Me yiwuwa Ronaldo da Messi ba za su je Rasha 2018 ba - NewsHausa NewsHausa: Me yiwuwa Ronaldo da Messi ba za su je Rasha 2018 ba

Pages

LATEST POSTS

Monday, 9 October 2017

Me yiwuwa Ronaldo da Messi ba za su je Rasha 2018 ba

Fitattun 'yan kwallon kafa na duniya Ronaldo da Messi da Sanchez na fuskantar barazanar rashin zuwa gasar cin kofin duniya ta shekarar 2018 da za a yi a Rasha.

A halin da ake ciki yanzu dai, ana daf da rufe shiga gasar, kuma wasu daga cikin manyan kasashen duniya na fuskantar barazanar samun shiga.


Yayin da kasashe kamar su Brazil, da Spaniya, da Ingila suka samu gurbi a Rasha, wasu kasashen da ake zaton za su taka leda a gasar ta duniya har yanzu na fafutuka.
Hakan na nuna cewa akwai yiyuwar manyan fitattun 'yan wasa na duniya da suka hada da Lionel Messi da Cristiano Ronaldo da Alexis Sanchez ba za su halarci gasar ba.

Rahoto daga bbchausa

Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment