Tarihin Sunan FkD Production Company Ali Nuhu - NewsHausa NewsHausa: Tarihin Sunan FkD Production Company Ali Nuhu

Pages

LATEST POSTS

Friday 20 October 2017

Tarihin Sunan FkD Production Company Ali Nuhu

Sunan mahaifiyar jarumi Ali dai Hajiya Fatima Karderam Digema, wadda 'yar asalin garin Bama ce dake jihar Borno. Sakamakon haka ne jarumin ya yi amfani da sunan mahaifiyar ta sa wajen sanyawa kamfanin sa na shirya fina-finai sunan FKD wato dai ma'anar sunan mahaifiyar domin tunawa da ita.

 Jarumin ya kuma sanyawa 'yar sa ta farko sunan Fatima duka don ya samu damar tunawa da wadda ta yi sanadin zuwan sa duniya.

takaice yanzu shekara 18 kenan da rasuwar mahaifiyar ta sa, wanda shine adadin shekarun da jarumi Ali Nuhu ya yi yana sana'ar fim, wanda kafin rasuwar ta sai da ta baiwa dan na ta damar shiga wannan harka tare da neman ma sa tabarraki daga wurin Mahalicci.

A yayin ganawa da marubuta mujallai jarumi Ali Nuhu ya bayyana cikin barkwanci cewa, mahaifiyar ta sa ta na kiran shi da sunan Ali sarkin Matsala wanda sanadiyar hakan ne bayan ta siyo mi shi tsarabar riga a wata tafiya kasar Amurka da ta yi, aka sanya ma sa sunan Ali Official Trouble Maker a bayan taguwar. Daga karshe an yiwa mahaifiyar addu'a da cewar Allah ya kara haske a kabarin ta da kuma jin kan ta.


Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment