A wata tattaunawa da Aminu Shariff Momo yayi da mai bayar da umarni Isah Abubakar Alolo da ya yi fice da lakabin Sheikh a gidan Talabijin na Arewa 24 ya tambaye shi,
Momo: Me ya sa ake kiran ka da Sheikh?
Alolo: Me ya sa ba za a kira ni da Sheikh ba?
Momo: Akasari idan an ce Sheikh za ka ga suna ne na Malaman addini?
Alolo: Fada min su Malaman addinin wa aka yanka rago aka ce sunan sa Sheikh?
Momo: Saboda suna yi wa addini hidima?
Alolo: Ai kowane Musulmi yana yi wa addini hidima, yanzu ko dutse ka gani a hanya ka dauke ka jefar ai aikin lada ne.
Daga kannywoodscence
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment