Tare da :- mufti sheikh Dr Ahmad Mahmud Abubakar Gumi
ko baka da ra'ayin Dr. Ahmad Gumi ka daure ka saurari wannan karatu domin ya fadi hanyoyin dabarar zamba da Yan damfara suke yiwa jama'a
Wannan ita ce Muhadarar da Sheikh Dr Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya gabatar ranar Asabar 03/March/2018 a masallacin Marigayi Sheikh Bello Aladamawy dake Hayin Malam Bello Hayin Rigasa Kaduna.
A wannan Muhadarar zamu fahimci
👉 Mene asali da tushen Bokanci? Daga ina ya samo asali? Su waye suke yin shi?
👉 Me yasa jama'a suke yarda da bokaye ko malaman Tsibbu?
👉 Shin akwai bokanci kafin zuwan musulunci ya kuma mutanen farko suke yin sa?
👉 Mene hukuncin mutumin da ya yarda da wanda yace ya san wani abu da bai faru a gabansa ba?
👉 Shin akwai wanda Allah Ya bashi ikon tunkude masifa ko iya aukawa wani ita?
👉 Allah Ya fada mana Annabi Muhammad SAW bai mallaki amfanarwa ko iya cutarwar ba, to waye zai ce ya mallake su?
👉 Da gaske karfin da iya mulki ne na Annabi Sulaiman AS ya iya sarrafa Aljanu ko kuma umarnin Allah Aljanun suke bi?
👉 Malaman da suke amfani da ayoyin Alkur'ani ko Hadisai suna bayar da magani mene ne matsayinsu?
👉 Akwai abubuwan da babu wani makaluki da zai iya yi wa mutum sai Allah. Duk wanda ya yarda wani na iya yi to dakinsu daya da Shaidan a wuta wadansu abubuwa ne?
Wannan da sauran batutuwa duk a cikin wannan Muhadara.
Allah Ya tsare mana imanin mu baki daya amin.
© Salisu Hassan Webmaster
Latsa wannan link domin downloading
Download Audio Bokayen Zamani
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment