Rayuwar Matan Arewa Cike Take Da Kalubale - In Ji Jaruma Rahama Sadau - NewsHausa NewsHausa: Rayuwar Matan Arewa Cike Take Da Kalubale - In Ji Jaruma Rahama Sadau

Pages

LATEST POSTS

Tuesday 10 October 2017

Rayuwar Matan Arewa Cike Take Da Kalubale - In Ji Jaruma Rahama Sadau


Daga Habu Dan Sarki

Jarumar Hausa Fim Rahama Sadau ta bayyana cewar, rayuwar yar Arewa mai hankoron zama wani abu nan gaba cike take da cikas iri-iri.

Sadau ta yi wannan batu ne a tattaunawa ta da jaridar Thisday. Jarumar ta ce dakatar da ita da aka yi a harkar fim din Hausa ya janyo ta sake samun wasu sabbin hanyoyi a harkar fim na cikin gida da waje.

Jarumar ta ce a kullum tana kokari wajen kare mutuncinta da kuma al'adarta a lokacin da take harkar sana'ar fim na turanci wanda aka yi a kudancin Nijeriya.

Sadau ta ce ko cikin kwanakin nan ta ki amincewa da yin wani fim na turanci wanda aka bukaci ta fito a matsayin 'yar madigo.



Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment