Musulmin da ke hana a yanka shanu a Indiya - NewsHausa NewsHausa: Musulmin da ke hana a yanka shanu a Indiya

Pages

LATEST POSTS

Wednesday 10 May 2017

Musulmin da ke hana a yanka shanu a Indiya


Ranar Talata ce ranar da 'yan kabilar Hindu da dama ke girmamawa sai muka nufi wani sanannen wurin bauta a cikin rana mai zafi.

Sai muka nufi wani garken shanu da ke wani daki a kasan wurin bautar.

Dildar Hussain Beg ya shaida min cewa yana kai ziyara wurin bautar duk ranar Talata bayan ya yi sallah a wani masallaci da ke kusa da wurin domin ya kula da shanu sama da 20.

"Na shafe sama da shekara 10 ina zuwa nan kuma wadannan shanun sun zama tamkar dangina. Ina kuma kai wa wasu shanun da ke wasu garken ziyara a kai- a kai," a cewarsa.

Amma Mista Beg ba wai kawai kai wa shanun ziyara yake yi ba, yana kuma kare su.

Tare da wasu makotansa, Mista Beg ya hada wata kungiya da ake kira kungiyar Gauraksha Dal ta Muslumai, wato (kungiyar da ke kare shanu) kuma yana kokarin ilmantar da alumma su daina cin naman shanu.

"Masu kare shanu a Indiya na jan hankulan kafafen yada labarai saboda harin da suke kai wa mutane masu daukan shanu zuwa wasu wuraren.

Ana kai hare-hare da dama kan Musulmai, yayin da akasarin kungiyar kare shanun 'yan kabilar Hindu ne.

Hindu ta dauki shanu a matsayin abu mai tsarki kuma haramun ne kisansu a jihohi da dama a kasar. Amma kuma ana cin naman shanu a wasu al'ummomin wadanda suka hada da na Musulmai a Indiyan.

Mista Beg na cikin kungiyar Musulmai da ke da garken kula da shanu. A baya ma wasu al'ummomin Musulman sun kula da shanu mallakin kabilar Hindu.
Ya ce, "A na zargin al'ummarmu da yawan yanka shanu a Indiya. Idan har Musulmai ba su fito sun hana yankan shanu ba, wa zai hana?"
Ya kara da cewa bayan ma yawan aikin da ke wannan garken shanun, yana saka ni yawan bulaguro zuwa wasu sassa daban-daban na kasar, domin "wayar da kan al'ummarsa a kan yanka shanu da kuma kawar da al'adar cin naman shanu."
Ya kara da cewa ya yi taro a sansanonin da ke tsakiyar jihar Madhya Pradesh da ke Indiya, domin wayar da kan jama'a kuma kamar wasu kungiyoyin kare shanun na kabilar Hindu, Mista Beg ya yi ikrarin cewa ya shaida wa 'yan sanda safarar shanu ba bisa ka'ida ba zuwa ciki da ma wajen Delhi, babban birnin Indiya.

'Ba don na yi suna na ke yi ba'

Ya musanta cewa ba don ya yi suna yake yin abin da yake yi ba.
"Ba na goyon bayan ko wacce jam'iyyar siyasa kuma na yi yakin neman zaben majalisa a matsayina na dan takara mai zaman kansa a zaben da ya gabata.

"Da farko 'yan al'ummata na zolayata idan na roke su su daina cin naman shanu amma ba mu damu ba," a cewarsa.
Iyalinsa suna goyon bayan manufarsa. Matar Mista Beg, Shaheen Begum, ta ce da fari, na yi mamaki da ya yanke shawarar zama mai kare shanu.

Ta ce, "Ina ga ni ban dauki wani tsawon lokaci ba kafin na goyi bayan manufarsa saboda dama can ni ba ma'abociyar cin naman shanu ba ce, a ko da yaushe na fi so na ci naman kaza ko kifi".
Sai dai ra'ayoyin 'yan uwa sun sha ban-ban.
"Akasarin mutanen da muke hulda da su ba sa cin naman shanu. Da farko mutane kadan suna tambayar dalilin da yasa yake zuwa ganawar masu kare shanu. Amma a yanzu babu mai yin wannan tambayar," a cewar ta.
"Wasu na ganin cewa yana yi ne kawai don ya yi suna amma kuma su kan sauya ra'ayi idan suka ji cewa yana bai wa mutane shawarar su ci naman rago ko na bauna maimakon na saniya saboda sun fi lafiya."

Tashen da bashi da amfani

Indiya na fuskantar karuwar kungiyoyin 'yan kato da gora masu kare shanu, kuma an fi samun hakan bayan da jam'iyyar 'yan kabilar Hindu ta Nationalist BJP ta karbi mulki a shekarar 2014.
A shekarar 2015, wata kungiya ta kashe wani Musulmi da aka yi zargi da ajiye tare da cin naman shanu. Akwai rahotonnin hare-hare kan masu safarar shanu a kalla 12 a sassan kasar.

Jam'iyyun 'yan adawa na suka, inda suke so su shawo kan Firai ministan Narendra Modi ya soki kungiyoyin, inda suke cewa suna ba shi "haushi".

Sai dai wanan yunkurin bai yi wani tasiri a kasar ba.

A baya-bayan nan, an yi wa wata kungiyar manoma Musulmai duka a kan wani babban titi, da aka yi zargin masu kare shanu ne suka yi musu saboda suna safarar shanu daga wurin baje-kolinsu. Daya daga cikin wadanda abin ya ritsa da su, wani tsoho mai shekara 50 ya mutu a asibiti daga baya.

A wani rahoto na baya-bayan nan da kungiyar kare hakkin bil adama ta fitar, ta bukaci a dauki mataki kan wadanda ke da hannu kan irin hare-haren.

Amma Mista Bet ya yi amannar Musulmai ma za su iya hana lamarin ya yi kamari.
"Abu ne mai sauki. Idan akasarin al'ummomin kasata da dama ba su amince da cin naman shanu ba, me ya sa za a ci gaba da yi?"

"Bani da wata matsala da Musulmai masu cin naman bauna kuma ina karfafa musu gwiwar da su ci gaba. Sai dai mu al'umma ne marasa rinjaye kuma dole ne mu sassuatawa kabilar Hindu wadanda sune masu rinjaye.

" Idan har suna daukar shanu a matsayin wani abu mai tsarki, me ya sa zamu rika kashe su?

Rahoto:bbchausa

Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment