…Ciroki har duka ya taba sha a wurin masoyanta
Daga Aliyu Ahmad
Tsohuwar jarumar finafinan Hausa, Fati Muhammad, har yau wasu na ganin ba a yi jarumar da ta kai ta farin jini, kyau da daukaka ba a duniyar finafinan Hausa. Ban dai sani ba ko nan gaba, amma har yanzu dai babu kamarta a ra’ayina.
Ita ce jarumar da a lokacin ta a ke dokin ganin fuskarta a fastar finafinai. Ita ce wadda har yanzu ‘yan fim su ke kiran jarumai mata na yanzu da su yi koyi da ita wajen girmama na gaba da kuma sanin makamar aiki, sannan kuma ba ta da girman kai.
Ita ce wadda murmushinta a fim ke sa masoyanta yin murmushi a gaske. Haka kuma ita cewa kukanta a fim ke sa masoyanta yin kuka a gaske. Ita ce wadda idan ka nuna ma ta kauna a fim masoyanta su ke nuna ma ta kauna a gaske. Idan kuma ka fito a makiyinta a fim, masoyanta za su dauke ka a abokin gabarsu a gaske.
Wadannan duk na daga cikin irin farin jini da daukakar da Fati Muhammad ta yi a lokacin.
Idan masu karatu za su iya tunawa, a lokacin da a ka daura auren Fati da abokin sana’arta kuma tsohon mijinta, Sani Musa Mai Iska, an yi ittifakin cewa taron daurin aurenta ya na daya daga cikin manyan tarukan da a ka gudanar a tarihin jihar Kano, wanda ba a taba cika kamarsu ba.
Domin ba na mancewa masoyan jarumar da dama sun zo daga jihohi daban-daban da ke fadin kasar nan, har ma daga wasu kasashe mafi kusa kamar su Nijar, Chadi, Kamaru da sauransu.
Saboda irin farin jinin da Allah ya yi ma ta, ba na mancewa a lokacin daukar fim din Hedimasta, Bashir Bala Ciroki ya fada min cewa a fim din Zarge, wanda ya ke binne Fati da ranta, saboda son da a ke yi wa Fati a lokacin sai da ya yi bakin jini a wurin masoyanta.
Ciroki ya kara da cewa, “ba na mancewa a lokacin na je kallo a Marhaba Sinima da ke birnin Kano, kawai sai na ga wasu matasa rike da sanduna su ka ce min su masoyan Fati Muhammad ne. Me ya sa na binne ta da ranta a fim din Zarge?
“Kawai sai na ga sun rufe ni da duka. Daga karshe dai da kyar na sha a hannun wadannan mutanen.
Babur dina da na je da shi sinimar, sai da safe a ka kawo min gida.”
Ciroki ya ce, ya yi mamakin irin farin jinin da Fati ta ke da shi da har ya kai abinda a ka yi cikin wasa a fim, amma masoyanta sun mayar da shi kamar gaske, har ta kai ga za su iya daukar ma ta fansa, kamar ba wasa ba.
Kasancewa ta wanda ya ke bibiyar masana’antar shirya finafinai, a duk lokacin da wasu daga cikin ‘yan fim su na hira game da wadanda su ka fi kowa daukaka ko kwarewa a tarihin masana’antar, su kan yawan sanya Fati a sahun gaba, kasancewar kwararriya ce a duk matsayin da a ka ba ta a fim. Sannan kuma su na yawan yabon ta wajen girmama na gaba da ita a ciki da wajen masana’antar.
Abin nufi a nan shi ne, duk da, a na cewa mutum tara ya ke bai cika goma ba, amma ita Fati ta hada yawancin abubuwan da a ke bukata wajen kowane jarumi; kwarewa, kwarjini, karsashi, mutunci, kyau, kirki, shimfidar fuska, farin jini, sannan kuma ba ta janyo abin fada ga kanta ko ga masana’antar Kannywood.
Wadannan abubuwa sun a wahalar samuwa ga jaruma guda; sai dai a jarumai mata 10 watakila, domin jaruman sai dai ka samu su na da daya ko biyu ko uku daga cikin abubuwan da a ka ambata a sama.
Fitaccen jarumi kuma jigo a masana’antar fim, wato Tahir Muhammad Fagge, a wata hira da mu ka yi da shi, a yayin da ya tashi ambaton jarumai masu girmama na gaba da su, ba na mancewa Fati ya soma ambata, inda ya bayyana cewa da jarumai mata yanzu za su yi koyi da dabi’unta, babu shakka za su daukaka fiye da yadda su ke a yanzu.
Domin a cewarsa, daukakar da Allah Ya yi ma ta a lokacin bai sa ta yi amfani da wannan damar wajen wulakanta abokan sana’arta da masoyanta ba.
Haka kuma a lokacin da ta ke kan tashe, a duk lokacin da ta gamu da masoyanta, ta kan ba su lokaci su yi musabiha cikin nutsuwa ba kamar yadda na yanzu su ke yi a gurguje ba, idan sun gamu da masoyansu. Ko gida masoyanta su ka biyo ta, ta na karbar su hannu bibiyu ba tare da yi mu su wulakanci ba.
Haka kuma kasancewar lokacin da Fati ta yi tashe, waya ba ta karade gari ba. Hakan ya sa duk furodusan da zai yi fim da ita, sai dai ya yi asubanci ya je gidansu, inda duk furodusan da ya yi sa’a ya same ta a gida, shi zai yi aiki da ita a wannan ranar.
Wannan kadan kenan daga cikin farin jinin da Allah Ya horewa Fati. Banda masoyanta wadanda idan sun ga a na azabtar da ita a fim sun dinga sharbar kuka; su a ganinsu kamar da gaske a ke azabtar da ita.
Wasu masoyan nata a wancan lokacin wadanda su ka hada da maza da mata, haka za su yi tattaki daga jihohin da su ke, domin kawowa Fati ziyara har gida.
Ko a lokacin bikinta ma, kungiyoyi daga jihohi daban-daban sun halarci bikinta. Ba na mancewa daga cikin kungiyoyin masoyanta da na gani sun hada da; kungiyar ’yan acaba masoya Fati Muhammad, kungiyar direbobi masoyan Fati Moh’d da dai sauransu, inda su ka sanya riguna masu dauke da hotunanta.
A yanzu ba za ka samu irin wadannan kungiyoyi na masoyan jaruman wannan lokaci ba.
Saboda farin jinin Fati, ko a lokacin da su ke tashe da abokan aikinta irin su Abida Muhammad, Maijidda Abdulkadir, Fati ta fi su yawan masoya da farin jini.
Kusan za mu iya cewa daukaka da ta ke da ita a wannan lokacin ne har ta kai ga ta yi tallar da ta yi silar tafiyarta kasar waje ita da maigidanta a wancan lokacin Mai Iska, wanda kusan ita ce jaruma ta farko a farfajiyar fim din Hausa da sana’arta ta yi sanadiyarta zuwa kasar waje.
Saidai kash! abinda ya ragewa Fati a yanzu shi ne aure. Don haka babban fatana ga kyakkywar Bafilatanar jarumar shi ne, Allah Ya ba ta miji nagari ta yi aure, wanda kuma a koda yaushe hakan shi ne burin Fati ’Yar Muhammad, kamar yadda wasu abokan aikinta ke yi ma ta lakabi.
Shin ko za a sake samun wata jaruma ta yi farin jini da daukaka na hakika tamkar yadda wannan ’yar baiwa ta yi? Lokaci ne kadai zai tabbatar da hakan ko akasin hakan!
Daga:-fimhausa
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment