Ƙura Takai Bango : Buhari ya bada umarnin harbe 'yan bindiga a Zamfara - NewsHausa NewsHausa: Ƙura Takai Bango : Buhari ya bada umarnin harbe 'yan bindiga a Zamfara

Pages

LATEST POSTS

Saturday 31 March 2018

Ƙura Takai Bango : Buhari ya bada umarnin harbe 'yan bindiga a Zamfara

Bayan kazamin harin da 'yan bindiga suka kai garin Bawar-Daji da ke jihar Zamfara a Najeriya, wanda ya yi sanadiyar kashe mutane da dama, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bai wa jami’an tsaro umurnin harbe duk wani mutun da aka gani da bindiga a fadin Jihar.

Gwamnan Jihar Abdul Azizi Yari ne ya sanar da umarnin, a lokacin da ya ziyarci fadar Sarkin Anka Alhaji Attahiru Ahmad domin alhinin hare-haren da wasu ‘yan bindiga suka kai a garin Bawar Daji a baya bayannan.

Umarnin na shugaban Najeriya ya ce kada jami’an tsaro su bata lokaci wajen kokarin gurfanar da ‘yan bindiga ko barayin da suka kama a kotu, kai tsaye kawai su bindige su.

Gwamnan jihar ta Zamfara ya ce matakin ya biyo bayan yadda matsalar hare-haren 'yan bindiga ta ki ci ta ki cinyewa.
Yari ya kuma bada umurnin tube Hakiman yankunan da ake zargi da bai wa 'yan bindigar da ke kai harin mafaka, yayin da ya ja kunnen sauran Sarakuna cewar duk wanda aka samu yana boye irin wadannan mutane a yankunansu, zai gamu da fushin hukuma.

Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment