TIRKASHI: DALIBAN SAKANDIRE MASU RUBUTA JARABAWAR WAEC SUN FARA SHIGA DA BINDIGA DAKIN JARABAWA-KARANTA KAJI DALILI - NewsHausa NewsHausa: TIRKASHI: DALIBAN SAKANDIRE MASU RUBUTA JARABAWAR WAEC SUN FARA SHIGA DA BINDIGA DAKIN JARABAWA-KARANTA KAJI DALILI

Pages

LATEST POSTS

Wednesday 11 October 2017

TIRKASHI: DALIBAN SAKANDIRE MASU RUBUTA JARABAWAR WAEC SUN FARA SHIGA DA BINDIGA DAKIN JARABAWA-KARANTA KAJI DALILI

Bayan bugar da masu sa ido da kwaya, Dalibai sun fara zuwa dakin jarrabawa da bindiga – Hukumar WAEC
Magatakardan hukumar tsara jarrabawa ta WAEC ya koka da muguwar dabi’ar wasu daga cikin dalibai masu rubuta jarrabawar gama sakandire ta WAEC.

Magatakardan yayi wannan korafi ne a Legas yayin bayyana shirin yin wani taro a kan magance magudin jarrabawa.

Lamarin satar amsa a yanzu ya dauki wani sabon salo saboda lamarin har ya kai da barazanar rayukan ma’aikatan mu
Magatakardan hukumar tsara jarrabawa ta WAEC, Dakta Iyi Uwadiae, ya koka da muguwar dabi’ar wasu daga cikin dalibai masu rubuta jarrabawar gama sakandire ta WAEC ta bawa jami’an hukumar masu saka ido a kan jarrabawa kwaya, musamman a makarantu masu zaman kan su.

Magatakardan yayi wannan korafi ne a Legas yayin bayyana shirin yin wani taro a kan magance magudin jarrabawa a ranakun 19 da 20 ga watan nan.

Uwadiae, ya ce hukumar WAEC ba zata nemi izinin gwamnati domin ba wa jami’an hukumar makamai ba, saidai kawai su jawo hankalin gwamnati da kuma jama’a a kan hadarin da hukumar da jami’anta ke ciki.

“Lamarin satar amsa a yanzu ya dauki wani sabon salo saboda lamarin har ya kai da barazanar rayukan ma’aikatan mu.

Zamu iya kwatanta lamarin da irin yadda masu fasa kwabri ke hallaka jami’an hukumar kwastam, dalilin da ya sa dole gwamnati ta bawa jami’an kwastam din bindigu.

Saidai mu a hukumar WAEC ba zamu bukaci a bawa jami’an mu bindiga ba saidai mu sanar da duniya cewar dalibai a wasu makarantu ma su zaman kan su na shiga dakin jarrabawa da bindiga ba ya ga zuba kwaya a cikin abin shan jami’an mu masu sa ido a kan jarrabawa”. A fadin Uwadiae.

Bayan bugar da masu sa ido da kwaya, Dalibai sun fara zuwa dakin jarrabawa da bindiga – Hukumar WAEC
Magatakardan hukumar tsara jarrabawa ta WAEC ya koka da muguwar dabi’ar wasu daga cikin dalibai masu rubuta jarrabawar gama sakandire ta WAEC.

Magatakardan yayi wannan korafi ne a Legas yayin bayyana shirin yin wani taro a kan magance magudin jarrabawa.
Lamarin satar amsa a yanzu ya dauki wani sabon salo saboda lamarin har ya kai da barazanar rayukan ma’aikatan mu
Magatakardan hukumar tsara jarrabawa ta WAEC, Dakta Iyi Uwadiae, ya koka da muguwar dabi’ar wasu daga cikin dalibai masu rubuta jarrabawar gama sakandire ta WAEC ta bawa jami’an hukumar masu saka ido a kan jarrabawa kwaya, musamman a makarantu masu zaman kan su.
Magatakardan yayi wannan korafi ne a Legas yayin bayyana shirin yin wani taro a kan magance magudin jarrabawa a ranakun 19 da 20 ga watan nan. Uwadiae, ya ce hukumar WAEC ba zata nemi izinin gwamnati domin ba wa jami’an hukumar makamai ba, saidai kawai su jawo hankalin gwamnati da kuma jama’a a kan hadarin da hukumar da jami’anta ke ciki.
“Lamarin satar amsa a yanzu ya dauki wani sabon salo saboda lamarin har ya kai da barazanar rayukan ma’aikatan mu.
Zamu iya kwatanta lamarin da irin yadda masu fasa kwabri ke hallaka jami’an hukumar kwastam, dalilin da ya sa dole gwamnati ta bawa jami’an kwastam din bindigu.
Saidai mu a hukumar WAEC ba zamu bukaci a bawa jami’an mu bindiga ba saidai mu sanar da duniya cewar dalibai a wasu makarantu ma su zaman kan su na shiga dakin jarrabawa da bindiga ba ya ga zuba kwaya a cikin abin shan jami’an mu masu sa ido a kan jarrabawa”. A fadin Uwadiae.

Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE

No comments:

Post a Comment