June 2018 - NewsHausa NewsHausa: June 2018

Pages

LATEST POSTS

Wednesday 27 June 2018

Kalli wani kambun neman sa'a da Messi ya daura a kafarshi lokacin wasasu da Najeria

Kalli wani kambun neman sa'a da Messi ya daura a kafarshi lokacin wasasu da Najeria

A lokacin wata tattaunawar da yayi da manema labari, wani dan jarida ya tambayi dan kwallon kafar Argentina Messi ko har yanzu yana sanye da wani kambun neman sa'a da ya bashi lokacin wasan Iceland? Sai messin yace Eh.

Messin ya tattare safar kafarshi inda ya nunawa dan jaridar kambun, hakan ya farune bayan kammala wasa tsakanin Argentina da Najeriya wanda ya baiwa Argentinar nasara da ci 2-1.

Dan jaridar dai ya baiwa Messi wannan kambune wanda yace na neman sa'ane kuma shima matarshi ce ta bashi.

Wani likita ya hadiyi zuciya ya mutu saboda bakin cikin cin da Argentina tawa Najeriya

Wani likita ya hadiyi zuciya ya mutu saboda bakin cikin cin da Argentina tawa Najeriya

Wani babban likita a bangaren kula da lafiyar iyali na asibitin koyarwa dake Abakaliki (FETHA) a jihar Ebonyi, Dakta Chidi Ebirim, ya fadi matacce a jiya, Talata, bayan Najeriya ta gaza samun nasarar zuwa zagaye na biyu a gasar cin kofin duniya na kwallon kafa da ake bugawa kasar Rasha.

Rahotanni sun bayyana cewar, Dakta Ebirim ya fadi ne bayan kasar Argentina ta zura wa Najeriya kwallo ta biyu a raga.

Wani shaidar gani da ido ya bayyana cewar an garzaya da kwararren likitan asibiti bayan ya fadi, amma duk da haka y ace ga garinku nan da safiyar yau, Laraba.

“Yana kallon wasan kwallon ne a gidan sa. Amma sai kawai ya yanke jiki ya fadi bayan ya yi wata kara mai karfi yayin da aka saka wa Najeriya kwallo ta biyu a raga,” a cewar shaidar.

Mutuwar kwararren likitan ta jawo tsaiko a lamuran tiyata a asibitin, saboda dukkan likitocin dake aiki a asibitin sun shiga alhini da juyayin rtashin abokin aikin nasu.

Masoya kungiyar kwallon kafa ta Najeriya (Super Eagles) sun nuna matukar fushin su a kan wasan na jiya tare da zzargin yiwa kasar makarkashiya, ta hanyar hana ta bugun daga kai sai mai tsaron raga bayan kwallo ta taba hannun dan wasan baya na kasar Argentina a da'ira mai tsaron raga.

Tuesday 26 June 2018

Wata Inyamura ta zargi Jamil M.D Abubakar, mijin Fatima Dangote da yi mata cikin shege

Wannan iyamurar me suna, Irene Chiamaka Nwachukwu na zargin cewa dan tsohon shugaban 'yansandan Najeriya, Jamil MD Abubakar kuma miji ga diyar Dangote, Fatima Dangote ya mata cikin shege kuma har ta haifeshi.

Matar tace bata da labarin cewa Jamil zaiyi aure kuma shima be gaya mata ba sai da cikinshi da take dauke dashi yakai watanni takwas, tace yanzu ta haifi jaririnta dan watanni biyu kuma yayi kama da Jamil din sosai. Tace ta bukaci Jamil din yazo ayi gwajin kwayoyin halitta dan a tabbatar da cewa danshine amma ya kiya.

Saidai wai ya biyata kudi ta tafi ta bar kasarnan da jaririn dan tayi renonshi a wata kasa can, matar 'yar shekaru 22 tace tunda ya nuna mata shi me kudine dan haka ta bukaci ya biyata miliyan dari.

Amma lauyanshi ya kiya, tace abinda jamil yace zai iya bata shine dubu arba'in duk wata ko kuma miliyan biyar daga nan karta kara nemanshi, amma tace ita taki amincewa da hakan domin miliyan biyar ko dubu arba'in duk wata babu abinda zatayi wajan kula da jaririn.

Tace ta gama hidimar daukar cikin bata yiwa Jamil maganaba dan haka bawai neman kudine yasa tace ya bata miliyan dari ba, tunda yace beson ganinta ko dan nashi to ita zata raini jaririn amma sai ya biyata kudin da tasan cewa asusun bankinta zai tumbatsa.

Ta kara da cewa yanzu lauya na biyu kenan dake kareta akan wannan lamari kuma suna mata barazana, idan bata amince da kudin da yace zai bata ba zasu kai kara kotu su kwace jaririn daga hannunta, harma sun shirya wani sako da aka aikawa matar jamil din na barazana sunce wai itace ta aikashi duk dan suyi maganinta kamar yanda sukace dan haka tace idan wani abu ya faru da ita ko jaririnta sune sila.

Kuma ta janye daga tattaunawar da suke zata tafi kotu tunda bai shirya biyanta abinda ta bukata ba.

Shugaban kasar Philippines ya zagi Allah

Shugaban kasar Philippines, Rodrigo Duterte ya fadi wasu kalaman batanci ga Allah(S.W.A), ya fadi kalamanne a bisa dalilinshi na sukar halittar Annabi Adamu da Hauwa.

Yayi wadannan kalamaine a birnin Davao kuma koda a baya ma ya taba yin irin wadannan kalamai inda yake nuna cewa be yadda da akwai Allah ba. Shugaban kasar yayi kaurin suna wajan sukar darikar katolika inda yake cewa be yadda da Allahn su ba.

Ya fada cewa, shi dai tabbas yasan akwai me gudanar da Duniyarnan amma be yadda da ko wane addini ba.

Me mafana da yawun shugaban kasar lokacin da yake kareshi yace wannan magana da shugaban kasar yayi ra'ayinshine kuma kowa na da 'yancin yi ko kuma kin yin addini asalima 'yan kasar sun san shugaban kasar akan irin wannan ra'ayi nashi shi ba me boye-boye bane tun lokacin yakin zabe ya bayyana haka.

Wannan lamari dai ya dauki hankulan mutane a ciki da wajen kasar.

Wannan kyakkyawar baiwar Allahn na tuna shekaru 7 da suka gabata lokacin da ta zama gurguwa

Wannan kyakkyawar baiwar Allahn na tuna shekaru 7 da suka gabata lokacin da ta zama gurguwa

Wannan kyakyawar baiwar Allahn da rashin lafiya ya sameta wanda yayi dalilin komawarta gurguwa, yanzu take amfani da keke guragu, ta tuna da shekaru bakwai da suka gabata, lokacin da ibtila'in ya sameta.

Tace a duk shekara idan ta tuna da wannan rana takan ji bakin ciki amma wannan karin abin zai zama na daban, ita dai wannan baiwar Allah na matukar burge mutane musamman a shafukan sada zumunta saboda karfin gwiwar ta da kuma kyan da Allah ya mata.

Wannan baiwar Allahn na neman saurayi musulmi da zai musuluntar da ita

Wannan baiwar Allahn na neman saurayi musulmi da zai musuluntar da ita

Wannan baiwar Allahn me suna Jay Teresa ta fito dandalinta na sada zumunta inda ta bayyana cewa tana neman saurayi, Musulmi kuma a shirye take ta musulunta saboda addinin yana birgeta.

Bayan data bayyana wannan aniya tata batun ya dauki hankulan mutane sosai, Teresa ta kuma fito ta gayawa masu sukarta akan wannan aniya tata da cewa su daina damunta da surutai ita fa babu abinda zai sa ta canja ra'ayinta kuma ba wanine ya sata zata musulunta ba, kawai al'adar musulunci da musulmai na birgeta ne sosai.


Sunday 24 June 2018

Kasar Lebanon ta dauke 'yan mata sanye da gajerun wanduna aikin 'yansanda dan jan hakalin turawa

Kasar Lebanon ta dauke 'yan mata sanye da gajerun wanduna aikin 'yansanda dan jan hakalin turawa

Kasar Lebanon ta fara baiwa 'yan sanda 'yan mata gajerun wanduna dan su rika jawo hankulan turawa masu yawon bude ido kasar, magajin garin Baroummana inda abin ya faru me suna pierre Achkar ya bayyan cewa wanan tsari da suka fito dashi sunyi ne dan canja tunanin kasashen yamma akan kasar.

Lamarin dai ya Jawo cece-kuce tsakanin 'yan kasar amma wasu na ganin cewa hakan ba komai bane.

Wani dan kasuwa da kafar watsa labarai ta Reuters tayi hira dashi yace yana da shago a bakin kasuwa kuma 'yan matan 'yansandan na tsayuwa a bakin shagon nashi suna aiki, shi bega aibun wannan abinba, ya kara da cewa duka matan sun san abinda suke, sun kuma kammala jami'a dan haka ba zasu yarda su yi abinda be dace ba.

Itama wata ma'ikaciyar 'yarsandan da aka yi hira da ita tace ba a tilasta mata yin aikin ba da kanta ta nema kuma tana jin dadin aikin.

Kasar Lebanon ta dauke 'yan mata sanye da gajerun wanduna aikin 'yansanda dan jan hakalin turawa

Kasar Lebanon ta dauke 'yan mata sanye da gajerun wanduna aikin 'yansanda dan jan hakalin turawa

Kasar Lebanon ta fara baiwa 'yan sanda 'yan mata gajerun wanduna dan su rika jawo hankulan turawa masu yawon bude ido kasar, magajin garin Baroummana inda abin ya faru me suna pierre Achkar ya bayyan cewa wanan tsari da suka fito dashi sunyi ne dan canja tunanin kasashen yamma akan kasar.

Lamarin dai ya Jawo cece-kuce tsakanin 'yan kasar amma wasu na ganin cewa hakan ba komai bane.

Wani dan kasuwa da kafar watsa labarai ta Reuters tayi hira dashi yace yana da shago a bakin kasuwa kuma 'yan matan 'yansandan na tsayuwa a bakin shagon nashi suna aiki, shi bega aibun wannan abinba, ya kara da cewa duka matan sun san abinda suke, sun kuma kammala jami'a dan haka ba zasu yarda su yi abinda be dace ba.

Itama wata ma'ikaciyar 'yarsandan da aka yi hira da ita tace ba a tilasta mata yin aikin ba da kanta ta nema kuma tana jin dadin aikin.

Kalli Hotunan Kafin Bikin Jarumi Ramadan Booth Tare Da Wacce Zai Aura

Kalli Hotunan Kafin Bikin Jarumi Ramadan Booth Tare Da Wacce Zai Aura


A kwanakin bayane mukaji labarin cewa tauraron fina-finan Hausa, Ramadan Booth zai angwance, to abu yazo, anan Ramadan dinne da amaryarshi suka dauki hotunan kamin biki suna cikin annashuwa.

Rahotanni sun bayyana cewa ranar 30 ga watannan za'a daura auren, amma kamin zuwan lokacin akwai shagulgula kala-kala.
Muna fatan Allah yasa ayi lafiya ya kuma basu zaman lafiya da zuri'a dayyiba.









Saturday 23 June 2018

Nafisa Abdullahi na neman wannan yaron dan ta taimakamishi


Bayan da tauraruwar fina-finan Hausa, Nafisa Abdullahi taji labarin wannan yaron dan shekaru tara da haihuwa dake aikin karfi dan ciyar da mahaifiyarshi da kuma kannenshi biyu, ta bayyan cewa tana son ta taimaka mishi.

Wata baiwar Allahce ta saka hoton yaron a dandalinta na sada zumunta na Twitter inda tace sunan Yaro Isma'il kuma shekarunshi tara, tun yana dan shekaru shidda da haihuwa mahaifinshi ya rasu wannan yasa yanzu yake aikin karfi dan ciyar da mahaifiyarshi da kuma kannenshi guda biyu.

Da Nafisa ta ga wannan labari sai ta bayyana cewa duk me labari akan yanda za'a samu wannan yaro ya aikamata da cikakken bayani ta sakon sirri dan kuwa tana so ta taimakeshi.


Muna fatan Allah ya sa a dace ita kuma Nafisa ya saka mata da Alheri.
Bala Kamala
kamalabalamlf@gmail.com

Kalli wani bature na murnar nasarar da Najeriya ta samu

Kalli wani bature na murnar nasarar da Najeriya ta samu

Wannan wani baturene sanye da rigar Super Eagles yake murnar nasarar da suka samu akan kasar Iceland a gasar cin kofin Duniya da ake yi a kasar Rasha, kwallaye biyu Najeriyar taci Iceland ta hannun Ahmad Musa.

Friday 22 June 2018

Abun al’ajabi: Wata mata ta haifi ’ya’ya 17 a sa’o’i 29

Abun al’ajabi: Wata mata ta haifi ’ya’ya 17 a sa’o’i 29

Wata mutuniyar kasar Amurka Catherine Bridges ta kafa tarihi inda ta haifi yara 17 cikin awanni 29 a asibitin Indianapolis Memorial da ke Amurka.

Dakta Jack Morrow likitan da ya karbi haihuwar matar ya ce, a lokacin da Catherine Bridges ta fara haihuwa jariran na ta fitowa daya bayan daya.

Likitan ya bayyana haihuwar tata a matsayin abin tsoro inda yace yaa dade banga irin wannan haihuwar ba a duniya.

Catherine Bridges da Maigidanta sun dade tare amma ba su samu haihuwa ba, a shekarar da ta gabata ne dai suka ziyarci wani asibiti a garin Rhodes Island don ba su shawarwari a kan yadda za su iya samun karuwa.

An samu nasara a kan shawarwarin da Likitocin asibitin suka ba ma’auratan inda suka samu ’ya’ya maza 17 a jere masu kama da juna.

An dai rada wa jariran suna masu kama da juna wadanda suka hada da: James da Jacob da Jarod da Jarbis da Jason da Jeffrey da Jeremy da Jerome da Jesse da Jimmy da Joachim da Jonathan da Jonas da Joseph da Julian da Jimbo da kuma Darth.

Saturday 9 June 2018

KARANTA WATA TAMBAYA DA AKA WA MALAM ISAH ALI PANTAMI DA TA SA YAYI KUKA YA ZUBAR DA HAWAYE

KARANTA WATA TAMBAYA DA AKA WA MALAM ISAH ALI PANTAMI DA TA SA YAYI KUKA YA ZUBAR DA HAWAYE

A tafsirin Al-Qur'ani Maigirma wanda Babban Malaminmu Ash-sheikh Dr. Isah Ali Ibrahim Pantami yake gabatarwa a darasin jiya Talata 20 ga watan Ramadan, wani bawan Allah ya rubuto takarda yake rokon Malam akan ya yiwa 'dan uwansa nasiha sakamakon bijirewa mahaifiyarsa da yayi har yace babu shi babu ita, kuma sunyi iya kokarin da zasuyi domin yaje ya baiwa mahaifiyarsa hakuri amma yaki
Da malam ya tashi gabatar masa da nasiha sai ya fara da cewa ashe har ana iya yin fada da iyaye a kaurace musu?

Babbar magana!, bil hakki ni dai tun da muka shiga Ramadan ban taba jin wata fitina da ta kai wannan girma ba ace mutum da iyayensa yayi fada har an rokeshi don ya basu hakuri amma yaki
Daga nan Malam ya kawo bayanan ayoyin Qur'ani da Hadisai na Annabi (saw) wanda suke nuni da falalar yiwa iyaye biyayya musamman mahaifiya, sannan ya kawo wata kissa wacce daga karshe sai da Malam ya fashe da kuka
Kissar itace kamar haka:

A zamanin sahabbai wani mutum ne yana neman budurwa sai ya kasheta saboda taki aurensa, sai yazo wajen Ibnu Abbas (ra) sai yace masa nayi zunubi maigirma, ban san me zanyi Allah ya gafarta min ba, ban san me zanyi ba a rayuwata na shiga damuwa
Sai Ibnu Abbas ya tambayeshi mai ya faru gareka? Sai yace wallahi budurwa nake nema taki aure na sai na kashe ta, Ibnu Abbas yace Innalillahi wa innaa ilaihi raji'un haka ka aikata? yace eh!, yanzu don Allah yaya za'ayi Allah Ya yafe min?
Tambayar farko da Ibnu Abbas ya masa shine shin mahaifiyarka tana raye? sai mutumin yace masa a'a bata raye, sai Ibnu Abbas yayi shiru, bayan tsawon lokaci sai yace to kaje kayi ta tuba kayi ayyukan alheri.

Sai daliban Ibnu Abbas sukace masa me yasa ka tambayeshi ko mahaifiyarsa na raye kuma da yace bata raye sai kayi shiru?
Sai Ibnu Abbas yace Wallahi ban san wani aiki na nagarta da mutum zaiyi ya nemi gafarar Allah Ya yafe masa ba kamar BIYAYYA ZUWA GA MAHAIFIYA, yace ban san wani aikin dake kaffara na zunnubai a duniya ba kamar biyayyan da mutum yake yiwa Mahaifiyarsa.." daga nan wajen ne sai Malam Isah Ali Pantami ya fashe da kuka har ma ya kasa cigaba da bayanin kawai sai ya umarci Alarammansa Malam Abdullahi Abba Zaria ya karanto ayoyin Qur'ani.

Ni kuma nace Malam Ya tuna da tashi mahaifiyar wacce Allah Yayiwa rasuwa watannin baya shi yasa yake kuka, ga wani kuma tashi mahaifiyar tana raye amma yayi fushi da ita (Allah Ya sauwake)
Wanda yake da bukatar karatun ya nemi tafsirin Qur'ani na ranar 20 ga watan Ramadan wanda ya gabata jiya talata
Gaskiya duk wanda Mahaifiyarshi take raye ashe yana da wata babban alfarma wanda zai iya gyara lahirarsa da ita.

Mu kyautatawa iyayenmu da suke raye domin mu gama da duniya lafiya mu kuma hadu da Allah lafiya
Allah Ka shiryar damu ka bamu ikon kyautatawa iyayenmu, wadanda suka rasa nasu iyayen Allah Ka jikansu Ka basu Aljannah don RahamarKa Amin
Sarauniya.

Wani Musulmi ya kashe kanshi a Ka'aba


Wani mutum da ba a tantance ba ya fado daga saman kololuwar Masallacin Ka'aba a Makkah a daidai lokacin da mutane ke dawafi.

Kamfanin dillacin labaran Saudiya SPA ya ambato 'yan sandan kasar na cewa nan take mutumin ya mutu bayan fadowarsa.
Sai dai ba a bayyana abin da ya yi dalilin fadowarsa ba daga kololuwar saman masallacin na Haram a Makkah ba.

"An tafi da gawarsa zuwa asibiti, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike domin gano asalinsa da kuma abin da ya haddasa fadowarsa daga sama duk da an kewaye saman da waya" kamar yadda SPA ya ruwaito.

Kamfanin dillacin labaran Saudiyar kuma ya ce ana tunanin mutumin ya kashe kansa ne domin ba wannan ne karon farko ba da hakan ta faru a Masallacin na Ka'aba, yayin da Addinin Islama ya haramta kisan kai.

Al'amarin ya faru yayin da musulmi ke azumin Ramadan, a lokacin da kuma dubban al'ummar musulmi ke gudanar da Ibadah a Masallacin mai tsarki a Makkah.
A bara wani ya yi kokarin cinna wa kansa wuta a gaban Ka'aba, kafin jami'an tsaro suka hana shi.
BBCHausa.

Thursday 7 June 2018

Wakar da mata ke rawa sanye da hijabi ta jawo cece-kuce

Wakar da mata ke rawa sanye da hijabi ta jawo cece-kuce

Wata waka da wani mawakin Najeriya me suna Falz yayi na kara daukar hankulan mutane sosai, saboda irin sa'insar da ake samu tsakanin mawakin da kungiyar kare hakkin Musulmi a Najeriya me suna MURIC, mawakin dai ya saka mata sanye da hijabi suka yi wata rawar zamani da ake kira da shaku-shaku wanda kungiyar MURIC tace hakan badalane be kamata yayi amfani da hijabiba.

Haka nan MURIC ta zargi mawakin da batawa addinin musulunci suna da sanya kiyayyarshi a zukatana mutane, inda suka bada misali da wani da aka nuna a bidiyon wakar sanye da kayan fulani da yaje yana kashe wani mutum, MURIC tace wannan bata sunane, me yasa mawakin be nuna yanda suma fulanin ake kashe su ba da shanunsu musamman a yankin jihar Benue.

A karshe dai MURIC ta baiwa mawakin kwanaki bakwai daya janye wannan waka daga kasuwa ko kuma su kaishi kotu. A martaninshi, Falz yace da gangan ya saka mata sanye da Hijabi sun rawar ta Shaku-shaku sannan kuma hakan yana nuna irin 'yan matan Najeriya da Boko Haram suka sace ne.

Ya kuma kara da cewa irin ci mishi tuwo a kwarya da lamuran Najeriya ke yi ne yasa ya shirya wannan bidiyo. A wani yanayi na goyon bayan mawakin, masu yiwa mawakin tsare-tsare sun fitar da sanarwar cewa ba zasu janye wakar ba idan MURIC ta damu ta kaisu kotu.