Soyayya: Wani dan sanda ya harbe wata budurwa saboda taki amsa soyayyarsa a Kaduna - NewsHausa NewsHausa: Soyayya: Wani dan sanda ya harbe wata budurwa saboda taki amsa soyayyarsa a Kaduna

Pages

LATEST POSTS

Wednesday 11 October 2017

Soyayya: Wani dan sanda ya harbe wata budurwa saboda taki amsa soyayyarsa a Kaduna


- Ana zargin wani jami’in dan sanda a
jihar Kaduna da harbin wata budurwa
saboda taki amince da soyayyarsa

- Buduruwar ta kasance daga kauyen
Gadar Mallam mamman dake kan
hanyar Kaduna zuwa Abuja

- Sha’awa ta bayyana cewa dan sandan
ya labe ne a lokacin da ya harbe ta
Ana zargin wani jami'in dan sanda a
Kaduna da harbin wata budurwa da
bindiga saboda taki amincewa da
soyayyarsa.

Majiyar Arewafresh ta ruwaito
budurwar mai suna Sha’awa Nasiru,
mai kimanin shekaru 20 da haihuwa
daga kauyen Gadar Mallam mamman
dake kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.
Majiyar ta bayyana cewa dan sandan
ya labe ne a lokacin da ya hangi
sha’awa ta shiga wani gida, yayin da
take fitowa sai ya kira sunanta, tana
amsawa zai ya saka mata harsashi.


Budurwar da aka harbe a kan so
Nan da nan mutane suka watse a guje
sakamakon jin harbin bindigar kafin
daga bisani wasu suka garzaya inda
budurwar take a kwance cikin jini
suka dauke ta zuwa asibitin Doka
dake jihar Kaduna,

amma abin yafi
karfinsu, inda suka ce a mika ta zuwa
babban asibiti, sai dai hakan bata
samu ba sabida yajin aikin da
kungiyoyin ma’aikatan lafiya suke yi,
ciki kuwa har da asibitin koyarwa
dake Gwagwalada.


Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment