Ayoyi da ingantattun Hadisai sun mana bayanin su wanane Yajuju Da Majuju. A dunkule za mu iya cewa, Yajuju Da Maj uju su ne kamar haka:
1. Wasu kabilu ne guda biyu daga zurriyar Annabi Adam (A.S).
2. Kamannin halittarsu irin ta sauran ‘yan Adam ce babu wani banbanci.
3. Suna da yawan gaske.
4. Kabilu ne masu yawan barna da ta’adi a bayan kasa.
5. Suna rayuwa bayan ganuwar da Zul-Karnaini ya gina domin hana su shigowa garurwan makotansu su yi musu barna.
6. Dab da tashin alkiyama wannan ganuwa za ta rushe, su fito, su kwararo ta ko-ina, su shanye ruwan koramar Tabariyya.
7. Ba jimawa Allah ta’ala zai aiko musu annobar wata irin tsutsa wadda za ta rika shiga wuyayensu ta rika kashe su, har gaba daya su kare. Daga nan sai Allah ya aiko wasu manya-manyan tsitsaye da za su rika daukar gawawwakinsu suna jefa su cikin teku.
8. Duk wannan zai faru ne bayan bayyanar Mahdi, da saukar Annabi Isa, da kashe dujal.
9. Da zarar sun fito, sauran manya-manyan alamomin tashin kiyama za su biyo baya da gaggawa
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment