NewsHausa: Addini NewsHausa: Addini

Pages

LATEST POSTS
Showing posts with label Addini. Show all posts
Showing posts with label Addini. Show all posts

Sunday, 8 April 2018

KOYAR DA KIMIYAR AURE Abubuwan Da ZAMZAM ISLAMIC COLLEGE Zata Koyar Guda (41) - Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa



Wannan makaranta ta ZAMZAM ISLAMIC COLLEGE ta shirya tsaf domin koyar da kimiyar zamantakewar aure, ga bangarori guda uku na maza mata
Zawarawa maza da mata 
Samari da Yammata
Mazan aure da matan su. 
Domin kara inganta rayuwa ta maaurata wadannan kwasa kwashe sun hada
1- Manufar yin aure
2 Hikimar yin aure
3 Falalar yin Aure
4-Hukuncin yin aure
5 - Yadda ake neman aure
6 - Irin matar da ake so a aura
7- Irin mijin da ake so a aura
8- Yadda ake zuwa zance da yadda ake yi
9_ Yadda ake bincike kafin aure da abubuwan ake bincikawa guda biyar
10- Mata guda 42 da suka haramta mutum ya aure su saboda nasaba ko shan nono ko surukuta.
11 Rukunan Daurin aure.
12 - Sadaki da hukunce hukuncin sa
13 Wanene Waliyyi da sharuddan zama Waliyyi da kashe kashen waliyyai na aure
14 Sigar daurin aure da yadda ake yin ta.
15 - Shedun aure da siffofinsu.
16- Sanya sharudda a cikin aure.
17 - Yadda ake bukukuwan aure a musulunci, da aladun da suka shigo cikin aure marasa kyau. 
18- Yadda ake walima da shagalin aure.
19- Ladubban tarewar amarya da Ango.
20 Hakkokin mata akan miji
21 Hakkokin miji akan mata.
22 Ladubban kwanciyar aure
23 Abubuwan da suke kara soyayya tsakanin maaurata.
24 Yadda ake gyara matsalolin aure idan sun taso.kafin akai ga saki 
25 Abubuwan da suke kawo albarka a gidan aure
26 Abubuwan da suka halatta, da wadanda suka haramta tsakanin maaurata a lokacin da mace take al'ada
27 Abubuwan da suke kawo mutuwar aure
28 Hukuncin hana daukar ciki, ko zubar da ciki, da Tsarin iyali a musulunci.
29 Sharuddan da mutum, zai cika kafin ya kara aure.
30 Wanda ya kasa daukan nauyin iyalinsa. 
31 Hukuncin wanda ya kauracewa iyalinsa. bisa zalunci ko larura ko horo. da sanin lokacin da shari'a ta iyakan ce. 

32 Mutuwar aure, da hukunce hukuncan sa,
33 Hakkokin matar da aka saka, 
34 Wa yake da hakkin rike yaya bayan mutuwar aure? 
35 - Yadda ake kul'i (mace ta nemi rabuwa) da abubuwan da suke jawo shi. 
36- Hukuncin komai bayan saki. 
37- Idda da hukuncin ta a musulunci 
38 - Hukuncin Ila'i Rashin kusantar iyali da rantsuwa ko saka sharadi. 
39-  Hukuncin Zihari kamanta jikin mahaifiyar sa da matarsa. Ko sauran mahramansa. 
40 Hukuncin lia'ni idan mutum yana zargin matarsa da zina. 
Reno da tarbiyya tun daga daukar ciki har zuwa haihuwa da yaye, 
Hakkokin yaya akan iyaye da hakkokin iyaye akan yaya. 
41 Yadda ake Takaba idan. Miji ya mutu.

Thursday, 5 April 2018

TUNATARWA Tambayoyi Hudu Da Dan Aljanna Kadai Ya San Amsarsu Daga Sheikh Isa Ali Pantami



Annabi (SAW) Ya ce idan mutum ya mutu, Mala’iku biyu za su zo masa sannan su masa tambayoyi hudu a ‘Kabarinsa. Wadannan tambayoyi sune:

1) Waye Mahaliccinka?
Amsa: ALLAH.

2) Menene addininka?
Amsa: Addini na shine Musulunci

3) Me zaka ce akan wannan da
aka aiko muku?
Amsa: Muhammad, Manzon Allah

4) Menene ilminka?
Amsa: Na karanta littafin Allah,
kuma na yi imani da shi.

Annabi (SAW) Yace duk wanda ya
amsa ko ta amsa tambayoyin nan
dai dai a ‘Kabari, za a rubuta
sunansa/ta a cikin “ILLIYUN”
wanda shine register ta sunayen
‘yan Aljannah. (Abu Daud, 4753;
Ahmad, 18063; Saheehul’Jamiy,
1676)

Yaa Allah ka ba mu ikon amsawa
daidai da shiga wannan rajista
mai daraja. Amin.

Tuesday, 3 April 2018

AUDIO : A Gobe Kiyama Shehu Tijaniyya Ya Dauko Jama'arsa ko Mala'iku Ba wanda Zai Tareshi kai su Aljannah - Inji Babban Shehin Tijaniyya

A GOBE KIYAMA IDAN SHEHU TIJJANI YA KWASO MU, BABU WANI MALA'IKA DA ZAIYI BURGE BA WANDA ZAI TSARESU SAI ALJANNAH WALLAHI - INJI WANI SHEHIN MALAMIN TIJJANIYYA.

Allah ya shiryemu ! Wani malamin darikar Tijaniyya ne yayi wannan lafazi a cikin tafsirinsa wanda yana da kyau yan uwa musulmi ku fahimci wannan darikar da kyau ku fahimci irin katobarar da ke cikinta.

Wanda inyass ya samu wannan matsayi a gobe lahira abun yayi muni.

Ga audio wannan karatun malamin domin ku saurara da kanku kada kuce karya nake sai kuji dala dala.

Latsa wannan link domin saurarin wannan maganar daga babban shehin malamin.



Download Audio here

Friday, 30 March 2018

Kungiyar Izala Ta Sauka Kasar Jamus Domin Gudanar Da Gagarumin Wa'azi (kalli Hotuna)


Wata tawagar malamman Izala daga Nijeriya da ta hada wasu fitattun malumai da suka hada:

Sheikh Bala Lau, Sheikh Kabiru Haruna Gombe, Sheikh Dr. Jabir Sani Mai Hula Sokoto, Sheikh Saifuddeen, (Daga Spain) Sheikh Mahmod da Sheikh Bature Amin.(daga UK) za su gabatar da gagarumin wa'azi mai taken 'Farfadowar Muryar Sunnah a  kasashen Turawa'.

Wanda za a yi a ranakun 31/3/2018 da 1-4-2018 Masjid Rahma Being, Gesunbrunnen 1 20537, Hamburng karfe 12:00 na safe da BuegerHaus Wilheems Burgh Mengestrasse 2021107 Hamburg 10:00-20:00.

Ga hotunan kamar haka


Tuesday, 27 March 2018

AL'AJABI: An Haifi Yaro Dauke Da Kur'ani Da Carbi A Jihar Bauchi: Wannan karamar Shehu Tijjani Ne Ta Kara Bayyana Ga Masu Inkarin Me Darikar Ta Tijjaniyya


...wannan raddi ne ga masu inkari da Annabi (S.A.W), cewar Sheik Dahiru Bauchi

Daga Maiwada B. Atake

Wata mata a garin Burga dake jihar Bauchi ta haifi yaro da Kur'ani da kuma carbi a hanunsa.

A yayin da matar ta zo da labarin al'ajabin zuwa gidan Shehin Malamin nan, wato Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ta shaida cewa, wannan yaro wanda aka rada masa suna Muhammad Auwal, haka ta haife shi. Ta kuma rantse da Allah cewa wannan lamari gaskiya ne babu kokonto.

A yayain hadubar Juma'ar da ta gabata da Sheik Dahiru Bauchi ya yi, ya ce "wannan ba komai bane a wurin Ubangiji illah raddi ga kafurai masu inkari da Annabi (SAW), don kara nuna musu cewa Manzon Allah gaskiya ne.

"Sannan ya kara nuna wa duniya irin mu'ujizar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam. Shine ya sa aka haifo wannan yaro da Kur'ani da kuma carbi".

Shehin Malamin ya kara da cewa "wannan carbi kuma ba komai bane face raddi ne ga masu inkarin Shehu Tijjani da darikarsa ta Tijjaniyya, don Allah ya kara nuna wa duniya cewa Dariku gaskiya ne.

Shehin ya kara da cewa duk ga alamomin Tijjaniyya a jikin wannan carbin. Wannan karamar Shehu Tijjani ne ta kara bayyana ga masu inkarin me Darikar ta Tijjaniyya.

A karshe Shehin ya yi addu'ar Allah ya kare Musulunci Da Musulmai, ya kuma zaunar da Nijeriya lafiya tare da kare ta daga dukkan bala'o'i.

Monday, 26 March 2018

AUDIO : Amsar da Dr. Sani Umar R/Lemo Ya Mayar Ma Yan Shi'a Akan Tambayar Da Sukayi Mashi Na Ya fassara Ayar Al-Qur'ani ba Daidai Ba!!!



A cikin wannan Amsar Dr sani umar r/lemo ya caccaki Yan Akidar Shi'a sosai wanda sunyi tambaya amma bisa jahilci wanda ya nuna biyane kawae suke basu san komai ba.

Wanda yana da kyau ku saurari wannan martani da ya mayar musu da sukace bai fassara ayar Al-Qur'ani dai dai ba.

Latsa wannan link domin downloading

Download Audio here

Ayi saurare lafiya !!!

Wasika Zuwa Ga Matasa - Daga Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Babban malamin addini Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa yayi wasika zuwa ga matasa na wannan kasar nigeriya da su yi amfani da wannan damar ta samartaka kafin ta gushe musu. 

Shehin mallamin yayi wannan wasika ne ga matasa 'ya'yan talakawa akan yadda suke rayuwa a cikin wannan kasar ga jawabinsa. 

"BAYAN GAISUWA DA FATAN ALKHAIRI,
INA YI MUKU ADDU'A DA FATAN SHIRIYA
WASU SUNA KIRANKU YAN JAGALIYA, 
WASU SUNA KIRANKU YAN SARA SUKA, 
 WASU SUNA KIRANKU YAN SHARA, 
 WASU SUNA KIRANKU YAN DABA, 
 WASU SUNA KIRAN SU YAN KALARE,
AMMA NI INA KARANKU MATASA MASU DARAJA , DA WASU MARASA KISHI SUKE AMFANI DA KU, DOMIN BIYAN BUKATUN SU NA SIYASA
A LOKACIN DA YAYANSU SUNA MANYAN MAKARANTU, DA MANYAN GIDAJE DA MAKUDAN KUDADE,
KUN TABA GANIN DAN WANI YANA SAI BABANSA
KIN TABA GANIN MATAR WANI DAGA CIKIN SU A WANNAN HALI DA SUKA JEFA KU.?
DON ALLAH KU YI WATSI DA WANNAN RAYUWAR KU KAMA ILMI DA SANAA.
MUYI TIR DA ALLAH WADAI GA MASU BATA MANA RAYUWAR MATASA".

AUDIO :Ko Ina Kano Aka Yi Bad’alar Gidan Gwamnati Sai Dai Mu Yi Allah Ya Isa”!!! Malam Aminu Ibrahim


“Ko ina Kano aka yi bad’alar gidan gwamnati sai dai mu yi Allah ya isa”!!! Malam Aminu Ibrahim 

Malam Daurawa yayi wannan jawabin ne a ranar Juma’a, 16-3-2018 a wajen karatun littafin “Adabul Mufrad” da yake gabatarwa duk sati a majalisin Ansarissunah na Marigayi Sheikh Abubakar Hussein (Albany) da ke Fagge, jihar Kano. Na yi qoqarin tsakuro jawabin da malam yayi akan surutu da kakaci da jama’a suke yi game da shirun da malam yayi akan “rashin kunya da fitsara” da Fatima Abdullahi Ganduje ta yi a wajen bikinta.

Malam yace: “a tafiyar da muka yi a satin nan, na samu saqo sama da 2000. Da hotuna da bidiyo. Aka yi ta yi min waya ana cewa “malam ana ta6argaza a Kano, ana raye-raye da kad’e-kad’e. Bayan na dawo, y’an jarida (da na Fesbuk, da na Whatsapp, da na rediyo, da na talabijin) suka cika a Hizbah suna jirana. Sai wani malami yayi min text, yace idan ka ga text dinnan ka kira ni. Na kira shi. Yace an ce ka tara y’an jarida a Hizbah za ka zuba, to kar [ka sake] ka zuba. Sai ya kashe wayarsa. Sai wani d’an jarida ma ya kirani, yace malam gamu duk an tara mu ana jiran kai so, to don Allah shawarar da zan bayar, kar kayi Magana akan abun. Amma ba dole ka d’au shawarata ba. Duk abinda ka ga dama kayi. Amma don Allah kar ka yi Magana. Na ce ai ni yanzu kun saka ni a tsaka mai wuya. Idan ban yi magana ba ace anyi laifi anyi shiru. Yanzu wanne zan d’auka? In je in yi cashiyata in more? Ko in yi shiru? Wanne ya fi? 

Idan na yi shiru, wad’anda suka saba in an yi abu ina magana, to za su ce to me ya sa malam yayi shiru. Wancan malamin kuma malamina ne, na yi karatu a agurinsa, yana cikin malaman da duk Kano ana girmama su. Shi kuma yace kar nayi magana, yanzu ina zan sa kaina! Don haka sai na zagaye na qi shiga Hizbar. Y’an jarida suka yi ta nema na. Na ce musu ina makaranta. Sai ga su yuuuu. Ni nake gudu suna bina [suna cewa] ‘akaramakallahu an yi ta6argaza, an yi 6arna, an yi shegantaka, an yi  tsalle-tsalle, an yi raye-raye, an kad’a d’uwawu, innalillahi wa inna ilaihirrajiun! Addini ya mutu a Kano. Mu talakawa da muke sa6o ku daina hana mu. Tunda ba kwa hana manya . . . . . Wani kuma yace akaramakallahu da kana bud’e wuta, yanzu kuma ka daina bud’e wuta. Wani kuma yace abinda ya sa malam ya qi magana, malam yana kare kujerarsa  da muqaminsa ne. Kar yace yar gwamna ta yi tabargaza gwamna ya cire shi. To ni da hizbah wa yake kare wani? Kujerar Hizbah har ta na da wani dad’in da za ka kare ta? To jiya ma sai da aka kaini qara kotu. Qungiyar kiristocin Kano sun dauki lauyoyi sama da goma sha, aka ce wai NA HANA MUTANE SU YI RIDDA A KANO!!!

Ka fito kace an yi ta6argaza a bune mai sauqi. Amma abubuwa dole ana tafiya ana lissafa su. In dai yanzu abinda mutane suke so za ka yi, to wallahi baza kayi komai ba. Duk abinda muke yi, yardarm Allah muke nema. Lokacin yakamata ayi magana za ayi. Lokacin da yakamata ayi shiru za ayi. Mutane so suke mu ringa yin abinda zai burge su, ba wai don Allah ba. Kamata yayi mutum yayi abinda ya dace. Da me zaginka, da mai yabonka, kowa yaje yayi abinda ya ga dama, irin tarbiyyar gidansu kenan. Duk wanda Allah ya bashi qarfin mulki, to ba kowane mai qarfi ba ne a qasa zai iya tunkararsa. Mu Hizbah kwamiti ne qwaya d’aya acikin kwamitocin gwamnati. To ta ya ya za ka kama fad’a da gwamnati? Sai dai ka yi mata nasiha! SAI DAI [MATSALAR] SU YAN SIYASA SUN FI JIN NASIHA A LOKACIN ZABE (shebi you understand?). BA SA JIN ALLAH YA CE ANNABI YA CE. SUN FI JIN TSORON RANAR ZABE. RANAR DA TALAKA ZAI RAMA. Ina cikin gwamnatin, aka zo aka ce za ayi fim village a Kano, gwamnatin na da ra’ayi, na fito nace ban yarda ba! Har daga fadar shugaban qasa sai da aka kira ni. A ka zo aka yi maganar rage shekarun auren y’a mace, duk da na san gwamnatin na da hannu aciki, amma nace ban yarda ba. 

A baya mun yi makamanciyar wannan maganar akan Masallacin Idi! Muka kira taron y’an jaridu. Muka ce mu a matsayinmu na malamai da suke cikin wannan gwamnatin (Zakkah, Hizbah, Shari’a) BA MU YARDA GWAMNATI TA MAIDA MASALLACIN IDI YA KOMA KASUWA BA. Muka rubuta arubuce, duk muka sa hannu, muka kaiwa gwamnati muka ce muna bada shawara kada ta kuskura ta ringa yanka massalaci ana siyarwa. Duk da mun yi abinda kuke so d’in, amma bai yi amfani ba. Kuma kowa yana kallo, ba wanda yace qala. Daga baya ma sai aka zo aka ce an bawa malamai fili d’ai-d’ai [hahhahahah]! Muka je muka kewaye masallacin, y’an jarida suka ringa cewa muna zanga-zanga [kun san an yi haka?]. Mu kace don Allah a qara inganta masallacin, a gyara shi, a sa masa tsaro, a qara fito da darajar Kano, amma [gwamnati] ta yi watsi da mu!

WANNAN BIKIN NA FITSARA, a halin yanzu, a koi’na ana yin shi. Gidajen da ake yi [a Kano] sun fi 100. Mun yi mun yi adaina, da mun bi ta can, sai azo mana da wata doka, ko mutum yayi rijista da da Fed govt. Wani gurin idan ka je ba zai shigu ba. Za ka tarar da sojoji da bindigogi. SU KUMA YAN HIZBAH BA YAN BOKO HARAM BANE! BALLE SU SHIGA GURI SU KWASHI YAN MATA KAMAR YADDA AKA KWASHI MATAN DAPCHI! Wani gurin za su je suga ana badala, amma ga sojoji a bakin gate, sai ince ku taho, ALLAH YA ISA! Yanzu ko ance ana badala a gidan gwamnati, ya d’an Hizbah zai shiga gidan gwamnati ya kamo wani? Gidan gwamnati fa! ‘Dan Hizbah ya je ya ture SOJA, DA DAN SANDA, DA DAN SIKYURITI, YA KAMA YAR GWAMNA, YA KAMA MATAR GWAMNA, YA KAMA MATAR WAYE . . . . . HABA!!! Ko da ina nan aka yi wannan sai dai mu yi Allah ya isa! Abun ya fi qarfinmu. Dokar da ta kafa abun [Hizbah] ba za ta iya ba. 

Akwai gwamnan Sakkwato, ana bikin y’arsa, yan Hizbar Sakkwato suka yi kabbara, suka ce Allahu Akbar, aje a tashi bikin, suka kai farmaki, sai gwamnan yace ya rushe Hizbar. Ba wanda yayi Magana [hahhahhhhah]. Sai ni na tashi na je na same shi, nace your excellency, ka yi haquri ka dawo da Hizbah, yace to malam ga abubuwa [kaza da kaza], nace yi haquri, yanzu ya bani aikin dawo da Hizbah a Sakkwato. Na je na samu gwamnan Katsina, nace don Allah ka kafa Hizbah, za ta yi muku amfani, yace ance in sun kama mutum, sai sun bud’a bakinsa sun shinshina sun ji wai ko ya sha giya. Na ce ba haka bane. Mun kafa makaranta a Kano wacce za ta ringa ba da ilimi. Ba za aringa bin mutum da gudu ba. Ko yanzu in ana biki, in aka kawo min rahoto, cewa nake kar ku je. Idan an fara kar ku je. Idan an gama kar ku je. Ku kawo min sunan mai gidan da adireshinsa. Idan an fara, ka tafi da gudu, akwai mata, akwai masu goyo, akwai yara qanana, da ance ga y’an Hizbah nan, sai a fara guje-guje, sai wani ya karye, wani ya ji ciwo, sai kuma a zo ace y’an Hizbah tsinannu! Subhanakallahumma wa bi hamdik . . . . 

Tsokaci: Wad’annan duk bayanan Malam Aminu Ibrahim Daurawa ne. Babu kalma ta ko d’aya. Kuma malam zai yi magana akan bikin nan. Wannan  kamar wata y’ar shimfida ce. Domin kawai magana ce ta shigo. Domin bi sa al’ada, malam ya fi yin cikakken jawabi wajen amsa tambayoyi. Kuma akwai sauran bayanai masu faida wanda ban kawo su ba. Saboda yanayin lokacina. Ga ma son kashe qishirwarsa akan cikakken bayanin, sai ya nemi karatun da kansa. In sha Allahu zan zo na yi sharhin wasu kalmomi daga kalaman malam.


Dukku Mai son Sauke audio sai ya shiga cikin Wannan link din 

  👇🏽👇🏽👇🏽

Download Audio here

Ayi Sauraro da Karantawa lafiya

Sunday, 25 March 2018

Wata kungiya ta karama sheikh Bala Lau saboda wa'azi akan shan Kwaya (kalli Hotunan)


Wata kungiya Mai fafutukar wayar da kan Al'umma akan illar shan Kwaya a Naijeriya karkashin jagorancin Amb. Adasu Fred T, ta karrama Shugaban Izalar Naijeriya Sheikh Abdullahi Bala lau Saboda Kira da yakeyi a wajen wa'azi da sauran karatuttukan sa da Adena Shan Kwaya.

Kungiyar Mai suna "Youths Against Substance Abuse And CRIME In Nigeria (YASAC)" tace tayi wannan karramawa ce domin Shugaba Sheikh Bala Lau yakan Yi kira Da Babban Murya akan Mimbarin wa'azi kan hana Matasa harma da Tsofaffi Da sudena Shan kwaya.

Sheikh Lau dai yakanyi kira ga Gwamnati Da hukumar hana shan Kwaya (NDLEA) Da Hukumar NAFDAC Su Tashi don kama tare da Hukunta masu shigo Da miyagun kwayoyi Da Gurbatattun abubuwa wadanda suke cutar da Al'umma.
Ga hotunan kamar haka:-



Saturday, 24 March 2018

A Kaduna Za A Yi Mauludin Sheik Ibrahim Nyass Ba A Abuja Ba, Inji Sheik Tijjani Abdulkadir Zaria



Shahararren malamnin nan kuma daya daga cikin jagororin darikar Tijjaniya dake garin Zaria, Sheik Tijjani Abdulkadir Zaria, ya bayyana cewa za a gudanar da Mauludin Sheik Ibrahim Nyass ne a garin Kaduna sabanin yadda wasu ke yada jita-jitar cewa za a gudanar da Mauludin ne a babban birnin tarayya Abuja.

Shehin Malamin ya yi kira da mabiya Darikar Tijjaniyya da su yi watsi da jita-jitar da ake ta yadawa na cewa za a gudanar da Mauludin ne a Abuja. 

Ya ce duk wanda ya samo wannan rahoto, ya samo sa ne ta barauniyar hanya, wanda ba shi da asali. Domin tun farko an tsara ne cewa za a yi Mauludin a Kaduna.

Shehin ya ce wasu mutane ne daga cikin su suke nema su yi amfani da wata dama da suke da ita domin kawo ruduni game da Mauludin. 

Ya ce Abuja ba ta nemi a bata karbar bakoncin Mauludin ba, amma jihar Kaduna ta nema, daga bisani kuma kwamitin kungiyar suka amince a gudanar a Kaduna. Ya kuma kara da cewa duk wanda ya ce Abuja za a gudanar, ya kawo masa takardar da ta tabbatar da cewa a Abuja za a gudanar da Mauludin.

Ya kuma kara da cewa kungiyar dake gudanar da Mauludin wato Maj'maul Ahbabul Sheik tana da rijistarta, kuma ita ta bayyana jihar Kaduna a matsayin wurin da za a gudanar da Mauludin, don haka bai ga amfanin wasu da ba su da hurumi a kungiyar ba su kawo cikas a tafiyar. 

Sheik Tijjani Zaria ya kara da cewa ko muryar wa aka ji ya bayyana cewa ba a Kaduna za a gudanar ba, kada a yarda da shi.

Za a gudanr da Mauludin na Sheik Nyass ne wanda aka saba gudanarwa a duk shekara a ranar 14 ga watan Afrilu, 2018 a dandalin Murtala Square dake garin Kaduna.

Tuesday, 20 March 2018

Muhimman Abubuwa Tara (9) Da Suke Kare Yaro Daga Fadawa Halaka Idan An Gina Shi Akai - Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

TUN RAN GINI TUN RAN ZANE 

MANZON ALLAH SAW YACE : DUK ABIN HAIHUWA, ANA HAIHUWARSA AKAN FIDRA TA ADDINI, IYAYE SU KE YAHUDANTAR DA SHI,  KO SU NASARANTAR DA SHI, KO SU MAGUZANTAR  DA SHI.
BUKHARI DA MUSLUM. 

IDAN KAGA YARO DA AL'ADUN YAHUDAWA, KO MAGUZAWA KO NASARA. 

daga irin tarbiyyar ce gurbattaciya da ya samu daga mahaifansa,  ko daga sakacin mahaifansa.

Ga abubuwa tara, da su ke kare yaro daga fadawa halaka idan an gina shi akai. 


1. na daya, imani da ingattaciyar akida

2. na biyu  Ibada ga Allah Kamar sallah azumi tun yana yaro. 

3. Na ukku halaye na Kwarai kamar gaskiya da kunya da amana da mutunci.

4. na Hudu: Ilmi na addini da zamani.

5. Na biyar : kula da lafiya da nisantar kayan maye.

6. Na Shida : zamantakewa Girmama Manya Da Tausayawa Kanana, da a bawa dukkan mai hakki, hakkinsa. 

7. Na Bakwai: Koya Masa sana'a Da Aikin yi. Domin Ya Dogara Da Kansa. 

8.Na Takwas:  Nuna Masa Illar Zina Da Luwadi Da madigo, Sa Dukkan mu'amala Mai  Muni. 

9. Na Tara:  Addua, Ta Neman Kariya Da Tsari Daga farmaki Shedan. 

Allah Ka Bamu Yaya Masu Albarka Da Tarbiyya.

Wednesday, 14 March 2018

Taƙaitaccen Tarihin Sheikh Abdul-Rahma Ibn Abdulaziz Wanda Ankafi Sani Da Al -Sudais


Daga Musa Badayi

Cikkaken sunan sa shi ne Shiek Abdul-Rahman Ibn AbdulAziz As Sudais. An haifishi a shekarar 1960, a Riyard, babban birnin kasar Saudi Arabia, ya fitone a daga cikin wani jinsi mai suna Anza. Al Sudais, ya haddace Alkur'ani, ya na dan shekaru 12, ya kuma kammala karatunsa na makarantar Sakandiri, a shekarar 1979, ya kuma kammala digirinsa, a fan nin Sharia, a shekarar 1983, ya yi wan nan digirinne a wata jami'ar Musulunci da ke Riyard, babban birnin Saudi Arabia.

Ya yi digiri na biyu, wato (masters), a cikin shekarar 1995, kuma ya yi digirin digirgir (Doctorate), duk a fannin Sharia. Ya yi aiki a jami'ar da ya kammala ta Riyard, San nan ya yi aiki a a jami'ar Ummal Qura, a matsayin mataimakin Farfesa. An zabe  shi ya zama limamin babban Masallacin Makka, ya na da shekaru 24, kachal, ya kuma yi hudubar sa ta fari ya na shekaru 24, a cikin watan july cikin shekarar 1984. A cikin shekarar 2012, ya zama babban mai kula da babban masallacin Makka, kuma aka ba shi mukamin minista.

Monday, 12 March 2018

Sheƙe Aya a Bikin Fatima Ganduje: Sheikh Aminu Daurawa Ya Wanke Kansa Dangane da Zargin kawar Da kai

Shugaban hukumar Hisbah ta jihar Kano, kuma fitaccen Malamin addinin Musulunci, Sheikh Aminu Daurawa ya bara game da cecekucen da ake yi a shafukan sadarwa na yanzar gizo inda ake zargin Hisbah da kawar da kai daga sheke ayar da aka yi a bikin diyar Ganduje.

Malam Daurawa ya bayyana haka ne a shafinsa na yanar gizo, inda ya bayyana wuraren da ya kasance tun bayan da aka daura auren Fatima Ganduje Angonta Idris Ajimobi,


“Ranar Asabar bayan a Daura aure kamar karfe daya, na kama hanya zuwa sokoto domin bitar littafi da Sheikh Mansur ya rubuta akan sharhin iziyya, bayan nayi kwana biyu, naje Zamfara nayi wa’azi na kwana guda, daga nan na wuce Kaduna nayi program a DITV na awa biyu.” Inji Daurawa.

Shehin Malamin ya cigaba da bayanin cewa: “A ranar Juma'a na yiwa mata wa’azi a Rigasan jihar Kaduna daganan na wuce masallacin Juma’a nayi pre-kudubah kuma na gabatar da khudubar juma'a. Bayan magariba nayi waazi a masallacin Shaik Rabiu Daura.

“Ranar Asabar da safe nayiwa mata waazi a masallacin Sultan Bello. Daga nan na taho Kano.Masu son su ganni na dawo Ina office.Bayan abubuwan da suka faru a wajan bikin yar Gov kowa yana jira yaji mai Daurawa zai fada, to ku mai kuke zaton zan fada?”

Jama’a da daman a zargin hukumar ne da rashin adalci da tsoron fada ma gwamnati gaskiya duba da irin sheke ayar da aka yi a bikin Fatima Ganduje, wanda ake yi ma kallo da keta haddin musulunci da ala’adara Hausa a bikin nata.

Wednesday, 7 March 2018

"SHIN 'DARIQA 'KUNGIYA CE???" Ga AMSAR Daga Sheikh Usman Dahiru Bauchi Ya Bayar Kamar Haka karanta kaji


:
Tambayar Da Wani Bawan ALLAH Ya Yiwa LISANUL-FAIDHA(Maulanmu Shehu Dahiru Usman Bauchi(R.A) Kenan.
:
:
"Ita 'DARIQA a 'Lugga' Tana Nufin Hanya, a 'Istilahi' Kuma Tana Nufin Riko Da Hanyar Bayin ALLAH Akan 'Azkaransu' Na Gyaran Zuciya Da Sharud'a, Ita 'DARIQA Tana a 'Muqamul Iman' Ne Daga Cikin Hawa Uku Na Musulunci, Ita Hanya Ce('Dariqa) Wadda Zata Kai Ka Zuwa Wajen Neman Wani Abu Shi Ne; Zikirin ALLAH, Amma Ba Wai Ita Ce Manufa Ba, Kamar Masallaci Ne Da Sallah, Shi Masallaci Ba Shi Bane Manufar, Shi Matakala Ne Zuwa Ga Abin Nema Shi Ne Sallah, 'DARIQA Ba 'Kungiya Bace, In 'Kungiya Ce To Waye Ne Chairman Na 'Dariqa a Nigeria, Waye Sakatarenta, Waye Treasury Na 'Dariqa(Na 'Kasa) Duka Babu, 'Dariqa Ba 'Kungiya Bace Makaranta Ce Ta Gyaran Zuciyar 'Dan Adam Kamar Yadda Mazhaba Ta Zamo Makaranta Ce Ta Fiqhu, To Haka Abin Yake".
:
Mun Gode SHEHU(R.A)!
:
ALLAH Ya 'Karawa SHEHU Lafiya Da Nisan Kwana, Ya Bamu Albarkarsu Don Alfarmar MA'AIKI(S.A.W). AMEEEEEN

Sources : fatyanul  islam of Nigeria 

Wata Sabuwa : Duk Wanda Ya Zagi SALATUL FATIH Ko Yayi Izgili Da Ita Haqiqa Yayi Ridda!! Inji Sheikh Dahiru usman Bauchi


Dalili kuwa shi ne Akwai ALLAHUMMA a Ciki ALLAHUMMA Ismu Zati Ne, ALLAH Ya Kan Iya Bada Aron SunayenSa  Duka Amma Ban Da ALLAH, Ya Kebanci ALLAH Ne Shi Kadai. 
.
Haka Idan Ance SAYYIDINA MUHAMMADU Idan Akace MUHAMMADU Duk Wanda Aka Masa Takwara Da MUHAMMADU Zai Iya Amsawa Amma In Akace ALLAHUMMA SALLI ALA MUHAMMADU Babu Wanda Ya Isa Ya Juyo Sai ANNABI MUHAMMADU(S.A.w) Shi Kadai Saboda Da Shi Akeyi. 
.
Haka Idan Akace WA ALA ALIHI NamMa Babu Mai Juyawa Sai Iyalan Gidan ANNABI MUHAMMADU(S.A.w.w) Su Kadai Don Matsayinsu Ne Babu Kamar Su, Sauran Abinda SALATUL FATIH Yake Fada Duka Sunayen MANZON ALLAH(S.A.w.w) Ne, Wanda QUR'ANI Yake Yabonsa Dasu Babu Wani Abu Sabo Wanda Ya Saba Wa Shari'a Don Haka Wallahi a Kiyaye Babu Abinda Yake Gaggawan Fidda Musulmi a Musulunci Irin Wasa Da Martaban MANZON ALLAH(S.A.w.w).
:
ALLAH Ya Kiyaye Mana Imanin Mu Alfarman MA'AIKI(S.A.w). 
.
AMIN SHEHU MUNGODE!
.
ALLAH Ya Ja Mana Kwananka Ya Qara Maka lafiya Da Juriya Alfarman SAYYIDUL SADATI(S.A.w.w) AMEEEEEEEEN.

Tuesday, 6 March 2018

Video : Shugabanni Kuji Tsoron Allah! Allah Zai Tambaye Ku - Dr Ahmad Abubakar Mahmud Gumi

SHUGABANNI KU JI TSORON ALLAH! ALLAH ZAI TAMBAYE KU

Wannan nasiha mai ratsa zukata ga dukkan wani mutum da yake yin shugabancin al'umma.

Yana da kyau ka daure ko baka ra'ayinsa ka saurari wannan nasiha
Allah yasa mu dace.

A cikin karatu da yayi yau Lahadi 04-03-2018 a Masallacin Sultan Bello Kaduna inda yake yin fassarar littafin Muwatta Malik.

Hukuncin mutumin

Lasta wannan link domin downloading wannan video



Download Shugabanni Kuji Tsoron Allah 

Thursday, 1 March 2018

AUDIO : ingattatun Addu'o'i Daga Littafen Hisnul Muslim Daga Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

GARABASA ! GARABASA!! GARABASA!!!

Ingattatun Addu'o'i Daga littafen Hisnul muslim

Daga Bakin

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Mallam yayi bayyanin ko wace addu'a domin kwadaitar damu da mu dage da yin wannan Addu'o'i domin samun falala da rahama da gafara daga Allah madaukakin sarki.


Ga Audio nan domin ku saurara kuma ka ajiye a wayarka domin wata rana.


Download Ingattatun Addu'o'i Hisnul muslim

Thursday, 22 February 2018

AUDIO : Falalar Boye Fushi Daga Sheikh Ja'afar Mahmud Adam Kano


Manzon Allah s.w.a Yana cewa duk wanda yake da damar nuna fushi amma boye  fushi a gobe kiyama Allah zai sashi aljannah yace zabi  wanda kake so a cikin Hurul'ini

Boye fushi kamar sadaki ne na hurul'ini a gobe kiyama.


Manzon Allah yasan abu ne mai matukar wuya mutum yana da damar nuna fushi amma hadiye shi saboda abu ne  mai matukar kuna a wajen hadiyewa balanata yanzu mutum na neman zalunci su kadai balanta an tabashi.

Kaji kamar baka ji ba, ka gani kamar baka gani ba lallai abu ne mai samama mutum daraja a gobe kiyama.

Babu masu boye wannan boye fushi sai masu hakuri da imani.

Ga Audion nan domin saurare

Download Audio here

Tuesday, 20 February 2018

Gane Mini Hanya : Hukumar SUBEB ta Hana Wazifa a Makarantun Tsangayar Bauchi

Rahotanni sun kawo cewa hukumar kula da ilimin bai daya wato SUBEB sashinj jihar Bauchi ta bukaci makarantun Tsangaya da su daina yin wazifa ko karanta salatul fatihi a hidimar makarantar.

A cewar hukumar hakan baya daga cikin tsarun makarantun a fadin jihar da ma tsarin hukumar UBEC ta fitar akan karatun Tsangaya.

Wannan bayani na tattare ne a wata takarda da shugaban hukumar ta SUBEB Yahaya Ibrahim Yaro ya fitar da sanya hannun sakataren hukumar Mahmeed A. Kari.


An saki wasikar ne a ranar 5 ga watan Fabairu mai taken wasikar dakatar da wazifa da salatil fatihi mai addireshi kai tsaye zuwa ga Shugabannin makarantun Tsangaya-Tsanya da suke fadin Bauchi.



Hukumar ta yi bayanin cewar ta samu korafin cewar ana tilasta wa dalibai yin wazifa da salatil fatihi.

Jaridar Leadershin ta rahoto cewa wannan mataki bai yi wa mamallakin wannan makarantar Tsangayar Sheikh Dahiru Bauchi dadi ba.

Sunday, 18 February 2018

AUDIO : Shi'a Ba Addinin Musulunci Bace Kafirci Ne Tsantsa: Inji Yayan Zazakky Yakubu Yahaya Katsina


Hujja Takobin Ahlul Sunnah ba ma karya ba ma yarfe sai dai muna fadin abinda mutun ya fadi da bakin shi.



Wannan Lecture ce da Yakubu Yahayya yayi bayan dawowar shi daga Iran kuma wannan shine a zuciyarshi Shi'a ba Musulunci bane amma yayi maku halin naku na munafurci wato TAKIYYA.

Shi yasa lokacin da Zakzaky yasa yaran shi sukai ma Atullahi Burtai rashin kunya yaki zuwa Zaria lokacin hasalima ya tafi amma da yaji linzami yafi karfin bakin kaza sai ya dawo yaki ya ida isa.

Haka lokacin da aka kuresu daga Masallacin Masarauta sai ya dauke ma mabiyan shi zuwa Sallar Juma'a.

Jiya kuma mun sanya ido domin muga Malam ya fito domin zagayen Ashura amma shiru kamar mushiriki yaci shurwa.

Duk wanda ya saurari wannan lecture da ya gabatar yasan Malam yasan aikin banza ne suke dan haka ba zai yarda ba yakai kanshi ga mutuwar asara.


SAURARA KAJI

Download Audio here 

Allah ya kara shiryamu shiri na Musulunci