NewsHausa: SPORT::::::::::::: NewsHausa: SPORT:::::::::::::

Pages

LATEST POSTS
Showing posts with label SPORT:::::::::::::. Show all posts
Showing posts with label SPORT:::::::::::::. Show all posts

Friday, 16 March 2018

Sevilla Ta Karya Tarihin Shekara (60) Na Manchester United

Daga Abba Ibrahim Wada Gwale
Kungiyar kwallon kafa ta Sevilla dake kasar sipaniya ta fitar da Manchester United daga gasar zakarun nahiyar turai, bayan samun nasarar da tayi akanta daci 2-1 a wasan mataki na kungiyoyi 16, bayan da a wasan farko aka tashi canjaras-0-0.

Dan wasan Sebilla Wissam ben Yedder ne ya zura duka Kwallyen biyu bayan yashigo daga baya, yayinda Romelu Lukaku ya zurawa United kwallo daya tilo da ta ci.
Karo na farko kenan da Manchester United ta gaza kai wa matakin gaf dana kusa dana karshe (kwata Final) acikin shekaru 60.

Manchester United ta bi sawun kungiyar Tottenham wadda itama kungiyar Jubentus ta yi waje da ita a gasar zakarun nahiyar turan.

Mai koyar day an wasan kungiyar Jose Mourinho ya bayyana cewa daman ba sabon abu bane kuma kungiyar zata mayar da hankali a ragowar wasanninta da take bugawa.

Real Madrid Sun Shiga Sahun Mahaukata Akan De Gea - Mourinho

Daga Abba Ibrahim Wada Gwale
Mai koyar da yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Jose Mourinho, ya bayyana cewa Real Madrid suna bata lokacinsu ne kawai akan mai tsaron ragar kungiyar tasa, David De Gea domin dan mai tsaron ragar bana siyarwa bane.

Mourinho ya bayyana hakane bayan kungiyarsa ta tashi daga wasan da suka buga da Sebilla inda yace ya kamata su nemi wani mai tsaron ragar saboda bazasu samu abinda suke so ba a Manchester United.

Yaci gaba da cewa idan shine shugaban gudanarwar kungiyar ta Real madrid da tuni ya hakura da neman De Gea saboda yana neman abinda bazai samu ba kuma yana bata lokacinsa domin idan ya hakura zai iya samun wani a wata kungiyar.
Real Madrid dai tana shirin yin garambawul a kungiyar bayan da kungiyar takasa abin azo agani a gasar laliga kuma tuni shugaban kungiyar ya shirya kashe kudi domin siyan duk dan wasan da yake so.

Dabid De Gea dai shine mai tsaron ragar da Real Madrid take zawarci sai kuma mai tsaron ragar kungiyar Chelsea, Thibaut Courtoise wanda kungiyar shima take zawarci idan bata samu De Gea ba.

Sai dai Mourinho ya bayyana cewa mai tsaron ragar babu inda zashi a wannan kakar domin ya shirya cigaba da buga wasa dashi har zuwa kakar wasa mai zuwa.
Dabid De Gea dai yanada ragowar watanni 16 a ragowar kwantaragin daya rage masa a kungiyar.

Ina So Allah Ya Hadamu Da Liverpool ko Real Madrid - Dzeko

Daga Abba Ibrahim Wada Gwale
Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta AS.Roma, Edin Dzeko ya bayyana cewa yanzu burinsa shine su hadu da kungiyar Real Madrid ko Liverpool a wasan zakarun turai da suka kai wasanmatakin kusa dana kusa dana karshe a ranar Talata bayan sun doke Shakhtar Donesk.

Kungiyar kwallon kafa ta Roma ta samu kai wa ga matakin gaf da kusa dana karshe, bayan samun nasara akan Shaktar Donetsk ta kasar Ukraine daci 1-0.
Dan wasan gaba na Roma Edin Dzeko, dan kasar Bosnia Herzgobinia ne ya ci wa kungiyar tasa kwallon a mintuna na 52 da fara wasan bayan yayi arangama da mai tsaron ragar Shakhtar.

A zagayen farko na wasan da suka buga a Ukraine, Roma ta yi rashin nasara a hannun Shaktar Donetsk da kwallaye 2-1.
Karo na farko kenan da AS Roma ta samu kai wa ga zagayen gaf da kusa dana karshe a gasar ta zakarun nahiyar turai cikin shekaru 10.

Zalika rabon da wasu kungiyoyin kwallon kafa da suka fito daga kasar Italiya su kai matakin na gaf da kusa da karshe, kamar wannan karon a lokaci guda, tun bayan kakar wasa ta 2006/2007, a lokacin da kungiyar ta Roma, da AC Milan suka samu nasarar kai wa zagayen.

Monday, 12 March 2018

Manchester City da Manchester United Sun Shiga Cikin Masu Zawarcin Neymar



Wani shafin harkar tamaula dake yanar gizo, Diario Gol (www.diariogol.com) ya bayar da labarin cewa kungiyoyin kwalon kafa biyu dake bugawa a wasannin Firimiya Lig na Ingila a birnin Manchester, watau City da United, sun shiga cikin jerin masu zawarcin dan wasan Brazil da kuma kungiyar PSG ta Faransa, Neymar Jr.

Ana rade-radin cewa Neymar ba ya jin dadin zamansa a kungiyar PSG, kuma yana kwadayin a sayar da shi ma wata kungiyar bayan shekara daya kawai a Faransa.

Har yanzu yana kwadayin komawa kungiyar Real Madrid mai bugawa a gasar La Liga, amma rahoton na Diario Gol yace Neymar ba zai ki komawa Manchester City ba, idan har aka kasa cimma daidaito kan komawarsa zuwa Real Madrid.


Cristiano Ronaldo Da Sergio Ramos Ba Su Son Madrid Ta Sayo Paul Pogba


Taurarin 'yan wasan kungiyar Real Madrid, Cristiano Ronaldo da Sergio Ramos sun daura damarar ganin cewa Real Madrid ba ta sayo Paul Pogba daga kungiyar Manchester United.

Shafin Don Balon mai buga labaran wasannin tamaula a yanar gizo, yace 'yan wasan biyu sun dukufa domin shawo kan shugaban Real Madrid, Florentino Perez, a kan kada ya sayi Pogba.

Ana rade-radin cewa Manchester United na tunanin sayar da Pogba a bayan rashin kuzarin da ya nuna cikin 'yan kwanakin nan, har ma aka ajiye shi a benci a wasu muhimman wasannin da United ta buga.

Ronaldo da Ramos sun damu da irin yadda kawo Pogba zai shafi sauran 'yan wasan Real Madrid, kuma su na ganin cewa kungiyar ba ta bukatarsa a yanzu.

Friday, 9 March 2018

Na Yi Nadamar Barin Barcelona - Neymar

Wani sabon labari da ya bulla a baya bayan nan ya bada tabbacin cewa dan wasa gaba na PSG mafi tsada a duniya, da ke jiyyar rauni Neymar, ya fara tuntubar jami’an tsohuwar kungiyarsa ta Barcelona da nufin yi mata kome.

Wata jaridar labarin wasanni ta Spain, 'Mundo Deportivo', ta rawaito cewa tuni Neymar ya bayyana nadamar sauyin shekar da ya yi daga tsohuwar kungiyarsa ta Barcelona zuwa PSG, kwanaki kadan bayan fitar da ita daga gasar zakarun turai da kungiyar Real Madrid ta yi da kwallaye 5-2 a jimillar wasanni 2 da suka buga.

Wannan sabon al’amari ya bijiro ne, watanni 7 kacal bayan sauyin shekar da Neymar ya yi daga PSG akan euro miliyan 222.

Sai dai fa ba wai Barcelona Neymar ya ke kallo kadai a matsayin hanyar samun damar raba gari da PSG ba, Real Madrid ma na daga ciki, kasancewar tuni shugabancin Madrid din ya ce a shirye yake ya biya euro miliyan 400 domin sayen dan wasan daga PSG.

Wasu masu sharhi na da ra’ayin Neymar yana neman hujjar komawa ne zuwa Real Madrid kai tsaye cikin sauki, kasancewar akwai yiwuwar Barcelona ta ki amincewa da tayin komensa.

Saturday, 3 March 2018

Yau Take Sallah : Ana Tuhumar Luca Modric Da Yiwa Kotu Karya

Hukumomi a Croatia na tuhumar kaftin din kasar Luca Modric da shan rantsuwar karya a kotu.
Ana zargin dan wasan na Real Madrid da yi wa kotu karya a lokacin da ake shari'ar Zdravko Mamic babban daraktan Dinamo Zagreb kan badakalar haraji.
Masu gabatar da kara sun ce Modric ya bada shedar karya a watan Yunin 2017 kan bayanan da suka shafi musayarsa daga Dinamo zuwa Tottenham Hotspur a 2008.
Idan dai har aka tabbatar da zargin, Dan wasan na iya fuskantar hukuncin daurin shekaru biyar a gidan yari.
An ce Mista Mamic da dan uwansa Zoran sun taushe wasu kudade ne a cinikin 'yan wasan Zagreb.
Ana zarginsu da wawushe kudaden Dinomo Zagreb da suka kai sama da $16.7m.

A Yau Assabar Za'a Yiwa Neymar Tiyata

Za a yi wa dan wasan Paris St-Germain na gaba Neymar tiyata a ranar Asabar kan raunin da ya ji a idon sawu a lokacin wasan da suka ci Marseille 1-0 a gasar Faransa ranar Lahadin satin daya gabata.

Likitan tawagar kwallon Brazil Rodrigo Lasmar shi ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai, kuma ya ce dan wasan mai shekara 26 ba zai yi wasa ba tsawon wata uku.
Ya ce Neymar ba zai iya samun damar yin sauran wasannin kungiyarsa PSG ba a kakar nan, amma yana sa ran zai warke ya yi wasannin gasar kofin duniya a watan Yuni.
Likitan ya ce za a yi wa Neymar aikin ne a wani asibiti da ke birnin Belo Horizonte na Brazil ranar Asabar da safe.

Da farko kociyan PSG Unai Emery ya ce Neymar yana da ‘yar damar yin wasansu da Real Madrid na Zakarun Turai a mako mai zuwa, kafin kuma mahaifin dan wasan ya sanar cewa ba zai yi wasa ba tsawon wata shida zuwa takwas.

PSG ta ba wa Monaco ta biyu a tebur tazarar maki 14 kuma a ranar 6 ga watan Maris za ta karbi bakuncin masu rike da kofin Zakarun Turai Real Madrid, wadanda suka ci su 3-1 a wasan farko na zagayen kungiyoyi 16.

Tuesday, 27 February 2018

Ba za a Mu yi Amfani da Fasahar Alkalanci Ba a Turai- Ceferin

Hukumar Kwallon Kafar nahiyar Turai ta ce, ba za ta yi amfani da fasahar bidiyon da ke taimaka wa alkalin wasa a kakar gasar zakarun Turai mai zuwa ba saboda tarin rudanin da ke tattare da fasahar kamar yadda shugaban hukumar, Aleksander Ceferin ya bayyana.

Ceferin ya ce, kawo yanzu babu wanda ke da cikakkiyar masaniya kan yadda fasahar ke aiki saboda rudanin da ke cikinta.
Ceferin ya kara da cewa, lallai wannan fasahar tana da kyau amma kar a yi garajen fara amfani da ita.

Kalamansa na zuwa ne a yayin da da Kwamitin Kwallon Kafa na kasa da kasa ya gudanar da wani taro a ranar Asabar don yanke shawara game da amincewa da fasahar kafin aiki da ita a gasar cin kofin duniya a Rasha a bana.
An dai yi amfani da fasahar a wasu kasahe kamar Ingila a gasar firimiya da Carabao da kuma Jamus a gasar Bundesliga, sai kuma Italiya a gasar Serie A.

Rauni zai hana Neymar Da Silva karawa da Ronaldo na Madrid

Ga alama gwarzon dan wasan PSG, wato Neymar De Silva ba zai samu damar buga wasan da kungiyarsa za ta yi da Real Madrid ba a gasar cin kofin zakarun Turai, matakin kungiyoyi 16 zagaye na biyu saboda raunin da ya samu a kafarsa kamar yadda binciken likitoci ya tabbatar.

Neyma mai shekaru 26 kuma dan asalin kasar Brazil ya gamu da raunin ne a fafatawar da PSG ta doke Marseille da 3-0 a ranar Lahadi a gasar Lig 1 ta Faransa, lamarin da ya sa aka cincibe shi akan gadon daukan mara lafiya cikin hawaye.
Sai dai kawo yanzu, PSG ba ta tabbatar da tsawon kwanakin da zai yi na jinya ba.

Kocin Real Madrid Zinedine Zidane ya yi fatan warkewar Neymar cikin hanzari don samun damar fafatawa da ‘yan wasansa da suka hada da Christiano Ronaldo.
PSG ta siyi dan wasan ne daga Barcelona akan farashin Pam miliyan 200 a cikin watan Agustan bara, in da ya ci ma ta kwallaye 29 cikin wasanni 30.

Saturday, 24 February 2018

Ana Rikici Tsakanin Mourinho Da Paul Pogba A Filin Daukar Horo

Rahotanni daga kasar ingila sun bayyana cewa mai koyar da yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Jose Mourinho da dan wasan kungiyar, Paul Pogba sunyi rikici a lokacin da kungiyar take daukar horo a filin daukar horon kungiyar bayan da Pogba yayi zargin cewa Mourinho yana kallonsa a matsayin wanda yasa kungiyar bata kokari.

Hakan yasamo asaline sakamakon halin da kungiyar ta shiga na rashin lashe wasanni a yan kwanakin nan bayan da kungiyar ta lashe wasanni biyu kacal cikin wasanni biyar da kungiyar ta buga.

Sau biyu Mourinho yana cire Pogba acikin wasannin da kungiyar ta buga sannan kuma sau uku yana ajiyeshi a benci wanda hakan yasa aka fara rade radin cewa akwai matsala a tsakanin mutanen guda biyu.

Wasu rahotannin sun bayyana cewa Mourinho yana zargin Pogba bias zakewa da yake wajen shiga aikin mai koyarwa abinda kuma Mourinho bayason.

Sannan an kuma bayyana cewa Mourinho yana gayawa dan wasan bakar Magana agaban ragowar yan wasan kungiyar wanda kuma Pogba yake ganin kamar yana wulakantashi.
Tuni aka fara rade radin cewa Pogba yafara tunanin barin kungiyar bayan daya bukaci wakilinsa daya fara neman kungiyar da zata siyeshi domin yana son barin kungiyar a karshen kaka mai zuwa.

Za a fafata karo Na 179 Tsakanin Man United da Chelsea

A ranar lahadin karshen makon nan ne za ayi zazzafar karawa tsakanin Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United da takwararta Chelsea karkashin gasar Firimiya da ke ci gaba da gudana. Wasan dai shi ne karo na 179 da kungiyoyin biyu za su kara tsakaninsu.

Manchester United ce dai ta lallasa Chealsea sau 76 yayin da suka yi canjaras a wasa 49 sai kuma wasanni 53 da ita Manchester ta sha kaye a hannun Chelsea.

Kawo yanzu dai Manchester United din ita ke a matsayi na biyu a teburin Firimiya da maki 56 banbancin maki 3 tsakaninta da Chelsea wadda ke a matsayi na hudu.

Monday, 19 February 2018

Ashe ba Ronaldo da Messi ne kan Gaba Wajen Yawan Dukiya Da Kudi a Cikin ‘Yan kwallon Kafa Ba

Faiq Bolkiah mai shekaru 19 a Duniya ya sha gaban har irin su Ronaldo

- Gidan wannan matashin ‘Dan kwallon ke rike da sarautar kasar Burnei

Kwanan nan mu ka gano cewa ashe wani yaro ne dabam ba manyan gwaraza irin su Ronaldo ba ne kan gaba wajen yawan dukiya a cikin jerin ‘Yan wasan kwallon Duniya ba. Iyayen wannan yaro sun taba biyan Marigayi Micheal Jackson Dala Miliyam 12 domin yayi masu wasa.

Ba Cristiano Ronaldo da Lionel Messi ne kan gaba wajen yawan dukiya ba
Dan kwallon da ya fi kudi a Duniya shi ne Faiq Bolkiah wanda da dama ba su da labarin sa don kuwa bai yi suna ba. Bolkiah mai shekaru 19 ma dai ko bugawa Kungiyar sa ta Leicester City bai taba yi ba a halin yanzu don kuwa yana sahun masu tasowa ne a Kungiyar.


Kamar yadda jaridun kasar waje ke bada rahoto, ‘Dan wasan ya mallaki abin da ya haura Biliyoyin Daloli. ‘Yan uwan wannan saurayi ne ke da rike da sarautar kasar Burnei wanda sun ba Dala Biliyan 20 baya tuni. Dan wasan ya bugawa Chelsea kafin ya koma Leicester.

An haifi wannan ‘dan gidan sarauta ne a Garin Los Angeles Kasar Amurka amma yanzu haka yana bugawa kasar sa ta Brunei inda har ya taba cin kwallo guda. Mahaifin wannan matashi yana da motoci sama da 2300 kuma mutum ne mai facaka da kudi kamar ba ya so.

Friday, 16 February 2018

Kane Ya Amince Da Sauya Sheka Zuwa Real Madrid

Dan wasan gaba na Kungiyar Tottenham Harry Kane ya
cimma yarjejeniya da Real Madrid kan sauya sheka zuwa
gareta idan aka bude kasuwar ‘yan wasa ta gaba.

Shahararriyar mujallar labaran wasanni ta kasar Spain 'Don
Balon' ta rawaito cewa Harry Kane ya amince ya rattabawa
Real Madrid hannu kan yarjejeniyar murza mata leda tsawon
shekaru 5.

Sai dai an cimma matsayar ce tsakanin dan wasan da wakilan
Real Madrid, yayin da a yanzu ya rage, tattaunawa tsakanin
Madrid din da kuma Tottenham kan farashin Harry Kane.

An dai shafe watanni ana alakanta Harry kane da sauya
sheka zuwa Real Madrid tun bayan da tauraruwarsa ta
dada haskawa a fagen zura kwallaye.

Wasanmu da PSG a Faransa ba mai sauki bane - Zidane

Mai horar da Real Madrid Zinaden Zidane ya ce ‘yan
wasansa zasu iya shan wahala sosai a zagaye na biyu na
wasan da zasu yi tattaki zuwa Faransa don karawa da
kungiyar PSG, a gasar zakarun turai mataki na kungiyoyi 16.

A zagayen farko na wasan dai Real Madrid ta lallasa PSG da
kwallaye 3-1, wadanda Critiano Ronaldo da Marcelo suka ci,
yayin da suka karbi bakuncin PSG din a filin wasa na Satiago
Bernabeu.

Zidane dai ya yi gargadin cewa dole Real Madrid ta jajirce a
wasa na biyu da zata yi tattaki zuwa Faransa, ba tare da
la’akari da nasarar farko da suka samu kan kungiyar ba.
Tun a farkon kakar wasa ta bana Real Madrid ke fuskantar
kalubalen koma baya kan nasarorin da ta saba samu a
wasanninta, musamman na gida Spain wato La Liga.

Kalaman na Zidane sun zo ne a dai dai lokacin da shi ma,
dan wasan gaba na kungiyar PSG, Neymar, ya jadadda cewa
kungiyar tasa, zata iya kai wa ga zagaye na gaba a gasar
zakarun turan, duk kuwa da rashin nasarar da suka yi a
hannun Real Madrid a Spain, ranar Laraba da ta gabata.

Ko da yake Neymar ya ce wasan zagaye na biyu da zasu
fafata a ranar 6 ga watan Maris mai wahala ne, yana da
kwarin gwiwar zasu iya samun nasara akan yaran Zidane.

Cristiano Ronaldo Ya fi Kowa a Gasar zakarun Turai

Cristiano Ronaldo na ci gaba da kafa gagarumin tarihi a wasannin da yake yi wa Real Madrid a gasar cin kofin zakarun Turai, inda kawo yanzu ya ci wa kungiyar kwallo 101, kuma yana kan hanyar karawa.

Ba ri mu fara da yin maraba da Cristiano Ronaldon cikin jerin 'yan wasan da suka ci kwallo 100 a gasar. Su wane ne gwanayen da ke cikin wannan jeri ? Mutum daya ne tal.
Kwallo biyun da ya ci wa Real Madrid ta farfado ta doke Paris St-Germain da ci 3-1, a wasansu na farko na kungiyoyi 16 na karshe, a ranar Laraba, Ronaldo ya zama dan wasa na farko da ya ci kwallo sama da 100 a gasar zakarun Turai, a kungiya daya.
Dan wasan na gaba a yanzu ya ci kwallo 21 a wasa 12 na karshe da ya yi a gasar ta zakarun Turai, kuma kwallo 11 a wasa bakwai a wannan kakar.

Amma kuma duk da wannan bajinta, wasu mutanen na ganin kokarinsa na raguwa, ya riga ya kai kololuwarsa, yanzu dakushewa yake yi.

To idan aka kwatanta shi da abokan hamayyarsa, ya yake?
Ba shakka Ronaldo zai ji dadin wannan kwatanci. Domin yana da tsiran kwallo hudu da ya ci wa kungiya daya a gasar ta zakarun Turai, tsakaninsa da babban abokin hamayyarsa, Lionel Messi na Barcelona.

Bayan Messi babu ma wani dan wasa da yake kusa da bajintar ta Ronaldo wajen daga raga a gasar ta zakarun Turai.
Ga jadawalin sunayen 'yan wasa da kwallayen da suka ci wa kungiya daya a babbar gasar ta Turai;

1-Cristiano Ronaldo Real Madrid 101
2-Lionel Messi Barcelona 97
3-Raul Real Madrid 66
4-Alessandro del Piero Juventus 42
5-Karim Benzema Real Madrid 41
6-Thomas Muller Bayern Munich 40
7-Didier Drogba Chelsea 36
8-Ruud van Nistelrooy Manchester United 35
9-Thierry Henry Arsenal 35
10-Wayne Rooney Manchester United 30

Friday, 12 January 2018

DONE DEAL: Valencia Sign Francis Coquelin From Arsenal For A Reported £12m

Francis Coquelin has joined Valencia from Arsenal for a reported £12m, the 26-year-old, who joined the Gunners as a youth player in 2008, and signed a contract with the Spanish side until the summer of 2022.. He has a release clause of €80m.

Thursday, 11 January 2018

Kane ya zama dan wasa na uku mafi daraja a duniya

Rahoton wani sabon bincike da masu bibiyar kwallon kafa suka yi na kasa da kasa a karkashin kungiyar CIES, ya nuna cewa dan wasan gaba na kungiyar Tottenham Harry Kane, shi ne dan wasa na uku mafi daraja a duniya.

Rahoton ya ce, a yanzu darajar Kane ta kai Euro miliyan 194. Hakan ya bashi damar zama mafi tsada ko darajar bayan dan wasan kungiyar PSG Neymar kan 213, da kuma Lionel Messi na Barcelona kan euro 202.

An dai kafa ginshikan wannan bincike ne ta hanyar la’akari da darajar ‘yan wasan, a kungiyoyinsu na nahiyar turai bisa matakan shekaru, kwarewa, tsawon yarjejeniyar da suka sanyawa kungiyoyinsu hannu da kuma kimar ‘yan wasan a kasashensu.
A shekarar da ta gabata, Harry Kane ya samu nasarar cin kwallaye 56, a wasannin da ya bugawa kungiyarsa ta Tottenham da kuma kasarsa Ingila, hakan ya bashi damar zama dan wasan da ya fi kowa yawan kwallaye a nahiyar Turai.

Sauran ‘yan wasan da kungiyar sa idon ta CIES ta fitar da matsayin darajarsu a fagen na kwallon kafa, sun hada da Kylian Mbappe na PSG a matsayi na 4 kan euro miliyan 192.5, sai kuma Paulo Dybala na kungiyar Juventus a matsayi na 5, kan euro miliyan 174.6.

Dele Alli na Tottenham shi ne dan wasa na 6 mafi daraja kan Euro miliyan 171.3, sai kuma Kevin de Bruyne na kungiyar Machester City a matsayi na 7, kan euro miliyan 167.8.
Binciken kungiyar ta CIES, ya nuna dan wasa na 8 mafi daraja shi ne Romelu Lukaku na Manchester United kan euro miliyan 164.8, shi kuwa Antonie Griezman na Atlectico Madrid na a matsayi na 9 kan euro miliyan 150.2.

Paul Pogba na Manchester United shi ne dan wasa na 10 kan euro miliyan 147.5
Gwarzon dan wasan duniya na shekarar 2017, Cristiano Ronaldo kuwa, ya tsinci kansa ne a matsayi na 49, inda yake da darajar euro miliyan 80.4.

Wednesday, 10 January 2018

Ina Son Albashin Fan Dubu Dari Hudu A Manchester United -GRIEZMAN

Daga Abba Ibrahim Wada Gwale
Rahotanni daga kasar sipaniya sun bayyana cewa dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid, Antoine Griezman, dan kasar faransa ya bayyana cewa idan har Manchester United zasu bashi albashin fan dubu dari hudu a shirye yake daya koma kungiyar.
Griezman, mai shekara 26 a duniya yakusa komawa Manchester United a kasuwar siye da siyar da yan wasan data gabata kafin daga bisani ya canja shawara bayan da aka cigaba da dakatar da kungiyarsa ta Atletico Madrid na hanata siyan yan wasa sakamkon laifin da sukayi na siyan kananan yan wasa.

Sakmakon hakane kungiyar Manchester United taje ta biya fam miliyan 75 ta siyi Rumelu Lukaku daga kungiyar kwallon kafa ta Eberton sai dai watakila kungiyar ta koma zawarcin dan wasan a wannan watan na janairu sakamkon kungiyar ta Atletico ta siyi tsohon dan wasan Chelsea, Diego Costa.

Sai dai kungiyar kwallon kafa ta Barcelona itama tana zawarcin dan wasan amma sakamakon siyan dan wasa Coutinho da kungiyar tayi wata kila ta hakura da dan wasan domin ta kasha kusan fam miliyan 146 akan Coutinho.

An bayyana cewa shima Griezman din yana fatan cigaba da zama a kasar sipaniya sai dai watakila dole idan har yanason barin Atletico Madrid dole sai yabar kasar ta sipaniya domin zuwa wata kasar daban.

Manchester United dai zata yimasa tayin albashin fan dubu dari biyu da casa’in sai dai dan wasan zaiso sama da haka sakamakon yadda yan wasa suke tsada a yanzu.

Friday, 5 January 2018

Lambar yabo Salah ya lashe kyautar gwarzon shekara ta nahiyar Afrika

Mohamed Salah na kasar Egypt ya lashe kyuatar gwarzon shekara ta nahiyar Afrika wanda hukumar CAF ta gudanar a kasar Ghana jiya alhamis 4 ga watan Janairu 2018.

Dan wasan Liverpoo l ya doke abokin aikin sa na kungiyar Sadio Mane na kasar Senegal da kuma dan wasan Dortmund Pierre Emerick Aubameyang na kasar Gabon wajen karban kyuatar.

Salah ya nuna gwanintr shi bara inda ya taka muhiman rawan gani a kungiyar AS Roma har ga sabon kulob dinsa ta Liverpool wanda har yanzu shine dan wasa mafi kwallaye a kungiyar a kakar bana.

Hakazalika dan wasan ya taimaka wajen ganin kasar shi Egypt ta tsallake tsiradi na buga gasar cin kofin duniya wanda za'a gudanar a kasar Rasha bana.
Wannan shine karo na farko da Salah zai amshi kyautar gwarzon shekara ta CAF.