Abin da Buhari ya shaida wa shugabannin APC - NewsHausa NewsHausa: Abin da Buhari ya shaida wa shugabannin APC

Pages

LATEST POSTS

Tuesday 31 October 2017

Abin da Buhari ya shaida wa shugabannin APC

Ranar Talatar yau ce Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa Shugabannnin Kwamitin Zartaswa na jam’iyyar APC jawabi dangane da abubuwan da ke faruwa a cikin jam’iyyar.
Ga cikakken jawabin da ya yi musu nan PREMIUM TIMES HAUSA ta fassara wa masu karatun ta:

FASSARAR JAWABIN SHUGABA MUHAMMADU BUHARI A TARON SHUGABANNIN KWAMITIN ZARTASWA NA JAM’IYYAR APC, A RANAR TALATA, A ABUJA

Bayan Gaisuwa,
Bari na fara da yi wa kowa lale marhabin da zuwa wannan muhimmin taro na shugabannin zartaswar jam’iyyar mu.
Sannan kuma ina mai yin godiya gare ku saboda addu’o’in da ku ka rika yi min da fatan alherin da ku ke yi min, wanda Allah cikin ikon sa ya amsa addu’o’in ku ta hanyar dawo min da lafiya ta, har na murmure.

Zan kuma mika gaisuwa da godiya ta ga shugabannin jam’iyya dangane da jajircewar da su ka yi wajen taimaka wa tafiyar gwamnatin mu a lokacin da na yi dogon hutun jinya.
Bari na fara da yin dan bayani kan shugabancin jam’iyyar mu, a bisa jagorancin Mai Girma Chief John Oyegun. Na yi aiki tare da shi, inda muka kusanci juna tun a cikin 1984 zuwa 1985. Abin farin ciki a nan, sai kaddara ta sake hada mu tare mu na shugabanci yaunzu a wannan kasa.

Ina mika godiya ga Cif John Oyegun da ma’aikatan da ke karkashin sa, bisa kokarin su na gudanar da kyakkyawan jagorancin jam’iyya a cikin shekaru biyu da rabi.

Tilas ne kuma na yaba wa shugabannin Majalisar Tarayya, a karkashin shugabancin Mai Girma Sanata Bukola Saraki da Mai Girma Kakakin Majalisa Yakubu Dogara. Tilas ba zan manta da hadin kan da na samu daga Majalisar Tarayya ba, ciki kuwa har daga bangaren masu adawa, wadanda su ka tanne zuciyar su daga nuna adawa mai dalili ko maras dalili, su ka bada gudummawa domin ci gaban kasa.

Godiya ta musamman ga Gwamnonin Jihohi wadanda su ka fuskanci babban kalubalen tabbatar da hadin kan al’ummar kasar nan. Wannan ya faru ne a daidai lokacin da haka kawai wasu su ka fito da hayaniyar siyasar da ta haifar da rikici saboda wasu munanan mafufofin su.
A dan kwarya-kwaryan jawabin da na yi a taron masu ruwa da tsaki da ya gudana jiya, na bayyana dalla-dalla wasu abubuwa na ci gaba da gwamnatin mu ta samar a bisa turbar daftarin alkawurran da jam’iyyar mu ta daukar wa jama’a a rubuce, da mu ka ce za mu gudanar musu idan mu ka yi nasara.

Za mu iya bugun kirji mu yi tutiya da irin gagarimar nasarar da mu ka samar a cikin shekaru biyu, a kan Boko Haram, Neja Delta, Wadatar Man Fetur, Karin Lantarki, Asusun Bai-daya, Harkokin Noma da Takin Zamani, da kuma uwa-uba jaddada cewa ba za mu laminci cin hanci da rashawa a kasar nan ba. Duk mun san da cewa yanzu dai an samu CANJI.
A yanzu dai daraja da martabar Najeriya ta nunka za mu, iya cewa kusan har ninki hudu.
Amma kuma duk da haka ba za mu shantake ba, saboda ina sane da babban kalubalen da ke gaban mu.

A shekarar da ta gabata na shaida muku cewa zan sake nada Mambobin Hukumomin Gwamnati. Ina matukar ba ku hakurin rashin samun damar yin haka, sakamakon wasu dalilai.
Wasu daga cikin mahalarta taron nan na sane da cewa an umarce ni tun a cikin 2015 da na yi wannan aikin sabbin nade-naden, to amma sai muka fuskanci tsaiko daga wasu kwamitoci masu yawa, domin a tabbatar an samu daidaito wajen yin nade-naden da nufin a tabbatar kowane yanki na kasar nan ya zamu wakilci daidai yadda ya dace.
A daya bangare kuma, ina sane da cewa mgoya bayan mu sun kagara su ga an yi wadannan nade-naden. Da yardar Allah za mu yi hakan nan ba da dadewa wa. Musamman ma ga shi a yanzu tattalin arziki na samun inganci, za mu samu halin kulawa da dukkan wadanda za a nada a dukkan hukumomin.

Haka nan kuma za a kara yawan ministoci domin a kara yawan hannayen daukar jinkar Gwamnatin Tarayya, ta yadda za a kara samun masu sabbin hikimomi da fasahar inganta al’amurran gwamnati.
Ina kara godiya a gare ku, dangane da jajircewar ku wajen sadaukarwa ga jam’iyyar mu kuma ina mai tunatar da ku cewa mu na kara bukatar karin kaimi daga gare ku nan da wattani masu zuwa. Ina fatan za mu ci gaba da dogaro da ku.

Idan mu ka ci gaba da tafiya a tsintsiya-madaurinki-daya, mu ka kau da kai daga rigingimu marasa tushe, dalili ko makama, to tabbas za mu kai ga nasarar CANJI a cikin kasar nan.
Ina yi muku fatan alheri.

Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment