Cristiano Ronaldo Da Sergio Ramos Ba Su Son Madrid Ta Sayo Paul Pogba - NewsHausa NewsHausa: Cristiano Ronaldo Da Sergio Ramos Ba Su Son Madrid Ta Sayo Paul Pogba

Pages

LATEST POSTS

Monday 12 March 2018

Cristiano Ronaldo Da Sergio Ramos Ba Su Son Madrid Ta Sayo Paul Pogba


Taurarin 'yan wasan kungiyar Real Madrid, Cristiano Ronaldo da Sergio Ramos sun daura damarar ganin cewa Real Madrid ba ta sayo Paul Pogba daga kungiyar Manchester United.

Shafin Don Balon mai buga labaran wasannin tamaula a yanar gizo, yace 'yan wasan biyu sun dukufa domin shawo kan shugaban Real Madrid, Florentino Perez, a kan kada ya sayi Pogba.

Ana rade-radin cewa Manchester United na tunanin sayar da Pogba a bayan rashin kuzarin da ya nuna cikin 'yan kwanakin nan, har ma aka ajiye shi a benci a wasu muhimman wasannin da United ta buga.

Ronaldo da Ramos sun damu da irin yadda kawo Pogba zai shafi sauran 'yan wasan Real Madrid, kuma su na ganin cewa kungiyar ba ta bukatarsa a yanzu.



Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment