Wane ne Shugaba Muhammadu Buhari na Nigeria? - NewsHausa NewsHausa: Wane ne Shugaba Muhammadu Buhari na Nigeria?

Pages

LATEST POSTS

Friday, 5 May 2017

Wane ne Shugaba Muhammadu Buhari na Nigeria?


Tsohon shugaban mulkin soja na Najeriya Muhammadu Buhari mai shekara 72 - mutum ne da ake ganinsa a matsayin tsayayye wanda ba ya gudu ba ja da baya.
Duk da shan kaye da ya yi a zabuka uku da suka gabata, amma ya sami nasara a zaben 28 ga watan Maris, inda ya zama dan adawa na farko da ya sami galaba a kan shugaban da ke kan karagar mulki.

Buhari ya kara da shugaba Goodluck Jonathan, wanda dan yankin Neja Delta ne, a karo na biyu da gudanar da zaben.
A wannan karon ya yi sa'ar samun goyon bayan gamayyar jam'iyyun siyasar Najeriya mai suna All Progressives Congress (watau APC).

Jam'iyyar APC ta sami karin karfi bayan da manyan 'yan siyasa daga jam'iyyar shugaba Jonathan ta People's Democratic Party (watau PDP) suka sauya sheka, jam'iyyar ta PDP ce ta mamaye fagen siyasar Najeriya tun karshen mulkin soji a shekarun 1999.

'Yunkurin kisa'


Buhari mutum ne mai farin jini a wajen marasa galihu da ke yankin arewacin kasar.

A yanzu wasu na ganin cewa zaman Buhari tsohon janar na soja, kana sanin halinsa na bin doka da oda zai ba kasar damar fuskantar kalubalen ta'adancin masu kaifin kishin Islama da suka mamaye yankin arewa maso gabashin kasar.
Shi dai Musulmi ne daga Daura a jihar Katsina, kuma tuni ya bayar da goyon bayansa ga tsarin aiwatar da shari'a a arewa, wanda ya sanya a baya dole ya fito yana kare kansa daga zargin da ake masa na cewa shi mai tsatsaurin ra'ayin addini ne.
Hakan ya yi masa illa a lokacin zaben shekarar 2003 - lokacin da ya kasa samun goyon bayan al'ummomin kirista da ke kudancin kasar.

Amma bayan da ya tsallake rijiya da baya a lokacin da aka kai hari kan jerin motocin da ke masa rakiya a Kaduna, harin da ya yi kama da irin wanda kungiyar Boko Haram take kai wa na kisan wadanda ke adawa da ita, Buhari ya yi alkawarin kawo karshen ta'addanci cikin watanni idan aka zabe shi.

Ya alakanta rashin karfin halin shugaba Jonathan a dalilin da ya jawo tabarbarewar al'amarin, da kuma kin yarda da kiraye-kirayen da ake masa na ya hau teburin tattaunawa da kungiyar.

Har yanzu ana tuna shi da matakan da ya dauka a lokacin yana kwamandan sojin Najeriya a shekarar 1983 - lokacin da wasu sojiojin Chadi suka kwace wasu tsibirai mallakin Najeriya - a yankin arewa-maso-gabas, yankin da sojojin kasar ke rike da shi bayan da ya fatattaki masu harin.


"Yaki Da Rashin Da'a"


Ya mulki Najeriya daga watan Janairu na 1984 har watan Agusta na 1985, bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Disamba na 1983.

Wannan lokaci ne da ake tunawa da shi don tsananin aiwatar da yaki da rashin da'a da kuma karya hakkokin dan adam da gwamnatinsa ta yi.
Bayani kan Shugaba Muhammadu Buhari a takaice:


  • Shekararsa 72
  • An zabe shi a matsayin shugaban kasa a zaben 28 ga Maris 2015
  • Ya yi shugaban mulkin sojan Najeriya daga 1984 zuwa 1985
  • An hambare shi a juyin mulki
  • Ya samu shaidar rashin kare hakkin dan adam
  • An yi amanna ba shi da cin hanci da rashawa
  • Mai ladabtarwa ne - a kan sa ma'aikatan gwamnati tsallen kwado idan suka yi lattin zuwa aiki
  • Musulmi ne daga arewacin Najeriya
  • Ya tsallake rijiya da baya a wani hari da Boko Haram ta kai masa
Akwai bambamcin ra'ayi game da tasirin mulkin sojin Buhari na watanni 20 da ya yi.
Kimanin 'yan siyasa 500 da ma'aikata da 'yan kasuwa ne aka tsare a kurkuku a lokacin wannan yaki na almubazzaranci da cin hanci da rashawa.
Wasu mutane suna ganin hakan a matsayin yin amfani da karfin soji da ya wuce misali.
Wasu ko suna tuna wannan lokacin a matsayin wani yunkurin yaki da cin hanci da yaki ci yaki cinyewa, abin da ya dakile ci gaban Najeriya.
A dalilin wannan ne 'yan siyasa har ma da sojoji da farar hula suka shaide shi da halin gaskiya da rikon amana.

    Daya daga cikin abubuwan da ya yi shi ne bai wa 'yan Najeriya umarnin bin layuka a tasoshin shiga mota kana ya tura sojoji masu rike da bulala su sa ido.
    An dinga ladabtar da ma'aikatan gwamnatin da aka kama su da yin lattin zuwa wurin aiki ta hanyar sa su yin tsallen kwado.

    Ya kuma gabatar da wata doka mai tsauri ta sanyawa 'yancin 'yan jarida takunkumi, inda har aka daure wasu 'yan jarida biyu.


    A hannu guda kuma, kokarinsa na farfado da tattalin arziki inda ya dakatar da shigo da kayayyaki daga kasashen waje ya jawo mutane da dama sun rasa ayyukan yi tare da rasa kasuwancinsu.

    A bangaren daukar matakan yaki da cin hanci kuwa, ya bayar da umarnin sauya kudin kasar - an sauya kalar takardar naira - inda ya tursasa duk masu rike da tsoffin kudi su kai su banki don a musanya musu cikin kankanin lokaci.

    Farashin kayayyaki sun tashi inda rayuwa ta sauya, wanda hakan ya sanya Janar Ibrahim Babangida ya yi masa juyin mulki ranar 27 ga watan Agustan 1985. An daure Buhari a kurkuku na tsawon wata 40.


    Janar Babangida ya so ya yi gaggawar bai wa farar hula mulki, wanda Janar Buhari bai dauki hakan da muhimmanci ba.


    'Mutane ya rage naku'


    Janar Buhari ya ci gaba da kare dalilin da ya sa ya yi juyin mulki a ranar 31 ga watan Disambar 1983.


    A watan Oktobar 2005 ne Janar Buhari ya ce, "Ya rage wa mutane. Idan kuna son shugabanci na gari, to ba bu bukatar mulkin soja.


    "An samu mulkin soja ne a lokacin da ya zama dole ana bukatar hakan, kuma wadanda aka zaba na farar hular ba su yi abin a zo a gani ba."


    A lokacin da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ke shugabanci na mulkin soja a shekarar 1970, Buhari ne ke rike da muhimmin mukamin ministan man fetur.

    Amma dangantakarsu ta yi tsami bayan da Buhari ya hambare gwamnatin farar hula ta Alhaji Shehu Shagari, wanda shi ne yaci zaben da Mista Obasanjo ya shirya.
    Wannan ya ci gaba da jawo kace-nace game da matsayar Buhari dangane da demokuradiyya.

    Ana ganin dangantaka tsakanin tsofaffin janar-janar na soji biyu zai inganta domin yadda Obasanjo ya yaba wa Buhari a cikin littafinsa da ya wallafa kwanan nan.


    Obasanjo wanda ya ci zaben shugaban kasa har sau biyu a karkashin inuwar jam'iyyar PDP daga 1999 ya ce, "Buhari ba zai zama kwararren mai inganta tattalin arziki ba, amma zai zama shugaba mai karfin zuciya wanda ba za a iya tankwara shi ba, zai kuma kasance shugaba mara wasa da aiki.

    Daga bbchausa


    Copy the link below and Share with your Friends:

    Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
    OR
    Download from another source HERE



    No comments:

    Post a Comment