Babu wanda zai sake lashe gasa idan ina Kannywood' - NewsHausa NewsHausa: Babu wanda zai sake lashe gasa idan ina Kannywood'

Pages

LATEST POSTS

Wednesday 16 August 2017

Babu wanda zai sake lashe gasa idan ina Kannywood'


Sadiq ya ce ya kamata a rika yi wa 'yan fim uzuri
Image captionSadiq ya ce ya kamata a rika yi wa 'yan fim uzuri

Fitaccen jarumin Kannywood Sadiq Sani Sadiq ya ce kwarewarsa ta iya taka kowacce rawa ce ta sa ya lashe gasar jarumin jarumai sau uku a jere.
"Idan har Ina cikin Kannywood ni ne zan ci gaba da lashe gasar jarumin jarumai a ko wacce shekara saboda ba na wasa da aikina", in ji Sadiq Sani Sadiq, a tattaunawa ta musamman da BBC Hausa.
Ya musanta zargin da ake yi cewa yana jajircewa a fim ne domin ya dusashe taurarin jarumai Ali Nuhu da Adam Zango, yana mai cewa "su iyayen gidana ne domin kuwa sun taimaka min sosai a wannan harkar. Ka ga kuwa babu wanda zai ja da iyayen dakinsa."
Sadiq Sani Sadiq, wanda ake yi wa lakabi da Dan marayan zaki, ya kara da cewa yana son dansa ya gaje shi.

Sadiq ya ce ya kamata a rika yi wa 'yan fim uzuriHakkin mallakar hotoINSTAGRAM/SADIQ SANI SADIQ
Image captionSadiq ya ce ya kamata a rika yi wa 'yan fim uzuri

Jarumin ya ce a baya ya yi kiwon karnuka sosai shi ya sa "da aka sa ni a wani fim a matsayin mafarauci ban fuskanci wata matsala ba".
"Abin da ya sa nake iya taka ko wacce rawa shi ne, na yi hulda da mutane daban-daban a rayuwa tun ma kafin na soma fim. Shi ya sa idan aka sa ni a matsayin mai sayar da shayi, misali, za ka ga na yi abin tamkar mai shayin gaske saboda na taba yin hulda da shi," in ji jarumin.
Sadiq Sani Sadiq ya bayyana zargin da ake yi wa 'yan fim na neman maza da cewa "karya ce kawai. Ni ban taba ji ko ganin wanda yake luwadi ba. Kuma na dade Ina yin fim. Ka ga kuwa tun da haka ne sai kawai in ce karya da kazafi ake yi mana."
Ya ce ba aikin 'yan fim ne koyar da mutane tarbiya ba kamar yadda wasu ke hasashe, yana mai cewa, "duk wanda ya ce 'yan fim sun bata masa tarbiyya da ma ba shi da ita. Ai tun daga gida ake samun tarbiyya".


Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment