Tsohon dan wasan Wales Robbie Savage, ya ce Wayne Rooney na Manchester United shi ne da a tarihi aka fi rashin darrajawa a Ingila.
Rooney dai, shi ne dan wasan da ya fi yawan cin kwallo a Manchester United da Ingila.
Sai dai kuma dan wasan mai shekara 31, wasa 22 kadai aka fara da shi a wannan kaka, kuma ya nuna alamun zai bar kungiyar domin ya je inda za a rinka sanya shi wasa a kai a kai.
A wata hira da BBC Savage ya ce: " Duk da muzgunawar da dan wasan ke sha, bai bari hakan ya dame shi ba, yadda ya kasance kan gaba wajen ci wa United da Ingila kwallo.''
Ya ce : "kwararren dan wasa ne, yana da kyakkyawar dabi'a, halayyarsa ba ta saba wa yadda yake ba.
Idan an yi masa hukuncin da bai masa dadi ba, yakan nuna bacin ransa. Yana nan dai yadda yake bai sauya ba.''
Tsohon dan wasan na Wales ya ce, ''kai a takaice dai yawan shekaru, da kuma rashin sanya shi wasa a kai a kai, su ne ke damun dan wasan.
Yanzu ba kamar da yake ba. Amma kuma shi ne dan wasa da aka fi rashin darrajawa a Ingila.
Rooney, ya shafe shekara 13 a United, tun bayan da ya koma kungiyar daga Everton a kan kudi fam miliyan 27, a watan Agustan 2004.
Ya samu nasarar daukar kofin Premier sau biyar, da kofin Zakarun Turai daya, da kofin kalubale na FA daya, da kofin lig uku, da kuma kofin duniya na kungiyoyi a tsawon zamansa a Old Trafford.
A wannan kakar ne ya zarce tsohon dan wasan kungiyar, Bobby Charlton, yawan kwallo da aka zura a raga, inda yanzu yake da 252 da ya ci mata.
Ya kuma zarce Charlon yawan kwallo da ya ci wa Ingila, inda ya ci wa kasar kwallo 53 a wasa 119 da ya yi mata.
Ranar Laraba ne, ya yi magana a kan makomarsa, inda ya ce: "Anya zan tsaya? Na shafe shekara 13 a kungiyarnan. Hakika ni fa ina son ganin ana sa ni a wasa."
Ana ci gaba da alakanta dan wasan da komawa China, yayin da Everton da Amurka ke ganin wata dama ce, da za su samu ta daukar dan wasan.
United din dai, za ta kara da Celta Vigo ranar Alhamis a wasan kusa da karshe na kofin Zakarun Turai na Europa, a karawa ta biyu.
Kungiyar dai ta samu nasara a kan Celta Vigo da ci 1-0 a wasan farko da suka kara a kasar Spaniya.
Rahoto :Bbchausa
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment