Fadakarwa Ta Sa Ni Shiga Harkar Fim Din Hausa - Inji Wata Jaruma - NewsHausa NewsHausa: Fadakarwa Ta Sa Ni Shiga Harkar Fim Din Hausa - Inji Wata Jaruma

Pages

LATEST POSTS

Wednesday 23 August 2017

Fadakarwa Ta Sa Ni Shiga Harkar Fim Din Hausa - Inji Wata Jaruma


Babban burina shi ne na zama tankar Hadija Gabon, a harkar fim baya ga ilimantarwa da zan yi ta harkar, inji matashiyar jaruma Amina Yola.

Ta ce ta shiga harkar fim domin sana’a ce da take burge ta mussaaman ma yadda suke fadakar da jama’a abubuwan da suke faruwa na yau da kullum.


Matashiyar ta bayyana cewa bata shiga harkar fim ba sai da ta karbi izini daga wajen iyayenta , inda ta ke cewa harkar fim harka ce da sai an hada da hakuri, ganin cewar ana mu’amala da mutane da dama.
Amina ta ce tun daga garin Yola ta zo Kano, ta kuma sayi form din shiga sana'ar bayan kammala bincike aka bata gurbin karatu.
Kawo yanzu dai ta ce ta cimma burinta, tunda ta shiga harkar kuma abinda ranta ke so Kenan. daga karshe ta ce a duk iya lokacin da take cikin wannan masana’anta bata fuskanci wata matsala ba.


Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment