Rahoton ya ce, a yanzu darajar Kane ta kai Euro miliyan 194. Hakan ya bashi damar zama mafi tsada ko darajar bayan dan wasan kungiyar PSG Neymar kan 213, da kuma Lionel Messi na Barcelona kan euro 202.
An dai kafa ginshikan wannan bincike ne ta hanyar la’akari da darajar ‘yan wasan, a kungiyoyinsu na nahiyar turai bisa matakan shekaru, kwarewa, tsawon yarjejeniyar da suka sanyawa kungiyoyinsu hannu da kuma kimar ‘yan wasan a kasashensu.
A shekarar da ta gabata, Harry Kane ya samu nasarar cin kwallaye 56, a wasannin da ya bugawa kungiyarsa ta Tottenham da kuma kasarsa Ingila, hakan ya bashi damar zama dan wasan da ya fi kowa yawan kwallaye a nahiyar Turai.
Sauran ‘yan wasan da kungiyar sa idon ta CIES ta fitar da matsayin darajarsu a fagen na kwallon kafa, sun hada da Kylian Mbappe na PSG a matsayi na 4 kan euro miliyan 192.5, sai kuma Paulo Dybala na kungiyar Juventus a matsayi na 5, kan euro miliyan 174.6.
Dele Alli na Tottenham shi ne dan wasa na 6 mafi daraja kan Euro miliyan 171.3, sai kuma Kevin de Bruyne na kungiyar Machester City a matsayi na 7, kan euro miliyan 167.8.
Binciken kungiyar ta CIES, ya nuna dan wasa na 8 mafi daraja shi ne Romelu Lukaku na Manchester United kan euro miliyan 164.8, shi kuwa Antonie Griezman na Atlectico Madrid na a matsayi na 9 kan euro miliyan 150.2.
Paul Pogba na Manchester United shi ne dan wasa na 10 kan euro miliyan 147.5
Gwarzon dan wasan duniya na shekarar 2017, Cristiano Ronaldo kuwa, ya tsinci kansa ne a matsayi na 49, inda yake da darajar euro miliyan 80.4.
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment