Sanata Ali Wakili na daga cikin Sanatoci mutum goma a majalisar dattawa da suka bayyanar da goyon bayansu ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari karkashin jagorancin Abdullahi Adamu.
Sune wadanda suka tayar da jijiyar wuya kan ba su amince da sake fasalin zaben da zai raba zaben 'yan majalisun tarayyar da na Shugaban kasa ba. Muryar Sanata Ali Wakili ta yi amo kan haka. Goyon bayansa ga Shugaba Buhari babu kumbiya kumbiya irin ta su Kabiru Gaya a ciki.
Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ya ce, yana kan hanya za shi bikin 'yar gidan mataimakin Shugaban kasa labarin rasuwar Sanata Ali Wakili ya riske shi, nan take ya fasa zuwa bikin ya ce a wuce gidan Ali Wakili, yana can har sai da aka kai Sanatan kushewa.
Amma duk da irin wannan soyayya da kauna da Malam Ali Wakili ya nunawa Shugaba Buhari, hakan ba ta iya sanya Shugaba Buhari zuwa jana'izarsa ba, kuma wannan shi ne abu daya tak da Shugaba Buhari zai yi iyalan Ali Wakili su ji cewa soyayyar Ali ga Buhari ta biya su.
A maimakon Shugaba Buhari ya maida sakamakon ladan soyayya da kaunar da Ali Wakili ya nuna masa ta hanyar abinda turawa suke cewa "paying his last respect" sai kawai ya tafi bikin duniya abinsa. Hausawa sun ce ana bikin duniya..., amma dai a lahira ba biki bane, sakamako ne "Yauma Tublas Sara'er"!
Na tabbatar da bayan rasuwar Ali Wakili za a ba shi labari a ce cikin wanda suka halarci jana'izarsa har da mutumin da yake so wato Shugaban kasa, ko bai yi murna ba zai yi murmushi.
Na sani cewar Shugaban kasa dan bai je jana'izar Ali Wakili ba, bai yi laifi ba, amma da ya je din karamci ne ga shi Ali Wakili kuma iyalansa za su yi farin ciki. Amma ba komai, Shugaban kasa ya yi addu'a wadda ita Ali Wakili ya fi bukata a yanzu.
Allah ya jikan Sanata Ali Wakili mni, ya yafe masa.
Yasir Ramadan Gwale
16-03-2018
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment