Tsananin Kama Da Messi Ta Sa Jami'an Tsaro Kama Wani Dalibi A Kasar Iran - NewsHausa NewsHausa: Tsananin Kama Da Messi Ta Sa Jami'an Tsaro Kama Wani Dalibi A Kasar Iran

Pages

LATEST POSTS

Tuesday 9 May 2017

Tsananin Kama Da Messi Ta Sa Jami'an Tsaro Kama Wani Dalibi A Kasar Iran

Tsananin Kama Da Messi Ta Sa Jami'an Tsaro Kama Wani Dalibi A Kasar Iran

A karshen mako ne, aka samu wani rudani wanda har sai da 'yan sanda suka dauke wani dalibi dan kasar Iran suka kai shi ofishinsu saboda yana matukar kama da Lionel Messi

Mutane da yawa a birnin Hamaden na kasar ta Iran suna son daukar hoto da dalibin mai suna Reza Parastesh yayin da 'yan sanda suka kama motarsa domin dakatar da rudanin da hakan ya haddasa.

Lamarin ya faru ne, watanni kadan bayan da mahaifin Reza Parastesh ya sa dan nasa ya dauki hoto da rigar Barcelona mai lamba 10 irin ta Messi.

Daga nan sai matashin mai shekara 25 ya fara yin aski tare da barin gemunsa kamar yadda Messi yake yi.

Hakkin mallakar hotoGetty Images
Image caption Ana rokon Parastesh yin hotuna a birnin Hameden, na kasar Iran
Ya fada wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa "Yanzu mutane suna daukarsa a matsayin Messi na Iran, kuma suna so in rika kwaikwayon duk abin da yake yi. Idan na je wani wurin sai ka ga mutane suna matukar mamaki.

" Ina matukar murna ganin cewa ganina zai sanya wasu farin ciki, kuma wannan farin ciki yakan sa ni farin ciki sosai."

Ya kuma ce yana koyon yadda ake wasu abubuwan a wasan kwallon kafa ta yadda zai zama kamar Messin sosai.

Rahoton BBC

Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment