Kannywood: Jaruma Nafisa Abdullahi tace ta gaji da ‘yan Najeriya - NewsHausa NewsHausa: Kannywood: Jaruma Nafisa Abdullahi tace ta gaji da ‘yan Najeriya

Pages

LATEST POSTS

Tuesday 17 October 2017

Kannywood: Jaruma Nafisa Abdullahi tace ta gaji da ‘yan Najeriya



Fitacciyar jarumar nan ta wasan fina-finan Hausa a masana’antar Kannywood watau Nafisa Abdullahi ta fada a shafin ta na sada zumunta cewa ita ta gaji da ‘yan Najeriya saboda sabar sa ido da ke gare su tare da kuma maida karamar magana ta zama babba.

Jarumar dai da yi wannan rubutu ne a shafin nata inda take nuna rashin jin dadin ta game da yadda wasu ‘yan Najeriya ba su da wani aikin yi sai dai su zauna suyi ta ruruta maganar da bata kai ta kawo ba.

Mun samu dai jarumar haka ma dai bada shawarar cewa kamata yayi mutum yayi kokari ya gyara nasa kuskuren ba wai yayi ta ruruta na wani ba kamr shi baya yi.

Ga dai gundarin abun da jarumar ta rubuta: “Mutane da yawa ba aikin yi, shi yasa duk kankancin abu sai ya zama abun magana. Na gaji da yan Nigeria wallahi; kowa sai ya dinga yi kaman wani mutumin Allah mutumin Allah. Mutum ya yi kokari ya gyara kurakurensa, ya daina yi kaman shi waliyyi ne.”


Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment