Labari Da Dumi Duminsa: An kashe Wani Babban kwamandan Sojojin Najeriya a Dajin Sambisa - NewsHausa NewsHausa: Labari Da Dumi Duminsa: An kashe Wani Babban kwamandan Sojojin Najeriya a Dajin Sambisa

Pages

LATEST POSTS

Thursday 1 March 2018

Labari Da Dumi Duminsa: An kashe Wani Babban kwamandan Sojojin Najeriya a Dajin Sambisa

Labarin da muka samu maras dadi daga majiyar mu ta Sahara Reporters ya bayyana cewa kasar Najeriya tayi wani babban rashi na daya daga cikin manyan kwamnadojin ta da ke yaki da 'yan ta'addan Boko Haram a dajin Sambisa mai suna Laftanal Kanal A. E. Mamudu.

Majiyar ta mu dai har ila yau ta bankado mana cewa yau din nan ne dai babban kwamnantan ya rasu tare da wani matashin sojan ruwa yayin da suke wani sintiri a dajin na Sambisa.


 Babban kwamandan wannan ne karo na biyu da aka tura shi yankin na arewa maso gabashin kasar domin yaki da 'yan ta'addan Boko Haram din.

Haka nan ma kuma an bayyana Laftanal KanaL Mamudu a matsayin wani zaki da bai da tsoro a filin daga.

A wani labarin kuma, A yau din nan ne dai dukkanin gwamnonin arewacin Najeriya suka hallara a garin Kaduna babban birnin jihar ta Kaduna domin fara wani muhimmin taro da zai yi duban tsanaki ga matsalolin da suka addabin yankin da suka hada da matsalar tsaro da kuma sauya fasalin kasa.

Shugaban gwamnonin na Arewa wanda kuma ke zaman Gwamnan jihar Borno, Alhaji Kashim Shetima a lokacin bude taron ya bayyana cewa a matsayin su na gwamnoni kuma wakilan al'umma sun ga cewar ya kamata su hadu wuri guda domin tattauna makomar yankin da kuma mutanen dake rayuwa a cikin sa.

Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment