Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban daraktan dake kula da harkokin yada labarai na gidauniyar Malam Ahmad Muhammad Saka ya fitar inda ya yi hasashen babban rikici idan har hukumar ta dage kan sai ta hana yin wazifa da kuma salatul fatihi a makarantun.
sanarwar ta kuma bayyana cewa makarantun da gwamnatin tarayya ta gina a jihar dukkan su an yi su ne saboda darajar Sheikh Dahiru Bauchi din don haka bai kamata ba yanzu kuma gwamnatin jihar ta nemi yi masu shishshigi da katsalandan.
A wani labarin kuma, Mataimakin shugaban kasar Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya yi ikirarin cewa kiristoci da kuma wadanda suka fito daga kudancin Najeriya ne suka fi shanawa a wannan gwamnatin ta shugaba Muhammadu Buhari sabanin yadda 'yan kasar ke tsammani.
Farfesa Osinbajo yayi wannan ikirarin ne a yayin da yake zantawa da wasu 'yan jarida tare kuma da ma'abota anfani da kafar sadarwar zamani a cikin karshen satin nan a jihar Legas.
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment