi inda ya bukaci a yi zabe dan samar da sabbin shuwagabannin.

Da yake amsa tambaya akan dalilin da yasa a farko ya goyi bayan a baiwa shuwagabannin APC din karin lokaci,

Gwamna Bello ya bayyana cewa yanzu ya goyi bayan a yi zabe kuma masu cewa yana da wata matsala da Tinubu ne shiyasa tun a farko ya goyi bayan karawa shuwagabannin APC wa'adi, ba gaskiya bane.

Tinubu shugaban shine shi kuwa shugaba Buhari shugaban kowane.
Dailypost.