Rungumar Da Nayi Wa Classiq a Waka Tsautsayi Ne - Inji Rahama Sadau - NewsHausa NewsHausa: Rungumar Da Nayi Wa Classiq a Waka Tsautsayi Ne - Inji Rahama Sadau

Pages

LATEST POSTS

Saturday 10 March 2018

Rungumar Da Nayi Wa Classiq a Waka Tsautsayi Ne - Inji Rahama Sadau


Sanannar jarumar nan ta fina-finan Hausa a masana'antar Kannywood da ma kuma turanci a masana'antar Nollywood watau Rahama Sadau ta bayyana rungume-rungumen da suka yi a cikin wakar da ta yi da mawakin nan Classiq a shekararun baya a matsayin tsautsayi da kuma kaddara.

Jarumar ta bayyana hakan ne a cikin wata fira da ta gabatar da wakilin majiyar mu ta Mujallar Fim a cikin wani yanayi mai cike da nadama da kuma ban tausayi.

A ta bakin jarumar, ta bayyana cewa kuma shi daman tsautsayi baya wuce ranar sa sannan Kuma duk dan Adam baya wuce kaddarar sa mai kyau ko mara kyau.

Da aka tambaye ta ko daman ta taba yi wa kungiyar masu shirya fina-finan Hausa ta MOPPAN da suka dakatar da ita, sai jarumar ta ce a'a.

Yanzu haka dai jarumar kamar yadda muka samu na a cikin wani hali na rashin tabbas da kuma sanin sahihiyar matsayar ta a masana'antar ta Kannywood bayan da kungiyar ta MOPPAN ta shigar da kara a kotu biyo bayan yafe mata da gwamnatin jihar Kano da kuma masarautar jihar ta Kano suka yi.

Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment