Tauraruwar fina-finan Hausa da turanci Rahama Sadau kenan a wadannan sabbin hotunan nata data saki inda take sannye da doguwar riga me ratsin baki-baki da fari, ta sha kwalliyar zamani ga kai babu dan kwali.
Jarumar fim din hausa, Fati Washa kenan a wannan hoton nata da tayi matukar kyau saidi kai babu dan kwali, Allah yasa ta gyara, domin kamar yanda suke cewa koya tarbiyya da wa'azi suke to ya kamata a gansu da alamar mutanen kirki.
Jarumar fina-finan Hausa, Maryam Yahaya kenan a wadannan hotunan nata da suka dauki hankalan mutane, Maryam na Sanye da yagaggen wando irin na gayu a wadannan hotunan.
Zamani me abubuwa da yawa kullun kara ganin sabbin kirkirar hanyoyin rayuwa ake gani, anan wani sabon salon dinkine na mata daya shigo gari kamar yanda ake iya gani a jikin wannan matar, dinkin dai zai nuna kafadar mace a waje.
Kamar dai yanda ya saba faruwa akai-akai:Ga wasu hotunan Maryam Gidado da suka jawo mata Allah wadai
Tauraruwar fina-finan Hausa Maryam gidado ta saba saka hotuna a yanar gizo da mutane ke ganin cewa basu dace ace tana sakawa ba, to kamar dai yanda ya saba faruwa akai-akai, yauma wasu hotunan ne na Maryam da ta saka kuma suka dauki hankulan mutane, wasu sunyyi magana.
Wani cewa yayi " ki dena daukar hoto hoto haka kina azawa a yanar gizo, ke wace irice dan Allah?"
Ga sauran abinda wasu mutane da suka bayyana ra'ayoyinsu akan wadannan hotunan na Maryam Gidado suka bayyana.
Hotunan Maryam Godado tare da 'yan uwanta da suka dauki hankula
Tauraruwar fina-finan Hausa, Maryam Gidado kenan a wadannan kyatattun hotunan nata da suka dauki hankula inda take tare da mahaifiyarta da sauran 'yan uwanta inda suka sha kwalliyar Juma'a.
Meyasa Amare ke nuna tsiraici da sunan hoton biki?
Wata baiwar Allah ce me suna khadija tayi jan hankali a shafinta na Facebook cewa wai me yasa Amare ke nuna tsiraici da sunan yin hoton biki amma bazaka taba ganin shi angon yayi shigar banza ba a hoton koda yaushe mazan zaka gansu da dogayen kaya da hula irin na al'ada.
Ta kara da cewa kuma abin ban haushi idan aka shirya liyafar cin abincin dare haka amaryar zata shigo irin wadannan kaya tsakanin yan uwanta da surukanta dda abokan mijin nata kuma har a kirata ita da angon suyi rawa kala-kala a gaban jama'ar da suka taru a gurin. Wannan dai ba addini bane kuma ba al'adar mu bace.
Ta kuma kara da cewa shin wai shi angon baya kishin matar tasfhi ne? Kuma ba cewa akayi ba zai zama sutura a gareta ba? To yaya akayi ya barta take nuna tsiraici haka? Ita kuma amaryar wa takeso ta nunawa jikinta?.
Wannan hoton na fadakarwa ne akan a yi hankali da saka kayan da suka jima a jiye ba tare da dubawaba, kamar yanda ake iya gani a hoton, ga kunama nan tayi lamo a jikin wandon inda ace da tsautsai ya saka, saidai aji wani labarin daban.
Shafin Sarauniyane ya wallafa hoton wannan wando da kiran mutane akan a rika lura.
Tauraruqar fina-finan Hausa da turanci, Rahama Sadau kenan a wannan kayataccen hoton nata da ta saka tana yiwa masoyanta barka da Sallah, tasha kyau, tubarkallah, muna mata fatan Alheri.