Daga Ahmadu Manaja Bauchi
Har yau bayan kwana goma da dawon Shugaban kasa Muhammadu Buhari, masoya da magoya baya na cigaba da gudanar da gangami dama shirya walima a garin Bauchi domin nuna godiyan su ga Allah da ya dawo da Shugaba Buhari, gida lafiya daga birnin Landan.
A makon da ya gabata Shugaban matasan jam'iyan APC, na jihar Bauchi haka kuma jagoran masoya Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a jihar Bauchi wato Alhaji Nasiru Umar Gwallaga ya jagoranci Mata da maza na garin Bauchi, inda suka gudanar da gagaruman gangamin da ya dauki hankalin Nijeriya.
Inda a wannan gangami ne jagoran wannan gangami ya soke rakumi aka yi sadaka da naman duk dai domun godiya ga Allah da ya bawa Shugaban kasa Buhari lafiya ya dawo gida lafiya.
Bayan wannan gangami na jagoran masoya Buhari, a Bauchi wasu matasa sun gudanar da walima da addu'oin murnan dawowar Buhari da samun lafiyar sa a garin Bauchi.
Yau kuma an shirya wani gagaruman taron murna da nuna goyon bayan 'yan Nijeriya da dawowar Shugaba Buhari.
A wannan babban gangami na yau ya samu halartar manyan mawakan Shugaban kasa Muhammadu Buhari, wadanda suka hada da Dauda Adamu Kahutu Rarara, da wasu mawakan dama 'yan fim din Hausa da suka hada da Jamila Nagudu da Rabiu Daushe da dai sauransu.
Mawaka da 'yan fim din Hausa sama da mutum talatin ne suka samu halartar gangamin. Da 'Yan Fim Sun Gudanar Da Gangamin Murnar Dawowar Shugaba Buhari Yau A Bauchi
Daga Ahmadu Manaja Bauchi
Har yau bayan kwana goma da dawon Shugaban kasa Muhammadu Buhari, masoya da magoya baya na cigaba da gudanar da gangami dama shirya walima a garin Bauchi domin nuna godiyan su ga Allah da ya dawo da Shugaba Buhari, gida lafiya daga birnin Landan.
A makon da ya gabata Shugaban matasan jam'iyan APC, na jihar Bauchi haka kuma jagoran masoya Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a jihar Bauchi wato Alhaji Nasiru Umar Gwallaga ya jagoranci Mata da maza na garin Bauchi, inda suka gudanar da gagaruman gangamin da ya dauki hankalin Nijeriya.
Inda a wannan gangami ne jagoran wannan gangami ya soke rakumi aka yi sadaka da naman duk dai domun godiya ga Allah da ya bawa Shugaban kasa Buhari lafiya ya dawo gida lafiya.
Bayan wannan gangami na jagoran masoya Buhari, a Bauchi wasu matasa sun gudanar da walima da addu'oin murnan dawowar Buhari da samun lafiyar sa a garin Bauchi.
Yau kuma an shirya wani gagaruman taron murna da nuna goyon bayan 'yan Nijeriya da dawowar Shugaba Buhari.
A wannan babban gangami na yau ya samu halartar manyan mawakan Shugaban kasa Muhammadu Buhari, wadanda suka hada da Dauda Adamu Kahutu Rarara, da wasu mawakan dama 'yan fim din Hausa da suka hada da Jamila Nagudu da Rabiu Daushe da dai sauransu.
Mawaka da 'yan fim din Hausa sama da mutum talatin ne suka samu halartar gangamin.
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment