Dalilin Da Yasa Auren manya manyan ƴan matan masana'antar kannywood ya mutu a cikin wannan Shekaran 2017 - NewsHausa NewsHausa: Dalilin Da Yasa Auren manya manyan ƴan matan masana'antar kannywood ya mutu a cikin wannan Shekaran 2017

Pages

LATEST POSTS

Wednesday 25 October 2017

Dalilin Da Yasa Auren manya manyan ƴan matan masana'antar kannywood ya mutu a cikin wannan Shekaran 2017


Rahotannin da muke samu daga majiyar mu ta Fim mai wallafa mujallar da ta shafi harkokin fina-finan Hausau ta bayyana cewa kimanin akalla auren mata 'yan fim shidda ne ya mutu a shekarar nan da muke ciki ta 2017. 

Haka ma dai mujallar ta bayyana hakan tamkar wani babban bala'i ko kuma annoba da ta fadawa 'yan masana'antar kasantuwar ba'a taba samun mace-macen aure da yawan da suka kai haka ba a cikin shekara daya. 

Wasu daga cikin matan dai sun bayyana cewa laifin mazan ne domin kuwa sun sa yaudara wajen neman auren nasu yayin da wasu kuma daga cikin matan suka bayyana cewa mazajen nasu ba su basu abinci.

Da majiyar tamu ta tuntubi wasu mazan da lamarin ya shafa daya daga cikin su ya bayyana cewa ita wadda ya auran tace wai bata son kishiya ne shi kuma ya ga kamata su rabu da ita. Matan dai da auren nasu ya mutun sun hada da Fauziyya Maikyau, Maryam Isah, Fati Al-Amin, Aisha Tafida, Safiya Kishiya da kuma Asma'u Musa.

Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment