A Yau Assabar Za'a Yiwa Neymar Tiyata - NewsHausa NewsHausa: A Yau Assabar Za'a Yiwa Neymar Tiyata

Pages

LATEST POSTS

Saturday 3 March 2018

A Yau Assabar Za'a Yiwa Neymar Tiyata

Za a yi wa dan wasan Paris St-Germain na gaba Neymar tiyata a ranar Asabar kan raunin da ya ji a idon sawu a lokacin wasan da suka ci Marseille 1-0 a gasar Faransa ranar Lahadin satin daya gabata.

Likitan tawagar kwallon Brazil Rodrigo Lasmar shi ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai, kuma ya ce dan wasan mai shekara 26 ba zai yi wasa ba tsawon wata uku.
Ya ce Neymar ba zai iya samun damar yin sauran wasannin kungiyarsa PSG ba a kakar nan, amma yana sa ran zai warke ya yi wasannin gasar kofin duniya a watan Yuni.
Likitan ya ce za a yi wa Neymar aikin ne a wani asibiti da ke birnin Belo Horizonte na Brazil ranar Asabar da safe.

Da farko kociyan PSG Unai Emery ya ce Neymar yana da ‘yar damar yin wasansu da Real Madrid na Zakarun Turai a mako mai zuwa, kafin kuma mahaifin dan wasan ya sanar cewa ba zai yi wasa ba tsawon wata shida zuwa takwas.

PSG ta ba wa Monaco ta biyu a tebur tazarar maki 14 kuma a ranar 6 ga watan Maris za ta karbi bakuncin masu rike da kofin Zakarun Turai Real Madrid, wadanda suka ci su 3-1 a wasan farko na zagayen kungiyoyi 16.

Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment