BIO: Umar M Sheriff Tsoron Budurwa yasa na zama mawaki - NewsHausa NewsHausa: BIO: Umar M Sheriff Tsoron Budurwa yasa na zama mawaki

Pages

LATEST POSTS

Thursday 4 May 2017

BIO: Umar M Sheriff Tsoron Budurwa yasa na zama mawaki



Umar Muhammad Sharif fitaccen mawakin
fina-finan Hausa ne, a hirar da ya yi da
Aminiya a ranar Lahadin da ta gabata ya
bayyana yadda ya fara waka da irin nasarorin
da ya samu da kuma wasu daga cikin
kalubalen da ya fuskanta:
Tarihina a takaice
Assalamu alaikum, sunana Umar
Muhammad Sharif,
an haife ni a Rigasa da ke Jihar Kaduna a
shekarar 1987. Na yi makarantar firamare
da sakandare duk a Rigasa.
Dalilin da ya sa na zabi sana’ar waka
Waka ta fado mini kwatsam da rana tsaka ne,
amma a gaskiya ban taba tunanin zan yi
sana’ar waka ba, saboda tun tasowata ni dalibi
ne, ina karatun boko da na addini, na ma fi ba
da karfi a bangaren addini. Silar fara waka
kuwa ita ce akwai wata budurwa da nake
matukar so da kauna, amma na kasa sanar da
ita abin da ke zuciyata. A gaskiya jin nauyin
abin shi ne ya hana ni sanar da ita. Nakan je
har kofar gidansu, na aika a yi mini sallama da
ita, amma inda gizo ke sakar shi ne da zarar ta
fito don ganin wanda ke neman ta, sai na buya,
ta gama dube-dubenta daga nan idan ba ta ga
kowa ba sai ta koma gida. To na yi hakan
kusan har sau uku ba tare da samun damar
tsayawa da ita ba. Daga nan wata rana sai na
yi ta maza na ce zan ga abin da zai ture wa
buzu nadi. Da na je sai na aika kamar yadda
na saba amma sai a wannan karon ba ta fito
ba. Na yi ta jira amma shiru kake ji. To daga
nan ne fa kamar wasa sai na fara yin waka a
kan halin da na samu kaina ciki. Daga kofar
gidansu na fara waka har na isa gida ban
daina ba. Haka na yi tayi duk lokacin na tuna
da wannan baiwar Allah.
A cikin wannan halin ne sai na samu biro da
takarda na rubuta wakar. Akwai wani mawaki
Ibrahim Suleiman (Zaki) wanda ya kasance
abokin yayana ne. Kamar wasa da ya ga
wakar kuma ya umarce na rera ta. Bayan ya
saurari wakar sai ya yaba kuma ya yi min wasu
gyararraki, kana ya karantar da ni kabli da
ba’adin waka. Daga nan ne fa na fara waka
gadan-gadan.
kalubale
Da farko na fuskanci kalubale daga gida, daga
bisani muka fahimtar da iyayenmu. Bayan ba
su ga canji daga irin tarbiyyar da suka yi mana
ba, sai suka fara sa mana albarka da fatan
alheri. Shakka babu addu’o’insu na tasirin
sosai a kan nasarorin da muke ci gaba da
samu.
Wakokin da na yi
A kalla wakokina za su kai 500
Kundin waka
Akwai su kamar haka: ‘Duniya Ce’ da ‘Nadiya’
da ‘Shahuda’ da ‘Madubi da ‘Mai Atamfa’ da
kuma ‘Babbar Yarinya’
Bakandamiyata
Duka wakokina.
Fitowa a fim
Ina fitowa a fim, sannan nakan shirya nawa.
Fina-finan da na fito sun hada da:
‘Mahaifiyata’ da ‘Nas’. Fina-finan da na shirya
sun hada da: ‘Ba Zan Barki Ba’ ’Ka So A So ka’
da ’Jinin Jikina ’
Burina
 Ba ni da wani burina saboda ko yanzu kasuwa
ta watse dan koli ya ci riba. Sunana ya kai duk
inda ba ka zato, saboda na sha samun kira ta
waya daga Amurka da sauran kasashen
duniya, wanda jama’a ne masu sauraren
wakokinmu ke yaba mana.
Iyali
Ina da mata daya Maryam da da daya ana
kiransa Aliyu.​


Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment