Dabarun Girki Guda 12 Da Za Su Maida Ke Tauraruwa A Kitchen - NewsHausa NewsHausa: Dabarun Girki Guda 12 Da Za Su Maida Ke Tauraruwa A Kitchen

Pages

LATEST POSTS

Sunday 27 August 2017

Dabarun Girki Guda 12 Da Za Su Maida Ke Tauraruwa A Kitchen


Iya dafa abinci kadai ba ya tabbatar da zamowar ki gwarzuwa a kitchen, dole sai kin iya wasu dabaru na yadda zaki biyo da matsaloli idan sun taso, yadda zaki gujewa almubazzaranci, yadda zaki hana kayan hadin ki lalacewa da wuri, yadda zaki rage bata lokaci wajan girki, da dai sauran su.

Sai dai yawancin wadannan dabaru su kan dauki shekaru kafin a gano su, wasu kuwa ma in har ba fada miki su aka yi ba baza ki taba gano su ba
Wannan ya sa Mujallar Al’ummata ta tattaro miki manyan dabarun nan guda 12 domin samun saukin ki :

Kayan Lambu: Karas, Kabeji, Koren wake da Ganyayyaki

1.Karas da kabeji suna da saurin yamushewa, sau da yawa sai dai mu zubar da su idan sun yi kwana biyu. Abin da baki sani ba shine, idan da zaki jika su a ruwa na dan awanni kafin kiyi girki, toh za su kara tauri su kame kamar yanzu kika sayo su, musamman ma karas. shi kabeji idan za ki masa haka sai kin yayyanka tukun.
2. Shi kuwa koren wake, idan kina so ki tabbatar da bai canja kala ba a cikin girki, to ki dan jika shi a ruwan kanwa na dan lokaci kadan kafin ki zuba shi a dahuwar ki.
3. Idan kina son ajiye koren ganye kamar alayyahu ba tare da ya lalace ba, to ki hura ledar da zaki ajiye shi da iska kafin ki daure

Kwai da bawon sa

4. Bare kwai da yawa a lokaci daya akwai bata lokaci, saboda haka zaki iya zuba su gaba daya a kwano ki girgiza da karfi, zasu fasa kansu amma fa ba zasu fito da kyau ba. Wannan kuwa a gani na ba matsala ba ne idan yayyankasu dama za kiyi, kamar wajen hadin salad.
5. Zaki ga wani lokacin idan kika fasa danyen kwai, bawon sai ya faffashe a ciki, kuma cire su ya kan bada matsala saboda tsantsin da kwan yake da shi. To abinda zakiyi a nan shine, ki dan karyi bawan kwan da kika fasa me dan tsini, sai kiyi amfani da shi.
Ko kuma ki saka ruwa a hannun ki kafin ki cire, wannan zai rage santsin kwan.
6. Idan kina da ajiyayyun kwai amma baza ki iya banbance tsakanin lalacacce da mai kyau ba, toh ki zuba su gaba daya a cikin ruwa. Za ki ga wanda ya lalace ya yo sama. Masu kyan kuma sun kwanta a kasa.

Leman bawo

7. Idan ba kya son acid din da ke cikin Lemo ya tsarto miki idan kin zo barewa, za ki iya dan gasa shi a cikin microwave ko kuma ki mulmulashi a kasa da kyau kafin ki bare

Dankalin turawa

8. Kowa ya san bare shi akwai cin rai da daukan lokaci. Toh idan amfanin da zaki yi dashi yana bukatar dafaffen dankali ne ba danye ba, kamar idan zaki yi potato salad, toh abin ya zo da sauki.
Zaki fara dafa dankalin, idan ya dahu sai ki zuba masa kankara na dan lokaci, zaki ga bawon ya bar jikin dankalin, sai ki kwashe shi kawai za kiyi.

Albasa

9. Idan ba kya son yajin albasa ya shiga idon ki a lokacin da kike yanka ta, toh zaki iya dan cizar bredi a bakin ki, barin sa daya yana waje yayin da kike yankan. Biredin zai shanye gas din da yake fitowa daga albasa kuma zai hana shi isa idon ki
Ko kuma zaki iya daskarar da albasar, sai ki yanka ta a daskare. Tunda gas din ya daskare ba zai tashi ya shiga ido ba. Matsalar wanna shine ba zaki iya barin albasar ta huce ba saboda zata koma lubulubu.
10. Ba kya son warin albasa ko tafarnuwa a hannunki? Zaki iya shafa Leman tsami ko kuma baking soda sannan ki wanke.

Miya ko abinci mai borowa

11. Idan zaki dafa abinci ko miyar da kika san tana da zuba idan ta tafaso, kuma ba kya san bude tukunyar ki ki bar ta a bude, toh zaki iya dora cokali ko ludayin katako a kan tukunyar kafin ki rufe. Tunda katako baya jin zafi, wannan zai hana ruwan taba murfin.

Tsadar Tumatir

12. Kasancewar tumatir yana da lokacinsa na araha da kuma lokacin da baya sayuwa, ga wani dan dabara da zaki iya yi domin ajiye danyen tumatir na lokaci mai tsaho.
Zaki sayi danyen tumatir dinki da yawa kamar Kwando daya, ki markada shi ki dafa. Sai ki tsane ruwan ki shanya shi a rana ya bushe karau, sai ki zuba shi a kwali ki ajiye.
Idan lokacin amfani ya zo zaki dauki daidai yanda kike so, ki dauraye shi da ruwan sanyi. Sai ki zuba ruwan zafi ki barshi ya narke. Za ki ganshi yayi kyau kamar a lokacin kika niko. Sai ki kara attaruhun ki, da albbasa ki ja miyar ki.
Da fatan wadannan yan dabaru zasu saukaka rayuwarki su kuma taimaka miki wajen kara inganta gidan ki.
 Sources:alummata.com


Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment