Ma’aikatar kiwon lafiyar kasar ta ce bayan gwaje-gwajen da aka gudanar a kan gawarwakin mutanen biyu da suka mutu, an tabbatar da cewa cutar ce wadda ke haddasa tsiyayar jini a cikin jikin dan adam ta yi sanadiyyar ajalinsu.
Cibiyar binciken cututtuka masu yaduwa a kasar, ta ce cutar da ake kira Marburg ta soma bula ne a kasar cikin wani yankin da ake kira Kamwenge a shekara ta 2007.
Cutar da ke yaduwa kamar Ebola, a shekara ta 2012 ta yi sanadi rai 10, kazalika a 2014 ta kashe mutun guda.
Marburg sunan wani yankin ne na Jamus, inda aka fara samun bular cutar a shekara ta 1967.
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment