1. Asalin Ruwan Zam-Zam: Dan Hajara Annabi Isma'il, tsira da aminci su kara tabbata a gare su, ya tsunduma cikin yunwa da kishirwa bayan guzuri ya yanke da mahaifin sa Annabi Ibrahim ya bari.
A sakamakon tausayi da jin kai irin na uwa ga dan ta, ta shiga kai komo tare da hawa da sauka a kan duwatsun Safa da Marwa wajen neman abin da dan ta zai sanya a baka. Bayan wannan kai komo har sau bakwai sai kawai cikin mamaki ta ankare da wani ruwa dake gudana a karkashin inda sawayen dan ta, Annabi Isma'il.
2. Wasu sunaye da ake yiwa ruwan lakabi: Akan kirayi ruwan Zam-Zam da Maimoona, Shabbaa'a da kuma Murwiya.
3. Karfin jiki: Binciken wani masanin kimiyya na kasar Jamus, Dakta Knut Pfeiffer ya bayyana cewa, kwayoyin halittu na jikin dan Adam su kan zabura da zarar an kwankwadi ruwan Zam-Zam.
4. Amfani: Alfanun ruwan Zam-Zam ba su da iyaka, ya kan biya bukata duk wata niyya da aka sha ruwan domin ta.
5. Kiwon Lafiya: Ruwan Zam-Zam ya kunshi sunadaran Magnesium da Calcium dake kawar da wata cuta mai kwazaba.
6. Tarihi: Tun shekaru sama da 4000 da suka gabata, ruwan Zam-Zam yake ta gudana ba bu kakkautawa.
7. Tsafta: Bincike ya bayyana cewa ba bu wani tsaftaceccen ruwa da zai goga kafada da ruwan Zam-Zam.
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment