April 2017 - NewsHausa NewsHausa: April 2017

Pages

LATEST POSTS

Sunday 30 April 2017

MUSIC: Deezell Ft. Morell, Classiq, Dj A.B, Kheengz& B.O.C – Ba Ruwan Mu



The Northern Heavyweight Mastermind in Geo collaboration - Deezell is out with the most anticipated single dubbed "Ba Ruwan Mu". Ba Ruwan Mu is a song which deezell enlist the Top Northern artiste such as (Morell, ClassiQ, DJ A.B, Kheengz & B.O.C).
Ba Ruwan Mu is a rap song which all the artiste showcases their rap versatility and delivered greatness on the self enriched tune. Deezell is creating something iconic and we've got more to watch out from him.

          Download Music here


Friday 28 April 2017

Jarumi SadiQ Sani SadiQ Kenan A Wurin Taron The Promise Cikin Kayan Sarauta.


Jarumi SadiQ Sani SadiQ Kenan Cikin Shigar Sarauta A Wurin Wani Taron Gangami Da Aka Gabatar A Jahar Kano Nigeria A Ranar 25th April 2017.

Taron Gangamin Me Suna "The Promise" Ya Hada Da Yawa Cikin Fitattu Da Kuma Shahararrun Mutane Na Daga Mawaka Irinsu Ice Prince, Dja, Da Kuma Fitattun Jaruman Masana'antar Kannywood, Kamar Irinsu SadiQ Sani SadiQ da makamantansu.





® www.Hausaloaded.com

An sallami jagoran 'yan Biafra Nnamdi Kanu daga kurkuku

An sallami jagoran 'yan Biafra Nnamdi Kanu daga kurkuku

An saki jagororin masu fafutikar kafa kasar Biafra, Nnamdi Kanu daga gidan yari bayan ya cika sharudan da wata babbar kotu da ke Abuja, babban birnin Najeriya, ta sanya masa.

A ranar Talata ne dai kotun, karkashin mai shari'a Binta Nyako, ta bayar da belin Mr Kanu saboda rashin lafiyar da yake fama da ita.

Sai dai ta sanya masa sharuda, wadanda suka hada da cewa ya gabatar da mutum uku wadanda za su tsaya masa kuma kowanne ya kasance yana da naira miliyan 100.
Mai shari'ar ta ce ba a yarda a gan shi a cikin taron jama'ar da suka wuce mutum 10 ba.

Ta kara da cewa "kar ya yi hira da 'yan jarida kuma kar ya shirya kowacce irin zanga-zanga".

Wannan ne karon farko da aka bayar da belinsa tunda aka fara sauraron shari'ar da ake yi masa kan zargin cin amanar kasa.

Ana tuhumar Mista Kanu, wanda shi ne shugaban kungiyar Indigenous People of Biafra, IPOB, tare da wasu mutum uku, wadanda duka suka musanta zargin da ake yi musu.

Mista Kanu ya shafe sama da shekara guda a tsare.

sources:bbchausa.com

Aisha Aliyu Tsamiya, Umar M Shareef Da Ado Gwanja, Zasu Zo Sokoto Waje Yin Wasa

Aisha Aliyu Tsamiya, Umar M Shareef Da Ado  Gwanja, Zasu Zo Sokoto Waje  Yin Wasa.

Ina masoyan  Aisha Tsamiya da masoyan  Umar M. Sharif tare da masoyan   Ado Gwanja, to Albishirinku. 

Shahararriyar Yar Wasar Fim din Hausa Aisha Aliyu Tsamiya, Shahararren Mawakin Hausa Umar M. Sharif tare da Shahararren Mawakin Hausa Ado Gwanja, za su zo Sokoto wajen yin Wasa.

Kungiyar Makaranta Mujallar Fim ta Kasa, itace ta shirya wannan wasar, wadda ba'a taba irin ta a Jahar Sokoto ba. 

Za'ayi wasar ne kamar haka.


                AISHA ALIYU TSAMIYA.

Zata yi  wasa Ranar Assabar 29 April, 2017.
Daga Karfe 03:30 Na Yamma Zuwa 06:30 Na Dare. 

Daga Karfe 08:00 Na Dare Zuwa 10:30 Na Dare. 


                   UMAR M.SHARIF. 

Zai tashi Wasar  Ranar Lahadi 30 April, 2017.
Daga Karfe 03:30 Na Yamma Zuwa 06:30 Na Dare.

Daga Karfe 08:00 Na Dare Zuwa 10:30 Na Dare.


                  ADO ISAH GWANJA. 

Zai tashi wasar a Ranar Attanin 01 May, 2017. 
Daga Karfe 03:30 Na Yamma Zuwa 06:30 Na Dare. 

Daga Karfe 08:00 Na Dare Zuwa 10:30 Na Dare. 

Dukkan su zasu yi wasar ne a Ahmad Maigero open Theater, kusa da gidan Gwamnatin Jahar Sokoto.

Kudin shiga wajen wannan wasar kuwa, ba'a sanya su da yawa ba. 

Daga Dan Shekara 18 zuwa sama zasu biya kudin shiga Naira Dari biyar Kacal #500. 

Daga Dan Kasa da shekara 18 zuwa kasa, su kuma zasu biya Naira uku kacal #300.

Domin karin bayani, sai ku tuntubi wadannan Lambobi, kamar haka. 

1. 08069661227. 
2. 08069452044.
3. 08095874748.
4. 08034543434.
5. 07035967561. 
6. 08030836649.

SANARWA DAGA. 
Kungiyar Makaranta Mujallar Fim Ta kasa Reshen Jahar Sokoto.

Bahubali 2: Fim ɗin da aka jima ba a yi kamarsa ba

Bahubali 2: Fim ɗin da aka jima ba a yi kamarsa ba

A ranar Juma'a ce aka fitar da wani shahararren fim ɗin Bollywood a kasar Indiya mai suna Bahubali kashi na biyu.

Fim ɗin Bahubali na 2 tun kafin fitarsa, ya ja hankalin mutane ciki har da wadanda ba su damu da kallon fina-finan Indiya ba.

Tun a ranar Alhamis, aka fara nuna wannan fim a Amurka.
Shi ne irinsa na farko da aka kashe makudan kuɗaɗe wajen shirya shi, saboda haka ne a kusan ko'ina duniya ake maganarsa.

A Indiya kadai, za a nuna shi a Silimu sama da 6,500 cikin manyan yaruka daban-daban na kasar, babu wani fim da ya taɓa samun irin wannan tagomashi a tarihin Bollywood.
Fim ɗin, ci gaba ne daga Bahubali kashi na ɗaya, wanda ya fita a shekarar 2015, kuma ya samu karɓuwa sosai a duniyar fina-finai.

Sharhi, Aisha Shariff Baffa

Babban dalilin da ya sa Bahubali na biyu ya samu karɓuwa a wajen mutane shi ne yadda ya yi tsokaci cikin sha'anin masarauta.

Ya fito da irin kutungwila da maƙarƙashiyar da ke da alaƙa da neman mulki a wajen wasu. Bayan kashe wani sarki a fim ɗin na Bahubali, sai kuma ake yunƙurin kashe ɗansa.
Abin da mutane ke son gani a kashi na biyu shi ne, dalilin da ya sa babban na hannu daman sarkin, ya ci amanar sarki ta hanyar kisan gilla.

A Nijeriya, masu sha'awar fina-finan Indiya ba a bar su a baya ba, inda suka shiga sahun masu alla-alla su ga fitowar Bahubali na biyu da ke faɗin duniya don kashe kwarkwatar idanunsu a wannan fim.

Source :bbchausa.com

Thursday 27 April 2017

KANNYWOOD:AMMAAWARD Nomination Dinner 2017

AMMAWARDS stands for Arewa Music and Movie Awards which is an annual award giving ceremony in which some professionals in the Kannywood Film industry are awarded for the role played by them or for a film script written by them.

–Kannywood scene Blog
– Kannywood Scene twitter
Below are some photos of the films, Actors and some writters nominated during the AMMAWARDS Nomination dinner Sunday night.

Ali Nuhu was nominated for Best Actor in a leading role with Umar Sanda at the #AMMAAwards 2017 nomination dinner Sunday night.


Fauziyya d suleiman
, Maula writer was nominated for Best Original Screenplay.

Rabiu rikadawa was nominated for baya da kura
Baya Da Kura Mafarin Tafiya writer, Ibrahim Birniwa was nominated for Best Adapted Screenplay.

Jamila Nagudu was nominated for Best Actor female in a leading role with Maula

Saddiq Sani Saddiq was nominated for Best Actor in leading role with Kasko.


Nuhu Abdullahi was nominated for Best Actor in a Supporting role with Furuci.

Hisabi was nominated for Best Film.


Tahir I Tahir was nominated for Best Set Designer with HIJIRA.
HIJIRA was nominated for Best Movie, Best Background Score, and the Movie with Best Costume.


There’s a Way was nominated for Best Film.

Script Writer Yakubu M Kumo, has been nominated for Best Original Screenplay with Hijira, Salma and Yazeed.

Asma’u Sadiq (Nass) was nominated for Best Actress in a Supporting role with Fatima Ko Zarah.

®arewamobile.com

Wednesday 26 April 2017

Najeriya: fasahar zamani zata samar da ayyukan yi sama da miliyan 3


Newly appointed Director-General of the National Information Technology Development Agency (NITDA) of Nigeria, Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami. iittelecomdgest.com
Hukumomin Najeriya sun ce fasahar zamani zata samar da ayyukan yi sama da miliyan 3 da kuma kudaden shiga ga kasar da yawansu ya kai Dala biliyan 88 nan da shekaru 10 masu zuwa.
Ministan kasuwancin Najeriya Dr Okechukwu Enelamah, ya bayyana haka a wajen wani taron ministocin kasashe masu tasowa da ake gudanarwa a birnin Geneva karkashin Majalisar Dinkin Duniya.
Enelamah yace Najeriya na da dimbin matasan da suka yi fice a fannin kere kere da sadarwa wanda zai taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin kasar.
Yayin zantawarsa da sashin hausa na RFI, Dr Isa Ali fantami, Darakta Janar na Hukumar NITDA dake kula da fasahar ta zamani a Najeriya ya ce lokaci ne yayi da Najeriya zata kauracewa dogaro da man fetur domin karfafa tattalin arzikinta, idan aka yi la’akari da halin da kasar ta fada na matsi sakamakon dogaro kan abu daya.
Dr Fantami ya ce fasahar na’ura mai kwakwalwa na kan gaba wajen hanyoyin da zasu taimakawa Najeriya wajen samar da ayyukan yi.

Abin da ya hana Buhari halartar taron majalisar zartarwa


A karo na biyu Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari bai halarci taron majalisar zartarwa da ake yi duk ranar Laraba ba, abin da ya kara jefa fargaba kan halin da yake ciki.
'Yan kasar da dama na ganin shugaban bai halarci taron ba ne saboda rashin lafiyar da yake fama da ita, kuma wasu na nuna damuwa kan halin da yake ciki.
Sai dai ministan watsa labarai na kasar Lai Mohammed, ya ce shugaban na ci gaba da hutawa ne a gidansa.
Tun bayan da shugaban na Najeriya ya koma kasar daga jinyar da ya kwashe kusan kwana 50 yana yi a birnin London, ya ce ba zai rika yin aiki sosai ba saboda yanayin jikinsa.


Tun bayan da shugaban ya dawo kasar dai, ba kasafai yake bayyana a bainar jama'a ba.
Mataimakinsa Yemi Osinbajo ne yake gudanar da yawancin al'amuran gwamnati, kuma wasu na ganin hakan yana kawo tsaiko wurin tafiyar da al'amura.
Sai dai mai magana da yawun shugaban Malam Garba Shehu ya shaida wa BBC cewa babu wani abu da ya tsaya a harkar gwamnati saboda matakin da shugaban ya dauka.
"Ya fada da bakinsa cewa bai taba yin jinya wacce ta ba shi wahala kamar wacce ya yi a birnin London ba," kuma ya fada cewa zai ci gaba da huta wa, in ji Garba Shehu.
A lokacin jinyar da ya yi dai, sai da likitoci suka kara masa jini, ko da yake bai fadi larurar da ke damunsa ba.
A lokacin, shugaban na Najeriya ya ce yana samun sauki sosai, "amma watakila nan da makonni kadan masu zuwan zan koma asibiti".
Shugaban dai yakan fito masallaci da ke fadarsa duk ranar Juma'a domin halartar salla.

Tuesday 25 April 2017

Fitattun Hotuna Daga Wurin Daukar Film Din ARASHI.

Fitattun Hotuna Daga Wurin Daukar Film Din ARASHI.
Daga :- Sunusi Oscar
Film Din ARASHI film ne dake dauke da fitaccen matashin Jarumin nan dake tashe a duniyar Kannywood a yau wato Garzali Miko.
Ga Hotunan nan ku kalla.








Saturday 22 April 2017

Kyawawan Hotunan Ango Sallau Da Amaryar Sa Da Zai Aura Furere Na #Arewa24 Dadin Kowa


Abu Kamar Wasa Kamar Gaske .. A Kwanaki Ne Aka Fitar Da Sanarwar Auren Umar S. Jigirya Wanda Akafi Sani Da Sallau Tare Da Amaryarsa Amina Muhammad Wanda Akafi Sani Fa Furere Waton Yan Wasan Dirama Na Shirin Dadin Kowa Da Ake Gabatarwa A Tashar Arewa24,
Kamar Yanda Muka Sani A Cikin Shirin Furere Itace Matar Sallau ..
Kwanci Tashi Ashe Da Gaske Ma Haka Allah Ya Kaddara Abunsa ...
Ga Sabbi Kyawawan Hotunan Sunan Kafin Auren Sau







Jarumi Lawan Ahmad Ya Sami Kyautar Sabuwar Mota.


Dan wasan fina-finan Hausa, Lawal Ahmad ya samu kyautar sabuwar Mota kirar Marsandi E320 a taron da jihar Katsina ta shirya domin karama jarumai yan asalin jihar.

Jihar Katsina a kowace shekara tana shirya taron karrama jarumai yan asalin jihar musamman wadanda suka nuna hazaka a fanni dabam dabam wanda ya hada da harkan kasuwanci, shakatawa da wasanni.

Da gidan Jaridar Premium Times ta tattauna da shi, Lawal Ahmad ya nuna farin cikin sa kan wannan karramawa da ya samu.

“ Ba’a taba yin irin wannan a Kannywood ba. Akan hada irin wadannan bukukuwa na karramawa amma sai dai a baka 
kwalin. Ita kuwa wannan Motace sukudun aka mika mini. Aiko kaga irin haka shine na farko a farfajiyar Kannywood.
“ saboda wannan karamci da na samu dama ina da mota da ni ke hawa kirar 406, zan ba matata ita ma ta hau.

KALLA CIKIN HOTO..





Banyi Dana Sanin Zuwana Kasar Amurka Ba -- Rahama Sadau


Jaruma Rahma Sadau ta musanta zargin da akeyi ma ta cewa tayi danasanin zuwa kasar America. - Acewar jarumar ba wani da nasani da nayi domin adalilin sana'a naje bada niyar shashanci ba.

Amma abinda nasan nace shine, "tabbas akwai banbanci tsakanin America da Nigeria awajen yin fim," banbancin abayane yake.
idan kai bahaushe ne to kayi sana'ar fim din hausa yafi maka amfani. domin shine wanda zai kare mutuncin mutum.

Dan haka a ra'ayina Hausa fim yafi min American fim, amma awajen hausawa.
kuma ni da America gwara kasata Nigeria. wannan maganar nasan kawai na fada amma jama'a sai suka canja min magana.

Sannan kuma Jarumar ta kara da cewa zanyi amfani da wannan damar nayi godiya zuwaga Ali Nuhu, Sani Danja da sauran mutanen da suke kokari awajen ganin nadawo masana'antar hausa fim.

® Naij Hausa

Rahma Sadau Ta Maka Nafisa Abdullahi A Kotu.


Jaruma Rahma Sadau ta maka Nafisa Abdullahi a kotu. wanda tace tana neman hakin ta agun Nafisa Abdullahi.

Wanda tace ta hana ta kudin ta har naira dubu tamanin da tara. Wanda Rahma Sadau taba Nafisa Abdullahi domin ta fito acikin fim din ta maisuna RARIYA. Amma har aka gama yin fim din Nafisa Abdullahi bata fito koda sau daya acikin fim din ba.
Anayin wannan sharia'a ne akotun Nomans land dake jihar Kano.

Majiyar mu ta kotu Sadiya Rk Panshekara ta ruwaito mana cewa: za'aci gaba da sauraron shar'ar ranar litinin.

Kamar yadda majiyarmu ta tattaro cewa a zantawar da wakiliyar mu tayi da wadda akeyin kara Nafisa Abdullahi sai jarumar tace: ni ba wasu kudi da Rahma ta bani dan nayi mata fim.

Abinda nasani shine, tace tanaso na fito acikin fim din ta maisuna RARIYA nace zan fito amma sabida wasu dalilai ban fito ba, amma ni ba wasu kudi da ta bani. Inji Nafisa Abdullahi.
To, mu dai aikin mu bibiya. zamu ci gaba da kawo maku yanda shari'ar take tafiya.

® Naij Hausa

Zamu Saki Film Din Mansoor Da Karamar Sallah_Ali Nuhu

Shahararre kuma gogarman Kannywood, jarumi Ali Nuhu ya bayyana cewar fim din kamfanisa, Mansoor da aka kammala dauka kwanan baya za a sake shi a sinumun Nijeriya lokacin bukukuwan karamar Sallah.
Jarumin ya bayyana haka ne yayin tattaunawar musamman da wakilinmu ta wayar tarho, inda ya ce duba da yanayin irin aikin da aka yi wa fim din, kamfanin FKD sun yanke shawarar sakinsa a bukukuwan sallah.

“Mansoor fim ne da aka kashe makudan kudade wajen yin sa, saboda haka hanyoyin tallata shi kadai sun bambanta da yadda ake yi wa saura finafinai. Mun zabi lokacin bukukuwan karamar sallah ne domin domin bawa mutane damar kallon sa kasnacewar ana hutu.” A cewar Ali Nuhu.


“Mutane da yawa sun kagu su ga wane sako Mansoor ke dauke da shi, abin da nake so in tabbatar shi ne, fim din ya zo da wani irin salo wanda ba a saba gani ba.


“Duk wanda ya ga yanayin jaruman da aka sanya a cikin fim din, zai ga cewa sabbi ne, watau wadanda ba su taba fitowa a matsayin cikakkun jarumai ba. Da ma shi kamfani FKD ba bako ba ne wajen dauko kananan jarumai ya wanke su, sannan ya saka su a finafinansa.” In ji shi.

Mansoor fim ne da ya hada jarumai irin su Ali Nuhu, Baballe Hayatu, Abba El-Mustapha, Tijjani Faraga; sai kuma sabbin jarumai, Umar M Shareef da Maryam Yahaya.

Wannan dai shi ne fim na farko da FKD ta shirya tun bayan fim din da ya tara zaratan jarumai maza zalla watau Ga Mu Nan Dai.

® Leadership Hausa