Wani babban likita a bangaren kula da lafiyar iyali na asibitin koyarwa dake Abakaliki (FETHA) a jihar Ebonyi, Dakta Chidi Ebirim, ya fadi matacce a jiya, Talata, bayan Najeriya ta gaza samun nasarar zuwa zagaye na biyu a gasar cin kofin duniya na kwallon kafa da ake bugawa kasar Rasha.
Rahotanni sun bayyana cewar, Dakta Ebirim ya fadi ne bayan kasar Argentina ta zura wa Najeriya kwallo ta biyu a raga.
Wani shaidar gani da ido ya bayyana cewar an garzaya da kwararren likitan asibiti bayan ya fadi, amma duk da haka y ace ga garinku nan da safiyar yau, Laraba.
“Yana kallon wasan kwallon ne a gidan sa. Amma sai kawai ya yanke jiki ya fadi bayan ya yi wata kara mai karfi yayin da aka saka wa Najeriya kwallo ta biyu a raga,” a cewar shaidar.
Mutuwar kwararren likitan ta jawo tsaiko a lamuran tiyata a asibitin, saboda dukkan likitocin dake aiki a asibitin sun shiga alhini da juyayin rtashin abokin aikin nasu.
Masoya kungiyar kwallon kafa ta Najeriya (Super Eagles) sun nuna matukar fushin su a kan wasan na jiya tare da zzargin yiwa kasar makarkashiya, ta hanyar hana ta bugun daga kai sai mai tsaron raga bayan kwallo ta taba hannun dan wasan baya na kasar Argentina a da'ira mai tsaron raga.
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment