May 2017 - NewsHausa NewsHausa: May 2017

Pages

LATEST POSTS

Wednesday 31 May 2017

Sirrin da ke tattare da cin danyen Tumatir musamman ga mai Azumi

Sirrin da ke tattare da cin danyen Tumatir musamman ga mai Azumi
Wani dalibi a jami’ar Maiduguri mai suna Jesse Tafida ya binciko wadansu hanyoyi da za a iya amfani da danyen tumatir wajen karfafa garkuwar jika da samar wa jiki lafiyar da take bukata, da kuma amfanin da ke gareshi a jikin dan Adam musamman yanzu da musulmai ke azumin watan Ramadan.
Ya ce ya gano hakan ne bayan binciken da ya gudanar akan sinadarorin da dayen tumatir ke dauke da su da mutane da yawa basu sani ba.
Tafida ya gano cewa tumatir na dauke da sunadarin da ake kira ‘Antioxidants’ a turance da ke kare mutum daga kamuwa daga wasu cututtuka sannan kuma ana samun sinadarin Vitamins A da B da kuma Folic Acid a cikinsa.
Dalibin yace cin dayen tumatir na kare mutum daga kamuwa da cutar daji, hawan jini da kuma bugawar zuciya.
Ya ce wasu binciken sun nuna cewa idan ana gauraya danyen tumatir a cikin abinci musamman cikin wasu gaiyayyakin da ake ci kamar zogale, rama da makamatansu yana rage cutar siga.
Ya kuma ce za a iya cin dayen tumatir idan cikin mutum ya murde ko kuma idan cikin mutum na ciwo sannan yana kuma rage kiba a jiki musamman ga wadanda suke bukatar haka.
Tafida ya ce cin dayen tumatir na kara karfin ido da kuma ya kare idon daga kamuwa daga wasu cututtuka kamar yanar ido, amosanin ido da makamatan su.
Daga karshe ya shawarci matan da suke dauke da juna biyu da su yawaita cin dayen tumatir lokacin da suke da ciki da kuma bayan sun haihu domin yana taimakawa wajen kare jariri daga kamuwa da cututtuka da kuma taimaka masa wajen girma.

Rahoto:premium hausa times

Tuesday 30 May 2017

Wata Magana Mai Ratsa Zuciya Da Marigayi Sheik Jafar Mahmud Adam Ya Fada Daf Da Za A Kashe Shi

Wata Magana Mai Ratsa Zuciya Da Marigayi Sheik Jafar Mahmud Adam Ya Fada Daf Da Za A Kashe Shi

"Idan kai kana ganin baka shirya ka mutuba, to idan ina karatu, ko huduba, ka daina zuwa sahun gaba, saboda idan an harbe ni, kada jini ya fallatsar maka a shaddarka da kake sawa kake ado da ita"

Hakan kuwa aka yi, domin a ranar wata Juma'a yana Limancin Sallar Asuba, wasu suka shiga sahun Sallar, kuma suka harbe shi.

Allah jikan Malam ya masa rahama. Amin.

Daga Bashir Abdullahi El-Bash

Kun san likitan da yake duba mutum 750,000 shi kadai?



An karrama likitan da yake duba mutum 750,000 shi kadai

An karrama wani likita, wanda shi kadai yake duba lafiyar mutane fiye da 750,000 domin ya rika yin aikin fida fiye da 1,000 a ko wacce shekara a kasar Sudan.

Likita Tom Catena, mai shekara 53 da haihuwa, mabiyin darikar katolika ne daga birnin New York, an karrama shi da lambar girma ta Tallafa wa Bil Adama ta Aurora.
Yayi aiki a Sudan na tsawon shekara fiye da 10, a lokacin yakin da aka fafata tsakanin gwamnati da mayaka 'yan tawaye.

A kalamansa a lokacin bikin, ya yi kira ga kasashen duniya da su taimaka a warware rikicin da ke hana samar da taimakon jin kai ga al'ummar yankin.

Dokta Catena shi ne likita daya tilo a yankin tsaunukan Nuba, inda yaki tsakanin sojojin gwamnatin shugaba Omar al-Bashir da 'yan tawayen kungiyar SPLM-Arewa ya ki ci, ya ki cinyewa.

An sha yaba masa domin kokarin da ya yi na shawo kan matsalolin rashin kayan aiki da magunguna a asibitin katolika na Mother of Mercy da ke tsaunukan Nuba, duk da aikinsa na duba wadanda suka jikkata saboda hare-haren da aka rika kai wa yankin.

"Gwamnatin Sudan da 'yan tawayen suna takaddama tsakaninsu game da wanda zai rika shigar da kayan agaji", in ji Dokta Catena.

"Dole mu yi allurar hankali."
Dokta Catena ya sanar da wadanda suka halarci bikin cewa gwamnatin kasar na son tabbatar da ikonta a kan shige da fice na kayan agajin.
"'Yan adawa na ganin akwai maganin hana haihuwa daga bangaren gwamnatin Sudan. Saboda haka suka fi son taimako daga Sudan ta Kudu mai makwabtaka da su.

Tun a shekara ta 2007 yake aiki a Sudan, inda ya rika duba masu raunuka da suka samu daga harbi. Ya rika karbar haihuwa da kuma yanke kafafuwa.

Dan wasan fim George Clooney ne ya mika wa likitan lambar yabon. "Dukkanmu muna da rawar da za mu taka domin wannan batun da ya shafi duniya. Muna da hakki a kanmu, dukkanmu", in ji Mista Clooney.
"Dole mu taimaka."
Sauran wadanda aka karrama sun hada da wani likitan hakora wanda ya yi aikin tiyatarsa ta farko lokacin yakin Siriya ta hanyar aikawa da hotunan masu bukatar aikin ga wasu kwararun likitocin da ke kasashen wajen ta hanyar shafukan zumunta.

Muhammad Darwish dan shekara 26 yana daya daga cikin likitoci uku da suka rage a garin Madaya, garin da a lokacin an yi masa kofar rago.

"Ba zan manta wannan batun ba har tsawon rayuwata", in ji shi.
"Ka zama ka sami kanka a halin da dole ka yarda wani wanda ba shi da isasshen horo ya yi tiyata a kan danka, kuma nima in yarda da hakan har in yanka cikin mutum mai rai a bisa tebur, lallai wannan lamarin bai kamata ma ya faru ba.
An yi nasara a aikin.

Ita ma Fartuun Adan wata mai rajin kare hakkin dan adam ce da ke birnin Mogadishu ta kasar Somaliya tana cikin wadanda aka karrama.

Mayaka sun kashe mijinta a shekara ta 1996 kuma tun lokacin take aikin taimaka wa kananan yaran da yakin ya rutsa da su.
Ta kafa cibiyar farko domin tallafa wa matan da aka yi wa fyade a Mogadishu.

Sai kuma Jamila Afghani daga Kabul, wacce take fafutukar ganin malaman addini sun mayar da hankulansu ga batun hakkokin mata.

"Idan ka ilmantar da mace daya, to ka ilmantar da iyali gaba daya ne. Kowa na amfana da iliminsu", in ji ta.

Shi kuma Dokta Denis Mukwege daga Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo ya taimaka wa fiye da mutane 50,000 a kan batutuwan cin zarafin jama'ai a kasar da aka lakaba wa sunan shalkwatar fyade ta duniya.

Rahoto Daga bbchausa_com

Monday 29 May 2017

Dan Kwallon Manchester United Paul Pogba Tare Da Limamin masallacin Annabi s.w.a Kalli (Hotuna).

Dan Kwallon Manchester United Paul Pogba Kenan Tare Da Limamin Masallacin Annabi (SAW) Shaykh Hudhayfee A Birnin Madinah.
To mutane sun dade suna rade raden cewa ba musulmi bane karya ce to yanzu dai Alhaji paul pogba ya nuna kanshi a matsayin musulmi a duniya.


Ya Allah wanannan bawa nakada yake dabi'u naarna Alah ka shiryesa ma'ana ina nufin wata rawa da ake kira dabb.

Addu’a A Asirce (1) Dr Muhammad Sani Umar R/Lemo

Ramadaaniyyat-Kashi Na Biyu - 2
                      Dr. Muhd Sani Umar
                       Addu’a A Asirce (1)

1. Allah (S.W.T) ya yabi Annabi Zakariyya (A.S) da cewa, ya roƙi Allah a asirce, yana mai cewa, (Lokacin da ya kira Ubangijinsa ya roƙe shi a asirce). Wannan ya nuna mahimmancin yin addu’a a asirce.


2. Yin Adda’a a asirce ita ce al’adar magabata na ƙwarai cikin wannan al’umma, Alhasan Al-Basri yana cewa, “Musulmai sun kasance masu matuƙar ƙoƙarin roƙon Allah, amma ba a jin su suna daga muryoyinsu wajen addu’a, suna yin ta ne da murya ƙasa-ƙasa, saboda Allah yana cewa, (Ku roƙi Ubangijinku cikin ƙasƙantar da kai da sussauta murya). [Al-A’raf, aya ta55”].[Ibnul Mubarak, Azzuhud, #140].


3. Allah ya yi umarni da a roƙe shi da murya ƙasa-ƙasa, kamar yadda ya gabata, domin yin haka ya fi nuna ikhalasin bawa da ƙasƙantar da kansa ga Allah.


4. Don haka yin gangamin addu’a abu ne da ba shi da madoga a cikin aikin magabata, in ban da a cikin ibadu da aka san ana yin su ne cikin jama’a, kamar addu’ar shayar da ruwa ko kusufin Rana da Wata, ko addu’ar alƙunut ko addu’ar liman a kan minbarin juma’a da makamantansu wadanda nassi ya zo da su.


Sources:darulfatawa.com

Sunday 28 May 2017

Me 'yan Nigeria ke cewa kan alƙawurran Buhari?


Yayin da Nijeriya ke cika shekara biyu a ranar Asabar da hawan Muhammadu Buhari karagar mulki, wasu 'yan ƙasar tuni sun fara yanke kauna, ganin ya cinye rabin wa'adin mulkinsa ba tare da cika wasu manyan alkawurran da ya yi ba.

Da dama dai na zargin cewa wasu mutane ƙalilan ne suka yi baba-kere a gwamnatin Muhammadu Buhari, yayin da wasu ke cewa ko a iya nan shugaban ya tsaya, ba shakka ya taka rawar-gani.

Batun taɓarɓarewar tsaro da karayar tattalin arziki da uwa-uba cin hanci da rashawa na daga cikin manyan matsalolin da suka dabaibaye Nijeriya lokacin da Buhari ya karɓi mulki ranar 29 ga watan Mayun 2015.

Shugaban dai tun lokacin yaƙin neman zabe, ya faɗa wa 'yan Nijeriya cewa ya ji ya gani, kuma zai iya, har ma ya nanata irin waɗannan alƙawarrun a yayin rantsuwar kama aiki, abin da ya ƙarfafa gwiwoyiin `yan ƙasar da dama tare da sanya ɗumbin fata.

Boko Haram

Rikicin boko-haram za a iya cewa shi ne gaba-gaba a tsakanin matsalolin tsaro da ke addabar Nijeriya, wanda ke haddasa asarar dubban rayukan jama`a, kuma Shugaba Buharin ya ɗauki matakin yankan shakku kan aniyarsa ta yaƙi da 'yan tada-ƙayar-baya.
Shugaba Buhari ya jaddada muhimmancin mai da hankali kan yaƙi da Boko Haram, inda ya mayar da shalkwatar rundunar sojin ƙasar zuwa birnin Maiduguri, inda mayaƙan suka fi karfi.

Wannan mataki da gwamnatin Muhammadu Buhari ta dauka na yin fito-na-fito da Boko Haram, kamar yadda mahukunta da ɗumbin `yan Najeriya ke cewa ya taimaka wajen karya-lagon 'yan ƙungiyar.
Dakarun sojin Nijeriya sun sake kwato yankunan ƙasar waɗanda 'yan tada-ƙayar-bayan a shiyyar arewa maso gabas suka mamaye a baya.

Sai kuma nasarar da gwamnatin ta cimma wajen ceto wasu daga cikin `yan matan sakandaren Chibok, duk da yake wasu `yan kasar na ci gaba da jayayya kan salon musayarsu da wasu kwamandojin Boko Haram.

Cin hanci da rashawa

Wani abin da ake yaba wa gwamnatin Muhammadu Buhari a kai shi ne rawar-ganin da take takawa wajen yaƙi da cin hanci da rashawa.

Wasu dai na ganin an samu nasara, don kuwa a karon farko an gurfanar da wasu manyan jami`an gwamnati da alkalai har ma da shugabannin siyasa da ake zargin sun tafka almundahana da dukiyar ƙasa a gaban kotu.

Amma wasu na zargin cewa yaƙin ya fi karkata a kan `yan adawa ko waɗanda ba sa ɗasawa da sabuwar gwamnati.
Sai dai shugaba Buhari ya ce bai kullaci kowa ba, don haka ba shi da niyyar ramuwar gayya.

Shugaban Nijeriyar ya yi yunkurin sauya tsarin kyautata rayuwar al`ummar yankin Niger-delta mai arzikin mai.

Sai dai wannan albishir na inganta rayuwar al`ummar Niger-Delta bai ratsa zukatan masu ta-da-kayar-baya ba, idan aka yi la'akari da irin luguden bama-baman da suka yi ta yi a kan bututan mai da iskar gas da ke yankin.

Hakan dai ya haddasa asara mai yawa tare da rage yawan man da Nijeriya ke fitarwa, ga kuma jefa al`ummar ƙasar a cikin matsalar ƙaranci ko rashin wutar lantarki.
Ko da yake, za a iya cewa harin ya lafa a ɗan tsakanin nan, bayan wani rangadi da muƙaddashin shugaban ƙasar Yemi Osinbajo ya kai yankin.

Samar da ayyuka musamman ga matasa

Shirin bunkasa noma da Npower da wasu makamantansu na cikin tsare-tsaren da gwamnatin Muhammadu Buhari ta bijiro da su don samar da hanyoyin dogaro da kai a tsakanin matasa.

Za a iya cewa matasa da dama sun samu tallafi, amma har yanzu akwai wasu miliyoyi da ba su da aikin yi a Nijeriya.

Yayin da gwamnatin shugaba Buhari ke lissafa irin nasarorin da ta samu wajen sauke alƙawuran ta yi wa `yan Nijeriya, wasu kuma na ganin cewa akwai wasu manyan alƙawurran da shugaba Buhari ya yi, waɗanda har yanzu ba su gani a kasa ba.

Ko da yake, mahukunta na zargin cewa harin da masu fafutukar `yanta yankin Niger-Delta ke kai wa na shafar ƙoƙarin inganta hasken lantarki.

Har ila yau, akwai masu zargin cewa shugaban ƙasar ya mai da wani ɓangare saniyar-ware ta fuskar naɗin muƙaman gwamnati, alhali yana iƙirarin cewa shi na kowa ne:

Sarkin kabilar Ibo mazauna Kano Eze Dr Boniface ya ce Buhari mutumin kirki ne shi ya sa mutane suke binsa, amma kuma inda ya gaza shi ne rashin tafiya da 'yan kabilar Ibo a gwamnatinsa.
"Laifinsa, ina gani bayan ya ci zaɓe sai ya bar 'yan kabilar Ibo a baya, bai ba su mukamai ba."
Sai dai shugaban Nijeriyar ya yi watsi da wannan zargin, inda ya ce gwamnatinsa ba ta nuna bambanci.
Yanzu dai shugaba Buhari ya cika shekara biyu a kan karagar mulki, wato ya ci rabin wa`adin mulkinsa, kuma `yan Magana kan ce juma`ar da za ta yi kyau, tun daga Laraba ake gane ta.

Ko me `yan Najeriya za su ce game da tafiyar?

Wannan ya ce: "Mun zaɓi Buhari don buƙatar zaman lafiya, gaskiya ina nan a kan bakata na son mulkin Buhari."
Shi ma wani cewa yake yi: "Buhari! Ni, ina goyon bayansa ɗari bisa ɗari, i(da)n Allah ya yarda zan sake zaɓensa''
"Gaskiya na zaɓi Buhari, amma shekara biyu ban ga wasu abubuwan ku zo ku gani ba, gaskiya yanzu na dawo daga rakiyarsa," in ji wani ɗan Nijeriyar.

Shi kuwa wannan: "Gaskiya ni ma masoyin Buhari ne amma a da, sai dai yanzu ina ganin mun samu canji ne irin na rigar mahaukaci, ya cire ta jikinsa ya ɗauko ta bola ya saka."

Mahukunta dai na cewa shekara biyu ba ta kai mizanin da za a yi kididdige tasirin mulki da ita ba, a ƙasa mai tarin matsaloli irin Nijeriya, amma masu sukar gwamnati na cewa gwamnati Muhammadu Buhari ta ƙare gudu saura zamiya, lokaci ya ƙure, don kuwa a cewarsu shekara biyun da ta rage, ta ruguntsumin siyasar babban zaɓe ce.

Rahoto:bbchausa_com

Saturday 27 May 2017

12 Simple Steps To Become A ethical Hacker

Steps to become a hacker
Hacking is an engaging field but it is surely not easy. To become a hacker one has to have an attitude and curiosity of learning and adapting new skills. You must have a deep knowledge of computer systems, programming languages, operating systems and the journey of learning goes on and on. Some people think that a hacker is always a criminal and do illegal activities but they are wrong. Actually many big companies hire hackers to protect their systems and information and are highly paid. We have prepared a list of 12 most important steps necessary to become a hacker, have a deeper look

1. Learn UNIX/LINUX

linux operating system
UNIX/LINUX is an open source operating system which provides better security to computer systems. It was first developed by AT&T in Bell labs and contributed a lot in the world of security. You should install LINUX freely available open source versions on your desktops as without learning UNIX/LINUX, it is not possible to become a hacker.


2. Code in C language 

c programming
C programming is the base of learning UNIX/LINUX as this operating system is coded in C programming which makes it the most powerful language as compared to other programming languages. C language was developed by Dennis Ritchie in late 1970’s. To become a hacker you should master C language.

3. Learn to code in more than one Programming Language

programming languages

It is important for a person in the hacking field to learn more than one programming. There are many programming languages to learn such as Python, JAVA, C++. Free eBooks, tutorials are easily available online.

4. Learn Networking Concepts

computer networking
Another important and essential step to become a hacker is to be good at networking concepts and understanding how the networks are created. You need to know the differences between different types of networks and must have a clear understanding of TCP/IP and UDP to exploit vulnerabilities (loop holes) in system.
Understanding what LAN, WAN, VPN, Firewall is also important.
You must have a clear understanding and use of network tools such as Wireshark, NMAP for packet analyzing, network scanning etc.

5. Learn More Than One Operating Systems 

operating system
It is essential for a hacker to learn more than one operating system. There are many other Operating systems apart from Windows, UNIX/LINUX etc. Every system has a loop hole, hacker needs it to exploit it.

6. Learn Cryptography

cryptography encryption
To become a successful hacker you need to master the art of cryptography. Encryption and Decryption are important skills in hacking. Encryption is widely done in several aspects of information system security in authentication, confidentiality and integrity of data. Information on a network is in encrypted form such as passwords. While hacking a system, these encrypted codes needs to be broken, which is called decryption.

7. Learn more and more about hacking

hacking or hackers
Go through various tutorials, eBooks written by experts in the field of hacking. In the field of hacking, learning is never ending because security changes every day with new updates in systems.

8. Experiment A Lot

experiment
After learning some concepts, sit and practice them. Setup your own lab for experimental purpose. You need a good computer system to start with as some tools may require powerful processor, RAM etc. Keep on Testing and learning until you breach a system.

9. Write Vulnerability (Loop hole program)

hacking vulnerability

Vulnerability is the weakness, loop hole or open door through which you enter the system. Look for vulnerabilities by scanning the system, network etc. Try to write your own and exploit the system.


10. Contribute To Open Source Security Projects

open source software
An open source computer security project helps you a lot in polishing and testing your hacking skills. It’s not a piece of cake to get it done. Some organizations such as MOZILLA, APACHE offer open source projects. Contribute and be a part of them even if your contribution is small, it will add a big value to your field.

11. Continue never ending Learning 

learning hacking
Learning is the key to success in the world of hacking. Continuous learning and practicing will make you the best hacker. Keep yourself updated about security changes and learn about new ways to exploit systems

12. Join Discussions and meet hackers 

discussion
Most important for a hacker is to make a community or join forums, discussions with other hackers worldwide, so that they can exchange and share their knowledge and work as a team. Join Facebook groups related to hacking where you can get more from experts.

[Audio] Sabuwar wakar Rarara Mallam Ya Hadiye Bakan Gizo 2017

Saukar da wakar rarara mai taken malam ya hadiye bakan gizo 2017.

wanannan waka dai yayi ta ne ga Gwanta el-rufai domin samun nasarorin da ake samu a gwamnatinsa a cikin jaharsa kaduna.

Wakar tayi dadi sosai ga baitutin wakar kadan daga ciki kamar haka:


ku bani kidan mallam babban bakan gizo.

farin wata ruwa ya zo birni da kauyuka.

Mallam ya hadiye bakan gizo ruwa ya zo birni da kauyuka.

Ruwa baba !Ruwa baba !! Ruwa baba!!!



Domin saukar da wanannan waka sai ka latsa blue rubutu.


 Download Audio Now

Friday 26 May 2017

Dan shekara 18 ya yi wa kanwar shi mai shekaru 8 fyade a Katsina

r
- An gurfanar da wani matashi mai shekaru 18 a kotu a bisa aikata laifin fyade

- An rahoto cewa yayi ma kanwar sa mai shekaru 8 a duniya fyade

An gurfanar da wani matashi mai shekaru 18 a kotu a bisa aikata laifin yi wa kanwar shi mai shekaru 8 fyade.

Wannan mummunan lamari dai ya faru ne a rukunin gidaje na ‘Steel Rolling Mills’ da ke kan titin Dutsinma a jahar Katsina.

Alkalin Kotun, mai shari’a Hajiya Falile Dikko ta bayar da umarnin a tsare matashin a gidan maza har zuwa ranar 29 ga watan Yuni yayin da za a saurari karar.

‘Yan sanda sun bayyana wa kotun yadda matashin ya yaudari kanwar ta shi zuwa cikin bandaki, inda ya aikata aika aikar akan ta da karfin tuwa.

Tuni aka kai yarinyar asibiti inda aka duba lafiyar ta tare da yi mata magani.

©naij.com

Man United: Jose Mourinho na san sayo 'yan wasa uku ko hudu


Jose Mourinho ya bayyana wa mataimakin shugaban hukumar gudanarwar kungiyar aniyarsa

Man Utd na son takaita kashe kudinta wajen sayen manyan 'yan wasa uku ko hudu, da ake ganin za su yadda  da Griezman da Michael Keane.

United za ta buga gasar Zakarun Turai ta badi, kuma koci Jose Mourinho ya ce mataimakin shugaban gudanarwar kungiyar Ed Woodward na sane da wannan aniya tasa "sama da wata biyu da suka gabata"
Mourinho na son kara karfafa 'yan wasan gaban kungiyar tare da 'yan wasan baya, saboda fuskantar kalubalen gasar Premier a kaka mai zuwa.


Ana dai alakanta kungiyar da son daukar dan wasan gaba na Atletico Madrid, Antoine Griezmann, da kuma dan wasan baya na Burnley Michael Keane.

Kocin dan Portugal wanda ya bayyana haka ranar Laraba, bayan da kungiyar ta dauki kofin Zakarun Turai na Europa ya ce "Ed Woodward na sane aniyata."
Ya kara da cewa "yanzu ya rage nasa da kuma masu kungiyar".

Burin Mourinho

Griezmann, dan wasan Faransan mai shekara 26 da ke da farashin euro miliyan 100 a kwantiraginsa, ya fada a farkon makon nan cewa, damar da yake da ita ta zuwa United kashi "shida ce cikin goma"
Samun gurbin zuwa gasar Zakarun Turai zai bai wa kungiyar kwarin gwiwar nemansa kai tsaye.

Griezmann dai na da gudu da kuma waskiya abin da United ta rasa, amma idan hakan bai samu ba, to kungiyar ka iya koma wa ga dan wasan gaba na Torino Andrea Belotti dan asalin Italiya wanda ya ci kwallo 25 a gasar Serie A ta bana.


Griezmann ya ci wa Faransa kwallo 15 a wasa 41 da ya yi mata


Keaneya bar United zuwa Burnley a watabn Janairun 2015, amma yanzu Mourinho ya zaku ya dawo da dan wasan bayan mai shekara 24 zuwa Old Trafford.
A ka'ida kashi 25 cikin dari na yarjejeniyar da aka amince da ita a baya za a rage.

To sai dai Kocin Burnley Sean Dyche ya ce kungiyar ba ta da matsalar kudin da zai sa ta sayar da Keane, wanda ya fara bugawa kasar Ingila kwallo a watan Maris.

Rahoto :bbchausa_com

Thursday 25 May 2017

Tsotson farjin Mace Yayin Saduwa!!! Dr Jamilu Yusuf Zarewa

Tsotson Farjin Mace Yayin Saduwa !!!

Tambaya :
Assalamu alaikum, M. Na kasance ina tsotsan azzakarin mijina, shi kuma yana wasa da gabana da harshensa kafin mu sadu, ina matsayin haka a addinin musulunci.

Amsa :

To 'yar'uwa hakan ya halatta, ba matsala a sharian ce, saboda an rawaito halaccin haka, daga magabata, daga cikinsu akwai Imamu Malik, saidai ya wajaba a tabbatar an tsaftace wurin musamman farjin mata, saboda a bude yake, sannan kuma wuri ne da ake yin haila, ake kuma zuba maniyyi, ga shi kuma yana kusa da wajan yin bahaya, wasu masana likitanci suna bada shawarar cewa : 

a dinga wanke wurin da gishiri kafin a tsotsa, saboda neman kariya
Allah madaukakin sarki a cikin suratul Bakara aya ta : 223, ya kwatanta mace ga mijinta da gona, wannan sai ya nuna dukkan bangarorin jikinta ya halatta a ji dadi da su, in ban da cikin dubura wacce nassi ya togace.

Allah ne mafi sani.

Duba : Mawahibul-jalil sharhin Muktasarul Khalil 3\406

©www.Darulfatawa.com

Sheikh Ja'afar barka da zuwa

SHEIKH JAAFAR BARKA DA ZUWA

Jiya Allah ya Azurta Sheikh Dr. Ibrahim Abdullahi Rijiyar Lemo da Iyalinsa Zainab Jafar Mahmud samun karuwar d'a Namiji wanda suka sanyawa suna Jaafar. Mai jego da jaririnta suna nan cikin koshin lafiya.

Muna yiwa babban bako Sheikh Jaafar barka da zuwa, muna masa adduar fatan alheri da fatan Allah ya raya shi, Allah ya sa ya gaji kakansa Sheikh Jaafar Mahmud Adama wajen neman ilimi da yada shi.

Allah ya raya mana Sheikh Jaafar Ibn Ibrahim.

25-05-2017

Sources:sadeeqmedia.com.ng

Wednesday 24 May 2017

[video] Download video Umar M Shareef Show in kano 2017

Download video Umar M Shareef Show in Kano 2017

Download video mp4 now

Mai Babur Dauke Da Man Fetir Ya Jawo Silar Babbakewar Mutane Tara A Yankin Dakatsalle Dake Jihar Kano A Cikin (hotuna)

Mai Babur Dauke Da Man Fetir Ya Jawo Silar Babbakewar Mutane Tara A Yankin Dakatsalle Dake Jihar Kano A Cikin (hotuna)

Wani mai babur dauke da man fetur ya yi sanadiyar konewar wasu mutane tara a yankin Dakatsalle dake karamar hukumar Bebeji a jihar Kano. Inda mutane shida suka kone kurmus, yayin da ragowar guda ukun suke cikin halin rai-kwakwai-mutu'kwakwai a asibiti.

Lamarin wanda ya auku da ranar yau, mai babur din wanda yake dauke da jarkokin man fetur guda biyu, ya bugi wata mota ce a yayin da direbanta ke daukar fasinja a bakin hanya.

Shi dai mai babur din ya yi kokarin kaucewa wata mota ne da ta so ta buge shi, wanda a dalilin haka jarkokin da suke dauke da fetir din suka fashe a kusa da wani mai shayi har ta kai ga fetir din ya kama da wuta, ita ma motar ta kama da wuta dauke da fasinjojin dake cikinta.

Kalli Hotunan Hadarin da abu ya afku Allah ya jikansu da rahama






 Allah Ya jikansu da Rahama ,Allah ya tsare gaba

Rahoto:Rariya

Tuesday 23 May 2017

Sokoto State govt to sell houses to civil servants

Sokoto State govt to sell houses to civil servants

The Sokoto State government says it will sell its houses to civil servants occupying them on owner-occupier basis.


Alhaji Bello Gwiwa, the Commissioner for Lands, Housing and Survey, disclosed this in Sokoto on Sunday, at a ministerial press briefing to mark Gov. Aminu Tambuwal’s second year in office.


He listed houses to be sold to include those at the parliamentary quarters, Yauri flats, Runjin Sambo housing estate, Arkilla quarters, Gwiwe intermediate housing estate and G-quarters.


Others included the government houses behind UBA quarters, temporary site quarters, among others.


“The governor has already set up a committee to ascertain the houses involved, assess their costs and recommend the prices and modalities for payment.


“As the commissioner in the housing ministry and head of the committee, I can tell you that we have completed our assignment and will submit the report this week,” he said.


The official said that the gesture would minimise accommodation problems faced by the workers, adding that 1000 additional houses were being constructed at Gidan-Man Ada and Gidan Solanke.


“When the 1000 houses are completed, they will equally be sold to the workers,” he said.


Gwiwa said that 500 houses, recently inaugurated by President Muhammadu Buhari, would soon be sold to the workers on owner-occupier basis, and promised to be fair to all in the housing sales exercise.


He said that government was also concerned about the rising congestion in Sokoto metropolis and had resolved to relocate auto mechanics to various mechanic villages.


The commissioner said that nine new cemeteries were being established in Sokoto city and environs to address the shortage of burial grounds in the affected areas.

Kalli kyawawan Hotunan Sabuwar Jarumar Kannywood Aysher Sarki

Wanannan dai wata sabuwar jaruma ce a kannywood wato a masana'antar hausa film ce mai suna Aysher sarki wadda akwae fina finai da zata haska nan gaba kadan.Ga hotuna kamar haka




 kalli ka gani wanannan sabuwar jaruma aysher sarki

 wato wanannan jaruma mundade abokai da ita amma ba gane 'yar wasan hausa film bace sai jiya naga tana zaune tana karanta wani script na hausa film

®www.hausaloaded.com

Tun bayan komawar shugaba Muhammadu buhari birnin london a ranar lahadi 07/05/2017, har zuwa wannan rana Hoto guda dayane kawai aka saki wanda ke nuna shugaban a birnin london.



Kamar yadda labari yake zuwa mana jikin Baba Buhari yana kara yin sauki Alhamdulillah. .....

Hotuna masu yawa suna yawo akan dandalin sadarwar zamani na Facebook da twitter wadanda ake cewa Baba ne tare da likita ko wasu mutane na daban.... 

Maganar gaskiya dukkan hotunan da ake sakawa ba sabbin hotuna bane,  wannan guda dayan shi kadaine kawqi wanda aka saki amma dai jikin baba yana kara ingantuwa Alhamdulillah. ......

Soyayya da damuwar da ake da ita akan shugaba buhari hakan ne ke sanyawa al,umma su dinga yadda da hotunan, kuma hakan ne ke sanyawa jaridun karya da marubatan karya suke amfani da damar wajen yawo da hankalin masoya baba......

SHAWARA.....

A matsayinka na masoyin shugaba Muhammadu buhari idan har kana bukatar samun ingantatten hoto ko labari akan shugaba buhari to zaifi kyau ka dinga ziyartar Shafin masu temaka masa a hanyar sadarwa irin su Garba Shehu, Femi Adesina, da kuma Bashir Ahmad anan ne kawai zaku samu labarin mai inganci......

Haka akwai marubutan Baba Buhari masu zaman kansu irin su Buhari Sallau, Biyora da sauransu wadanda tabbas in har kaga sun saka hoto ko labari akan Shugaba buhari to in sha Allah gaskiya ne..........

Masoya Baba Addua zamu cigaba da gudanarwa kamar yadda muka saba.... Baba zai dawo in sha Allah nan ba dadewa ba.........

Sources:Rabiu biyora

[MUSIC] sabuwar waka Daga Best of Mansoor By Fantimoti song

Saukar da wakar fatimoti daga ablum na mansoor idae mutane sun fahimci wani abu kadan shine a cikin banner  an nuna lyrics harda fatimoti to nasan wani zai ce ae batayi waka a cikin mansoor ba daga Umar m Shareef sai Abdul D One da kuma Muhammad maleri ne kawae nayi waka a ciki to yanxu dae ga wakar nan.
wanannan waka itama taken "mansoor" ne abun dai sai kaji da kunnenka.

     Download music here

Matashin yaro daga Adamawa ya ci 308 a jarrabawar JAMB ta 2017 (DUBA)


- Wani matsahin yaro daga jihar Adamawa ya ci maki 308 a jarrabawar shiga jami’a

- Bashar Umar Shagari, wani mai amfani da shafin zumunta, ya buga a shafin Facebook don ya taya yaron mai kwazo murna

Wani matsahin yaro daga jihar Adamawa, Abdulrahman Ali ya ci maki 308 a jarrabawar shiga jami’a wato Joint Admission Matriculation Board (JAMB) wanda aka kammala kwanan nan.

Wani mai amfani da shafin zumunta, Bashar Umar Shagari ya buga a shafin Facebook don ya taya yaron mai kwazo murna, tare da taken:
Hazikin yaron da ya ci 308 a JAMB daga Adamawa



Hazikin yaron da ya ci 308 a JAMB daga Adamawa

“Dole Gwamna Bindow ya ga wannan sannan kuma na jinjina ma gwarzon shekara. Abdulrahman Ali daga jihar Adamawa, wanda ya ci 308 a jarrabawar JAMB 2017, ina taya ka murna yaro, ina ma ace na kai ga cin wannan maki a lokacin da na rubuta nawa jarrabawar.”

©Naij.com