Duniya Ina Zaki Da mu : An Cafke Amaryar Da Ta Kashe Mijinta A Jihar Kano - NewsHausa NewsHausa: Duniya Ina Zaki Da mu : An Cafke Amaryar Da Ta Kashe Mijinta A Jihar Kano

Pages

LATEST POSTS

Wednesday 10 January 2018

Duniya Ina Zaki Da mu : An Cafke Amaryar Da Ta Kashe Mijinta A Jihar Kano


Rundunar 'yan sanda ta jihar Kano ta yi nasarar cafke wata Amarya da ake zargi ta kashe mijinta ta hanyar sanya masa guba cikin abinci.

Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, Magaji Majiya ya shaida wa manema labarai cewa 'yan uwan mijinta ne suka kai rahoto ofishin 'yan sanda da ke Kofar Wambai a birnin Kano.

Ya ce ana zargin Amaryar da sanyawa mijinta guba ne ranar alhamis 4 ga watan Janairun 2018 kuma ya rasu ne bayan kwana guda da sanya masa gubar.

Kakakin rundunar ya ce a lokaci da 'yan sanda suka isa gidan sun tarar cewa Amaryar ta tsere kafin daga bisani aka cafke ta ranar Litinin din da ta gabata.

Wasu rahotanni da ba a tabbatar ba sun ce an yi wa Amaryar auren dole ne.

Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment